Episode 34

1.9K 116 7
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 34
29_12_2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

"Ab..Abuh!" Wani irin kallo ya bita dashi yana son karantar yanayin ta hakan yasa ta kama bakin ta.
Ummy da Ammey data gano a bayan sa yasa gaban ta mugun fad'i, kallo d'aya Ummy ta mata tasan totally bata da gaskiya a fusace tace "Zaki bamu hanya mu wuce ne ko ya?"
Like a bloody idiot ta matsa gefe suka shiga ta miyar da k'ofan tayi locking, k'arasawa falour'n suka yi suka zauna ta durk'usa har k'asa tana gaishe su jikin ta na mugun kakkarwa muryan ta na rawa.
Sandai both ba wanda ya kulata du sun cika da shock jin yadda d'akin ya cika da kid'a, mik'ewa tayi dakyar taje ta kashe ta wuce ta d'ibo musu drinks tazo ta ajiye akan center table.
"Ina mijin naki yake?" Abuh daya d'aura k'afa d'aya kan d'aya yana jijjiga wa ya jefa mata tambayan.
   "Bacci yake" ta had'a k'aryan nan take cike da tsananin fargaba da tashin hankali.
"Saboda mahaukaciya ce ke baki san ciwon kanki ba shine zaki cika masa gida da kid'a haka?" Question ta Ummy tai hitting ta.
   Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa dan batasan ma me zatace ba.
"Dan uwarki ba magana nake miki ba? Mijin ki na bacci ki cika masa gida da kid'a Huh! Haka kika ga anayi? Nace haka kika ga anayi?" Ta buga mata shegen tsawan daya sa ta kusan sakin fitsari a wando.
    "Umm...umm wallahi Ummy!.. " sai kuma tayi shiru dan tama rasa k'aryan had'awa.
"Wallahi me?" cewan Ammey itama rai a b'ace.
     "Wata sabuwa!" Ta fad'i a zuciyan ta dan tai tsammanin Ammey zatai siding ta sai taga akasin hakan.
Shiru tayi ta sunkuyar dakai k'asa tana nanata innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un, dan ta tabbatar da yau ruwa ya k'are ma d'an kada, tana a wannan halin Abuh ya d'au hanyan d'akin nasu, ai in an eye blink sai gata a gaban sa tana faman zare blue eyes natan, tana zufa sosai tace "Abuh Dr ya hana a tada sa in yana bacci! And wallahi kana tab'a k'ofan d'akin zai tashi".
D'agowa yai ya bita da wani shegen kallo kafin ta fuskanci mai yake shirin yi ya tsinke ta da wani firgitaccen mari, k'aran data kwala yasa Suwayd runtse ido cike da tashin hankali dan du conversations nasu a kunnen sa.
A tsawace yace "Idan an kunna kid'a ne baya tashi ko? Answer me! Nace idan an kunna kid'a ne baya tashi?"
Girgiza kai ta shiga yi cike da tsananin tashin hankali hawaye kuwa kaman an bud'e lalataccen tap.
"Bani hanya in wuce kafin na karya ki! Wawiya kawai"
   Da sauri ta matsa jikin ta na tsananin kakkarwa, a time d'in du addu'an daya zo bakin ta yi take saboda tsabar tsoron halin da za'aje a iske sa.
"Innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un " Abuh yayi ex claiming da k'arfi hakan yasa Ammey da Ummy nufan d'akin da sauri.
      Abinda suma suka gani ne yasa suka soma nanatawa cike da tashin hankali, Ummy can't help har sanda ta fashe da kuka cause she just can't believe first class d'an gayu, mai tsafta, classy, arrogant Suwayd ne ya koma haka.
Ammey kuwa tsabar mamaki ma ko motsawa ta kasa sai hawaye.
Rufe ido Suwayd yayi cause bare iya had'a ido dasu ba a halin da yake ciki na najasa.
Kallon su Abuh yayi da jajayen idon sa yace "ku bamu guri".
Jiki a sanyaye suka koma falour, buga d'akin da Safwah tayi locking kanta ciki Ummy ta soma yi amma tak'i bud'ewa.
   Gyara sa Abuh yayi ya kwantar dashi, ganin yadda yake wahalallen numfashi Abuh ya zauna a gefen sa da sauri ya rik'o hannun sa yace "Lafiya Babana! Jikin ne?"
Girgiza kai yai yayi yana hawaye dakyar ya daure yace "Abuh yunwa nakeji, ka taimakamin da ruwa zan mutu".
     "Harda Horon yunwa take maka? Innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un".
Mik'ewa yayi da sauri ya fita fuska a had'e ya kalla Ummy yace "ki kawomin tea idan zaki samu dama".
      Cike da mamaki ta d'ago tana kallon sa tai saurin mayarwa k'asa ganin kallon da yake binta dashi, mik'ewa tayi jiki a sanyaye dan cika umarnin sa.
Bata wani d'au lokaci ba ta had'o ta fito, ganin basa falour ta wuce d'akin, har k'asa ta durk'usa ta mik'a masa yaja tsaki kawai ya karb'a.
Tsorata Ummy ta soma yi ganin sababbin abubuwan da Abuh ke mata, tsinkayo muryan sa tayi yana cewa "kije ki dafo abinci mai sauk'i in zaki iya!"
Mik'ewa kawai tayi ta fice tana jin mugun takaici a ranta ganin tana ji tana gani laifin d'iyar ta zai shafe ta, jallof macaroni ta had'o ta kawo.
Kafin ta kawo Suwayd harya shanye tea d'in, Abuh ya jingina sa da gado yana maida numfashi, karb'a yai ya soma feeding Suwayd, ganin har Allah_Allah yake Abuh ya mik'o masa jikin Ummy yai wani irin sanyi.
Duk yawan abincin nan sanda ya gama masa aiki, ruwa kam yana sha yana zubarwa gwanin ban tausayi, sanda yaji ruwan da abinci dayaci na k'ok'arin dawo masa ya hak'ura da sha.
     Mik'ewa Abuh yai batare da ya kula su ba ya fice yai saurin miyar da k'ofan yai locking, da sauri Ammey ta taso ta soma magana "Abuh'n Safwan dan Allah karka yanke hukunci cikin fushi! Saboda Allah ka bari karka yi".
Ko nakan ta baiyi ba ya wuce d'akin da Safwah take ya soma bugawa, tana ciki cike da azaban ciwon maran ta daya dad'u saboda tashin hankali, kuka ta soma yi tsakanin ta da Allah jin abinda Abuh ke cewa.
     Bata da option daya wuce tasowa jikin ta na tsananin rawa ta bud'e, fuzgo ta Abuh yai da k'arfi yana mai tuna halin daya iske mijin ta, wayan chaza ya finciko ya soma cin uban 'yar banza, sanda ya mata dukan daya san bazata moru ba ya kyale ta.
Ihu kuwa tun tanayi anaji harta daina, Suwayd kuwa nacan ya runtse ido dan shi kad'ai yasan mai yake ji a zuciyan sa.
Komawa Abuh yai ya bud'e d'akin, da sauri Ammey tai falour'n, chak ta tsaya tana kallon Safwah da jini ke bin k'afan ta "Miscarriage!" Tai ex claiming da k'arfi ko lura da girgiza mata kai da Safwah keyi batai ba saboda tsabar rud'ewa.
"Miscarriage!" Suwayd ya nanata a zuciyan sa hankali a matuk'ar tashe, "NO! Hell NO!" Ya fad'a da k'arfi jikin sa na wani irin rawa.
Kansa Abuh yayi amma ina harya riga ya sume, juyowa yayi ya kalli Ummy dake hawaye yace "Wallahi kin dai ji na rantse muka dawo daga asibiti nagan ki keda 'yarki a gidan nan in fact ma k'asar gaba d'aya a bakin auren ki!!" Yai saurin d'auke Suwayd suka fice.
Ammey dake tsaye kan Safwah ta rasa abin yi da sauri tabi bayan Abuh, a gate suka had'e da Zee tai joining su. 
In less than fifteen minutes suka isa asibitin aka wuce da Suwayd dan basa taimakon gaggawa.
Da sauri Ummy ta dafe bango jin jiri na k'ok'arin yasar da ita, ahankali ta zame k'asa ta had'a kai da gwiwa ta soma rera kuka gwanin ban tausayi, iya tsawon zaman ta da Abuh bata tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, ta dad'e tana kuka kafin ta mik'e ta fad'a toilet ta wanko fuskan ta, jakanta ta d'auka tai adjusting position ta hijab d'inta ta fito falour'n, tsayawa tai kan Safwah'n tace "minti biyar na baki ki shirya mu tafi, idan kuma kika k'ara wallahi tafiya ta zanyi inya so idan yazo ya same ki kyasan yadda zaki yi sha_sha_sha kawai".
      Dakyar Safwah take fidda numfashin wahala ta iya mik'ewa tana tangad'i wane bugaggiya ta shiga d'akin, tai saurin watsa ruwa ta sauya kaya ta jawo trolley d'in ta tana kuka ta jona Ummy suka wuce.
Gaba d'aya hankalin Zee ya kasa kwanciya sai safa da marwa take, kallon ta Abuh yayi yana jin k'aunar ta na ratsa sa yayin da zuciyan sa ke cike da bak'in cikin Safwah.
   Suna a wannan halin aka fito dashi zuwa d'akin hutu, da sauri suka nufa d'akin.
Zama Zee tayi a gefen sa ta rik'o hannun sa ta had'a da nata ta tsare sa da ido tana kallon yadda yai bak'i ya rame wane bashi ba.
      Hawaye ne masu zafi suka kwarinyo mata Ammey tai saurin dafa ta tana girgiza mata kai saboda nata situation d'in itama.

MAKAHON SO _Blinded Love_Donde viven las historias. Descúbrelo ahora