Episode 13

1.8K 104 3
                                    

.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*❤
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆


® *REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

    # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

   *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

_To you sweetheart Mamugee hak'ik'a ina taya ki murnan kammala daddad'an novel naki *EZNAH* tabbas ya fad'akar ya kuma nishad'antar damu, Allah ya bamu ikon amfanan sak'on da kike so ki isar Amin, Allah ya k'ara basira da kwarin ido Much love dear_

Episode 13
October, 2018

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Har suka isa gida ya gaza sama musu solution, he has no option than to stay with her no matter what it takes,  luckily da suka zo gate man yaje sallah without any hesitate ya wuce da ita part nasa batare da sanin kowa ba.

Suna shiga falour'n ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa dake tsanin sarawa da but hands nasa, tunanin sa bai wuce yadda zai soma shaidawa Mummy da Daddy yayi aure ba batare da sanin su ba.

Safiyya kam zamewa tayi ajikin k'ofan d'akin tana rera kuka mai ban tausayi.

Ringing ta wayar sa ta sashi mik'ewa yabar falour'n ya nufa bedroom, crying Sadiya ce ta kira gashi duk yadda yaso rarrashin ta abin ya faskara, kukan nata ma har ya wuce na hankali da tasan matsanancin halin daya ke ciki da bata saka sa a gaba da wannan kukan nata ba.

Kashe wayan yayi ya shiga nanata innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un ko yaji sauk'in rad'ad'in da zuciyan sa keyi, sai da ya d'auka tsawon lokaci sannan jiki a sanyaye ya nufa toilet ya sakarwa kansa shower.

Sai da ya d'au about 20 minutes sannan ya fito ya sanya kaya ya shimfid'a sallaya ya fuskanci alk'ibla, koda ya idar kasa tashi yayi a wurin ya shiga rok'on Allah ya bashi ikon cin jarrabawar daya jarabce shi.

Mik'ewa yayi ya haye gado abinsa dan ya sama peace of mind sai dai daya rufe ido innocent crying face na Safiyya yake gani, nan take kalamun mahaifin ta suka soma mar yawo aka, wane an mintsile sa ya mik'e ya nufa falour'n.

Kwance ya hango ta tana bacci a wahalance jikin ta banda rawa babu abinda take tayi matashi da hannun ta, one more look ya sake yi mata ya tabbatar da zazzab'i ajikin ta dan yadda ta k'ank'ame jikin nata wane mai tsoron za'a gudu da ita.

Ahankula ya mik'a hannun sa yana son tada ta amma ya kasa gashi baijin zai iya d'aukar ta, na sosai ya shiga k'are mata kallo " ba laifi she is cute " ya fad'a a zuciyan sa sannan yayi saurin mik'ewa.

K'afan sa yasa ya shiga shurin ta harya samu ta farka a firgice, addu'a tayi ta mik'e zaune ta sunkuyar da kanta k'asa jikin ta na rawa the more.

Tsuka yaja ya kalle ta yace " ga d'aki can kije kiyi wanka dan bansan k'azanta, sannan inhar kina so mu shirya ki san mutuncin addinin ki ".

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now