Episode 44

2.9K 148 63
                                    

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
 . ❉ .¸¸.✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ .¸¸.❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆'-
...¸.¤ª '☆'_____________☾_____________-'☆'-
💕💞 MAKAHON SO💞

Blinded Love
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯...¸.¤ª☆"˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆"˜¨''¨ '''_*Written By Beelkeey Shuwerh_ ''* "˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆'
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯...¸.¤ª☆"˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆  
¸.¤ª☆"˜¨•。❉ .¸¸.✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ .¸¸.❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ .¸¸.❄*.¸¸*❆

Wattpad @Shuwerh Beelkeey22

*In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 44
16_4_2019
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Tun Suwayd na d'aukan abin na Zee da wasa harya dena ya koma aikin rarrashi buh the more yake tausan ta the more qanwar mamarta ke zuge ta, still yauma suna zaune shi yana zaune da little Safwah a laps nasa yana aiki a laptop ita kuma tana can zaune kan gado ta had'e giran sama da qasa wane bata tab'a dariya ba, murmusawa yai ya cigaba da abinda yake sanda ya gama tsaf ya mik'e ahankali yadda bazai tayar da Little ba ya kwantar da ita then ya qarasa kusa da ita ya zauna, banza tayi dashi wane wani trash daman yasan haka zata faru dan haka ya ajiye pride and ego nasa ya riqo hannayen ta yana wasa da yatsun ta.
Qoqarin kwacewa ta soma amma ta kasa dan riqon dayama hannun bana wasa bane, surutu yata zuba mata amma ina Zee tayi nisa batajin kira dan kaman dutse haka ta zama harya qaraci abinsa ya qyaleta.
Daren ranan bata rintsa ba tana aikin saqa da warwara cause time na tafiyan qara matsowa yake, har aka qira sallah ta gaza samo solution dan haka ta yanke shawaran qiran qanwar mamarta da safe, saida tayi sallah wahalallen bacci yai gaba da ita.
The following day, da wuri ta qira Aunty'n tata ta irga mata halin da ake ciki, nan ta sake bud'e sabon babin zuge ta aikuwa luckily ta sake hawa kai ta zauna, cikin sati d'aya Sam Suwayd ya kasa gano kanta dan gaba d'aya ta sake birkicewa, abinda yafi qona masa rai shine sometimes yana fad'a tana fad'a dan haka ya fice harkan ta gaba d'aya.
Haka al amura sukai ta faruwa har Allah ya kawo wannan rana da wasu kejin tsoro wasu ke jin takaici, already sunyi sallama da kowa qarfe biyar duk yadda Suwayd yaso Zee ta saduda suyi sallaman arziqi taqi dan haka kawai ya ajiye mata kud'i ko wani buqata zaizo suka tafi, mutane dayawa aka musu rakiya anata yi musu fatan nasara, Safwah banda kuka Babu abinda take dan sosai Zee ta bata tausayi.
Qiran passengers da aka soma yasa Suwayd riqo hannun ta suka wuce suna waving ma familyn nasu hannu har suka shiga jirgi, tunda suka zauna banda kuka Babu abinda Safwah keyi da tunanin halin da Zee ke ciki har bacci ya d'auke ta, Zee kuwa kuka ta shigayi tsakani da Allah haka har Hafsa tazo ta same ta.
Shafa hannun ta da yake ne yasa ta farkawa duk idanun ta sun mata nauyi saboda yadda tasha kuka, sanda ta nutsu ta soma bin ko ina da kallo only to find kowa ya fice sai su, murmushi ya mata ya miqar da ita suma suka fice, abokin sa dake jiran su nan take ya qaraso suka gaisa yasa kayan su a mota suka shiga yaja suka tafi, had'ad'd'iyar flat d'insu ya wuce dasu suka soma wanka sukaci abinci suka bi lafiyar gado.
Sai almost nine suka tashi, sallah'n magrib da isha suka soma yi suka qaracin abinci ya chanza layin wayan sa ya qira gida, saida suka gaisa da kowa ya soma qiran layin Zee though yasan ba d'auka zatayi ba, k'a idan sa da mutum three missed call amma yau sai gashi yama Zee har goma tak'i d'agawa, haqura yai ya qyale ta suka wuce zasu kwanta nan Suwayd yace bai san zance ba dan tun Ana saura sati biyu tafiyan su yana tare da Zee, du yadda taso yabarta yaqi dole ta haqura takoji maza dan gyara na musamman su Mummy suka mata kafin su tawo, time in daya qyaleta ko hannu bata iya d'agawa wanka ma sai shi yayo mata suka kwanta.
Without any hesitation ya soma mata processing komai, nan take komai ya zamo perfect suka soma abinda ya kawo su, karatu suke cike da burgewa dan kowa yasan su cikin makaranta as the best perfect lovely couple ever.
Du hutun sa a Nigeria yake tare da Zee yadda yake nuna mata zallan so da qauna yasa ta manta du wani zuga ta kama mijin ta hannu biyu, Little Safwan da Safwah kam sai girma suke gwanin burgewa yayin da kyansu ke qara fitowa, sam babu abinda little Safwah ta baro ana mamarta yayin da little Safwan ba abunda ya baro ana Safwan.
As life moves on yanzu just a month ya ragema Suwayd abinda ya kawo sa yayin da Safwah Keda two years ahead, du tunanin Suwayd bai wuce yadda yana ji yana gani zai bar *Flower* d'insa ba ya tafi, cikin wannan watan ba abinda suke fuskanta a makarantan dan du wani lokacin su ya tafi gurin ririta juna, she never believes dagaske tafiya zai ya barta sai ranan, she cries so much lokacin da yake hawa steps na jirgi haka har suka tafii, ranan kwana tayi kuka buh tuna promise d'in data masa na giving her goddamn attention wa karatun ta yasa ta rarrashi kanta ta zama strong.
Karatu take sosai yayin da kullum suke cike Video call.
Tsayin shekara da tafiyan sa kenan amma ko sau d'aya baiyi visiting ta ba, tun tana qorafi harta gaji ta zuba masa ido yayin da in missing sa ya isheta sandai ta zauna taci kuka ta gode Allah, qoqari da basirarta yasa duk wani school competition sai kajiyo ta aciki yanzu duk duniya damuwan ta d'aya rashin haihuwa ganin almost four years kenan da auren nasu amma ko b'atan wata bata tab'a yi ba.
At Zee's side wani irin farin ciki take ciki ganin ko ta tambayi Suwayd when zaije gurin Safwah yana shashantar da zancen not knowing that tsaf ya gama shirin tafiyan cause an yaye little Safwan zai kai mata shi yanda zasu saba sosai kafin ta dawo, ana hakan Zee ta fuskanci tana da wani cikin dan tare suka yaye yaran.
Da farin ciki ta fad'awa Mum inta ita kuma ta shaida ma Aunty'n ta, a ranan kam ta qira ta dunga zigata wai inhar baso take ta tsufa ba ta zubar da cikin, yanda ta dinga nuna mata Suwayd da Safwah had'a baki sukai sukayi planning dan karta tsufa yasa ta hau ta zauna , da yamma kuwa sai ga tabs ta tura yarta ta kawo mata batare da tsoro ko tunanin komai ba ta bankawa cikin ta, qarfin kwayoyin yasa ko minti sha biyar batayi ba ta fara bleeding kafin wani lokaci gaba d'aya ta fice cikin hayyacin ta, luckily time na dawowan sa yayi dan haka yana shigowa ya same ta a wannan mawuyacin halin, bai tsaya b'ata lokaci ba ya d'auke ta suka wuce asibiti.
Emergency ward akai da ita likitoci suka rufa akanta dan bata taimakon daya dace, sunfi two hours kafin su samu su tsayar da bleeding d'in sai dai tun kan suzo cikin ya riga ya zube, saida aka mata wankin mara aka fito da ita zuwa d'akin hutu.
Lokacin da Dr Alkasim ke masa bayani ko tsayawa gama ji baiba yabar asibitin gaba d'aya, rai a matuqar b'ace ya had'o kayan little Safwah ya d'auko ta daga gidan Sayyid ya wuce ya d'auko Little Safwan ya wuce kai tsaye dama flight in ranan zai bi, da qoqarin wani friend d'in sa ya samu yai ma Little Safwah Visa qarfe takwas Jirgin su ya d'aga.
Safwah na zaune a falour tana hutawa tana murnar gama jarrabawan da sukai ranan ta jiyo doorbell, bata wani tsorata ba sanda ta kalla time taga yanda dare yai, take ta soma tunanin to waye dakyar taja jiki ko hijab bata sanya ba in fact tama manta kayan dake jikin ta taje ta bud'e, surprisingly ta tsaya da baki wide open tana kallon su.
Wasu pathetic looks da yake jifan ta da yasa ta had'iyan yawu dakyar dan sai lokacin da tuna me ajikin ta gashi ta masa promise no matter what in zata bud'e qofa zata sanya hijab, jikin tane yayi wani irin Sanyi ta sunkuyan dakai tana wasa da yan yatsun ta looking pitiful.
Bai kula ta ba ya sake hannun yaran ya wuce ciki, durqusawa tai ta bud'e musu hannu sukai hugging ta, breaking hug in tai taja su suka shige ciki suma, d'ayan bedroom in ta wuce da su ta soma yi musu wanka suka dawo falour ta zuba musu abinci.
D'akin da yake ta shiga ta same shi ya shirya yai flat akan gado ya zurawa ceiling ido, ahankali taja paralyze legs nata ta qarasa ta zauna ta side, dakyar ta iya gathering courage ta soma magana " *Habibi* please am sorry wallahi it was not intentionally.."
Shiru tayi ta tsaya tana kallon sa taga ya yake d'aukan zancen amma yadda tai noticing bai ma san tanayi ba nan ta gane lallai ba laifin data yi ne yasa sa b'acin rai haka ba.
Ta miqe zata fita ya riqo hannun ta kafin ta fuskanci abinda yake shirin yi ya fuzgota ta fad'a kansa hugging her so tight, yanda yake sauke ajiyan zuciya akai_akai yasa hankalin ta tashi amma zata bari Harya sauko saita tambaye sa damuwan sa jin ana buga qofa yasa tai saurin Zame jikinta ta miqe kafin ta gama saita nutsuwanta yaran sun kunno cikin d'akin, murmushi Suwayd ya musu ya nuna musu kusa dashi suka qaraso kan gadon ya qanqame su not long enough bacci ya d'auke su both, qare musu kallo tayi ta fita ta gyara inda sukaci abinci ta zauna tana tunanin rayuwa, tuno Safwan d'inta yasa gaba d'aya ta fita daga nutsuwanta ta soma sana ar tata ta kuka saida tai mai isarta ta miqe ta d'auro alwala ta tayar da Sallah, bayan ta idar ta dad'e tana masa addu'a har bacci ya d'auke ta agun.
Qarfe uku Suwayd ya farka ahankali ya zame yaran ya fice nan ya hangota kwance gefen kujera ta takure, d'aukan ta yai ya wuce d'ayan bedroom d'in ya rungume ta sukayi bacci.
The Following day
Duk sun riga ta tashi, tana tashi ta soma qoqarin had'a musu breakfast bayan sun karya tama yaran wanka ta wuce itama ta shirya, simple make-up tai applying ta same sa a d'aki a nitse ta soma tambayan sa amma sam yaqi fad'a mata exactly what is bothering him, mayar ma da laifin kanta yai bataji maganan sa ba in zata bud'e qofa bata sanya hijab, cike da kissa ta bashi haquri suka manta da komai.
One month ya mata ya tafi yabarta da yaran kasancewar tana da Nanny yasa take bar mata yaran in zata tafi school, in ta dawo kuma ita kanta bata da lokacin kanta saina yaran, yarda yaran ke qaunan Juna ya tabbatar mata lallai Little Safwan bazaiyi maraici ba.
Tunda ya koma ko takan Zee baibi ba dan tana gida ma ta kuma fad'ama iyayen ta duk abinda ya faru, jin haka yasa Dad inta yai fishi da ita ya kuma tsorata ta da sai yasa Suwayd in ya sake ta, hakan yasa hankalin ta mugun tashi gashi kullum cikin kiran sa take baya d'auka.
Saida Granny tasa baki ya yarda yaje ya d'auko ta daga gida amma kowa harkar sa yakeyi.
Musty duk qoqarin sa yanzu bai wuce mallakar Kadsah ba amma ina Sam ita baya gaban ta dan inya fara mata maganan aure ma kuka take masa hakan yasa ya kyale ta yai magana dasu Granny suka roqi daya qara mata lokaci.
A kwana a tashi babu wuya agurin Allah yau Safwah ke rubuta final paper inta farin ciki Sam yaqi barin ta yau burin ta ya cika ta kammala karatun ta, gagarumin party ake had'a mata acan gida Wanda Sam bata san dashi ba.
Saida ta had'a takardun ta da komai ta had'o ya nata ya nata tayo qasarta , kowa sai yaba kyau da girman data qara yake, mamaki tata yi da taga yanda yaran su Ya Sadeeyq suka zama 'yan mata yaran su Sayyid ma duk sun girma yayin da nata yaran Keda shekaru uku, dawowanta ya mugun yiwa Zee dad'i ko bakomai zata sa ya yafe mata laifin da tayi tunda haryanzu yaqi sakkowa.
Kwana biyu da dawowanta akai k'ayataccen Partyn suka koma makeken gidan su da Suwayd ya gina Wanda Zee Sam bata da labarin sa, ranan da Safwah ta cika sati da dawowa Zee ta same ta tafad'a mata duk abinda ke faruwa, sosai taji tausayin ta dan haka a daren ranan ta same sa da kuka ta bashi haquri, kukan da take da abinda take fad'a yasa tausayin ta kamasa ya haqura ya yafe ma yar Uwar tata suka koma living happily ever after.
Two Months Later
Safwah da Zee zaune a babban falour suna hira gwanin burgewa, tunda suka zauna ta lura da hamman da Safwah take jerawa kafin wani lokaci bacci ya d'auke ta, mamaki ne ya cika ta dan gaba d'aya Safwah ta chanza wane wata me sleeping sickness ba daman a zauna hira da ita sai bacci, ga shegen tsurfa da masifa wanda Sam da bata dashi, bata kawo komai a ranta ba ta qira Suwayd ta fad'a masa ko minti goma ba ayi ba sai gasa tsaban mamaki ma kasa kula sa tai ta zuba ma sarautar Allah ido........

~One Word For Safwah's Sleeping Sickness?~

Follow
Vote and
Comment on Wattpad
@Shuwerh Beelkeey22

MAKAHON SO ~Blinded Love~
#MS

*'Yar Gatan Miss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_On viuen les histories. Descobreix ara