Episode 25

2.4K 112 6
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 25
4_12_2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Neman kujeran kusa da ita yayi cike da takaici ya zauna, duk wanda ya kunno kai wurin Safwah da yaci karo da fuskan angry Suwayd sai ya juya but still sai da aka samu masu k'arfin halin cewa Suwayd sunga k'anwar sa suna so.
      Jarababben kishi yasa yace sai ta tashi sun tafi, badan ranta yaso ba ta mik'e yasa ta agaba suka wuce.
Yana gwada cewa bari ya chanza hanyan gidan Safwah ta soma kuka tana rantse_rantsen ita bata fad'awa kowa ba, yadda ta k'ank'ame hannun sa yafi komai basa dariya amma ya moze, ya tsaida motan a road side ya had'e rai yawa pregnant sky.
" Ke!! "
Da sauri ta d'ago tana kallon sa da kumburarrun idanun ta, murya a dishe tace " Na'am ".
     " Ki bud'e kunnen ki kiji, kin riga kinyi promise and no backing out, da bakin Ki kikace if you break the promise na miki duk abinda naga ya dace right? "
Saurin gyad'a masa kai tayi jin yadda ya murd'a mata kunne cike da mugunta ta sake siririn k'ara idanun ta na cikowa da kwalla tace " Eh na fad'a ".
      " Good girl, now listen to me very careful duk wanda kika yi kuskuren fad'awa hukuncin ki shine aure na ko kina so ko bakya so and karkiyi tunanin da wani manufa zan aure ki, zan aure ki ne dan inyi making life naki miserable hell saboda sirri na da kika sani, in fact ban tab'a kallon ki a mace ba balle kiyi tunanin ko wani abu naki yaja hankali na nake son na aure ki not at all zanyi hakan ne dan na cigaba da muzguna miki har k'arshen rayuwar ki, am I clear? "
Cike da tsananin tsoron sa tace " Ya Suwayd aure? "
     " Yes ko kina tunanin wasa nake?  Oya try me and see ".
" I need a favor " tayi maganan tana kuka sosai.
" Bazan yi ba " ya answer ta finally.
Cusa kanta tayi tsakankanin cinyoyin ta tashiga rera kuka abin tausayi sosai taji dad'in kalamun sa at the same time kuma tsoron dalilin da yasa zai aure ta, agaban iyayen ta ma bai rangwan ta mata ba balle ta zamo a k'ark'ashin sa bazata iya b'oyewa Safwan ba cause shine abokin shawaran ta, ya zamo mata dole ta shaida masa dan bata da mafita a wannan al'amarin dake shirin faruwa da ita.
     Tsawan daya buga mata ne ya sanya ta yin shiru ta koma jera ajiyan zuciya, har suka isa gida ba wanda ya sake magana.
Part d'in su ya wuce cike da farin ciki ya dannawa Abdul k'ira, yana d'agawa ya fuskanci how happy Suwayd is.
     " Maza!! Nagode, nagode sosai words can't describe how much you mean the world to me, shawara ka have sort things out ".
" Don't tell me mutumina ".
" Ka bari kawai na riga na gama da ita again yanzu haka na samu solutions wa Granny's issue ".
" Fad'amin ya hakan ta faru so easily? "
     Nan take kuwa ya masa narrating all that happened cike da tsantsan farin ciki. 
" Na tayaka murna mutumi na ai dama na fad'a maka da kayi attempting raping ta ko sanya ta shaye_shaye zata tsorata, so yanzu kana tunanin zata fad'ama wani har ka samu daman tilasta ta auran ka? ".
" Yes I have once tell you duk duniya bata b'oyewa Safwan damuwan ta so zanyi amfani da wannan daman na sanya ido akan ta, dan duk lokacin da tayi abin rashin gaskiya I use to understand it by her actions, kaga na gama da wannan sai dai inajin tausayin Sayyid sosai bansan kuma ya zai d'auki lamarin ba dama su Abuh bansan ya zasu kalla abin ba? ".
" Karka wani damu kanka Granny na k'aunar ka sosai kasan yadda zakayi ka sata basu umarni ba shawara ba, Sayyid kuma is so cool nasan zai yarda da k'addara amma wallahi Safwah na bani tausayi ina jiye maka tsoron ranan da zaka shiga hannun ta, yanzu kai ke playing role naka nan gaba kuma ita zatayi dan nasan da zaran ka mallake ta you can't hide the love you have for her anan ne zaka gane baka da wayo maza, ni wallahi when the time comes ma Nigeria zan dawo na dinga kallon show ".
" Lmao you are so funny wallahi dana mallake zuciyan ta shikenan na gama da ita dan nasan ita abinda zatayi ma sai yafi na Zee ".
Dariya sosai Abdul ya tsaya yi kafin yace " Ohhh haka kace? "
     " Ai hakan ne ma " yayi answering confidently.
" Shikenan Allah ya kaimu lokacin zan tuna maka kalamun ka word by word insha Allah, now back to business Musty na nan yana fama da kansa tun wuri ka koma shan hankali if not wallahi you will regret all this shit ranan da nadaman bare ma amfani ba ".
       " Subhanalla meya same sa? "
" Sunce dai k'odan sa ya soma samun matsala sai appendix, yanzu ma aiki aka masa ".
     " Innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un yaushe haka ta faru baka fad'amin ba? "
" No need to tell you tunda kaima lokacin you are not in a good situation and karka damu fa yaji sauk'i dan harya koma ruwa, na d'au ma zai rage amma kaman k'ara masa akai dan sai abinda yayi gaba ya riga ya zama so addict shiyasa yake so ku taru ku zama d'aya ".
     " Zan shigo insha Allah next week ".
" Wow kace Ghana zatayi bak'i ai kuwa ba kanta ".
     " Kai dai ka bari sai na shigo kawai ".
Hira suka yi sosai sannan suka kashe wayan.
Da sauri Mammy tabi bayan Safwah ganin yadda ta shigo a hargitse, tana shiga ta iske ta flat tayi ruf da ciki akan gado tana rusa kuka wane wadda akace uwar ta da uban ta sun mutu, gashin ta duk ya barbaje kaman zararriya.
Ahankali Mammy ta k'arasa ta d'agota ta janyo ta jikinta ta soma aikin rarrashi, dakyar ta samu tayi shiru sannan ta d'ago ta suna fuskantar juna, sai da ta had'e hannayen su gu d'aya sannan ta soma magana " d'ago ki kalle ni Baby ".
D'ago da jajayen idanun ta tayi ta d'aura su kan na Mammy tana ta jera ajiyan zuciya,hakan kad'ai ya isa shaida maka yadda taci kuka ta gode Allah.
Cike da kulawa tace " me yake damun ki? me yasa kullum kike kuka? Kina kallon kanki a mirror kuwa dubi fa yadda kika bi kika rame alamar bakya tare da kwanciyar hankali me yayi zafi haka? Fad'amin kar kiji tsoro insha Allah damuwan ki yazo k'arshe ko Ya Suwayd n.... "
   Ai bata bari Mammy takai k'arshen zancen ta ba tayi saurin tare ta " A'ah wallahi Mammy mara na ke ciwo " tayi maganan tana fashewa da matsanancin kuka.
Murmushin takaici Mammy ta sake tace " Halayyan ki sun soma chanzawa Safwah why? Meyasa kike min k'arya? Saboda ni ba Ummy bace? "
     Girgiza kai ta somayi tana kuka sosai " A'ah Mammy tsoro nakeji bana iya bacci sosai da zaran na kwanta nake soma mummunan mafarki, shiyasa kika ga du na zama haka... "
Kukan da yaci k'arfin ta ne yasa ta yin shiru, janyo ta Mammy tayi jikin ta cike da tausayin ta sannan ta soma magana a nitse " kici gaba da addu'a kinji Allah yana tare dake, kukan nan da kike was never a solution kinji? "
   With nod ta answer sannan Mammy ta mik'e ta shiga toilet ta had'a mata ruwan wanka, sai da tayi wankan ta fito ta kwanta bacci sannan Mammy ta tofe ta da addu'o'in tsari ta tafi.
Juyi tayi tayi har bacci ya d'auke ta.
Washe gari aka k'are biki aka kai amare su Safwah sun sha kukan rabuwa da Samha saika ce wadda ta tafi kenan har abada.

MAKAHON SO _Blinded Love_Onde histórias criam vida. Descubra agora