Episode 21

1.6K 99 3
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

   *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*
  
Episode 21
November, 2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Kuka tasha sosai sannan ta mik'e ta cire kayan ta chanza, toilet ta wuce ta d'aurayo fuskan ta takwanta abinta dan batajin zata iya fita duk da tanajin yunwa.
      Ahaka Granny tazo ta same ta tayi zurfi cikin tunani dan ko noticing shigowan ta batayi ba har saida ta dafa ta, a firgice ta d'ago amma ganin Granny yasa ta saurin juya mata baya ta sake sanya kuka wane 'yar Baby, aiki ne ya samu Granny dan dakyar ta samu ta rarrashe ta tayi shiru .
Mik'ewa tayi ta wuce babban falour dan having breakfast anan ta iske su Mammy suna hira, gaishe su tayi ta wuce dinning tayi serving kanta ta soma karyawa.
Tunda Mammy ta kalle ta tasan Suwayd ya d'aura a inda ya tsaya nan take taji ranta yayi masifar b'aci, Ummy kam ma d'auke kanta tayi daga Safwah'n yayin da Mummy ke tausayin ta sosai.
      Saida ta gama tsaf ta tako inda su Ummy suke ta durk'usa ahankali tace " Ummy please wayan ki zaki aramin ".
Batare da tace komai ba ta mik'a mata, tsokanan ta Mummy ta somayi wai bataji muryan twiny nata ba shine tayi kuka, ita kuwa murmushin yak'e kawai ta sake ta mik'e ta koma part d'in Granny.
A d'aki ta iske ta tana sallah'n walha dan haka saida ta bari ta idar taje tayi locking k'ofan d'akin ta dawo ta zauna a kusa da Ita.
Unlocking password ta wayan tayi, sannan tayi viewing contact na Sadiya, da Ummy tayi saving da Ammey cause haka yaran ke k'iran ta, video call ta mata inda ba tare da b'ata lokaci ba tayi picking.
Gaisawa sukai sosai_sosai cike da k'aunan juna kaman yadda suka saba.
     Granny kam mutuwan zaune tayi jin dagaske muryan Sadiyan ta take ji, hannu na rawa ta k'arfa wayan idon ta a runtse, ahankali ta bud'e idonta ta sauke su kan Sadiya da shocked na ganin mahaifiyar tata yasa ta kasa koda kwakwkwaran motsi.
Kallon_kallo suka shigayi yayin da wani irin farin ciki da annashuwa ya soma ratsa zuciyan su both, ahankali Granny ta soma magana " Sadiya na is that you? Is that really you? Dan Allah karku tashe ni idan bacci nake, Ya Allah idan mafarki nake ka dawwamar dani a haka... "
   " Mummy " tayi saurin tare ta tana kuka sosai " Mummy please forgive me " tayi pleading kukan ta na tsanantuwa.
" Shiiii Baby ni ya kamata in nemi tuban ki, na rok'eki dan Allah ki yafe min forgive me please daughter, idan kin so please allow me nazo in ganki in nemi yafiyar ki, i miss you so much I terribly miss you and want to be with you, do me this favor nasan ban cancanci hakan ba but please let me this is the right time da ya kamata na dai_dai ta tsakanin mu ".
   " Mummy ki daina fad'an haka please if not barin tab'a iya yafewa kaina ba, ni ya kamata na nemi tubarki for the pains i have made you went through, idan baki yafe min ba hak'k'in ki babban masifa ne agare ni ".

Nan dai suka sha kukan su kaman ba gobe, sai da sukayi mai isan su sannan suka yafi juna sai kuma hiran yaushe gamo ya biyo baya, a kama wancan a sake a kama wannan haka har suka gangaro kan auren da tai da 'ya'ya ukun da take da, duk saida ta had'a ta da yaran ta suka gaisa inda wonders ya kusa kashe ta ganin tsananin kaman da Safwah da Sayyada ke hatta da blue eyes nasu.
   Sosai yaran sukayi farin ciki dan suna damuwa sosai da rashin sanin family'n Ammy'n su, Abuh kad'ai suka sani dan yana kai musu visit sai Safwah da Safwan su kuma ta waya suke gaisawa.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now