Page 17-18

278 11 2
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

18

Tana zaune tana kuka tana k'arewa d'akin kallo, babu abinda ke cikin d'akin daga tabarma da bakko a gefe sai akwatunanta.

Har lokacin kuka take tana fad'in "na cuci kaine dana k'i bin shawararka Abba"

Jakarta ta janyo ta bud'e ta d'auki wayarta ta fara neman number Mameey,kawai ji tayi an fuzge wayar d'ago kai tayi kawai taga Umma ce.

Da sauri ta mik'e tsaye tana kallonta ido cikin ido.

"Ubanwa zaki kirawo da wayar?".

Shiru tayi bata ce komai ba,da mamakinta taji ta wanketa da mari.
" nace ubanwa zaki kirawo da wayar,munafuka kin tsareni da ido kina neman cinyeni"

Babu abinda Janan take sai kuka,wannan wace irin jarrabar rayuwace,tana tunanin tayi aure ta huta ashe ba haka bane.

Fita Umma tayi ta barta tana kuka tamkar yarinya.

Kusan magriba sai ga Aliyun ya shigo da wata katifa number 1, da kanshi ya ajjeta ya shinfid'a bedsheet ya ajje pillows sannan ya d'auki labulen k'ofa tare dana taga ya saka,sai a lokacin ta gane katifan tace extra da Mameey ta siyo bedsheet da labulayen tasan duk nata ne,ta tabbata anan zata zauna.

Sai daya gama tas yana shirin fita tayi saurin shan gabansa.

"Aliyu ban cancanci haka a gurinka ba ka tausaya min dan Allah, idan ma wani abu maihaifina yayi maka ka yafe masa karka manta Allah yana son mai yafiya"

Har ta gama maganar idonshi a kanta bai d'auke ba,kusan minti biyu sannan ya fara k'ok'arin bin gefenta ya wuce.

Tayi saurin sake tarar gabanshi,aikuwa ya saka hannu ya buge ta,fad'uwa tayi har k'asa cikin jin azaba da rad'ad'in ciwo,sunkuyawa yayi daidai saitinta ya d'an jona hannunsa akan hancinsa saboda idon ta a rufe yake.

"Oh ashe kina da numfashi,dan bana son ki mutu bakiga yadda zan k'ask'antar da mahaifinki ba"

Tashi yayi ya fice kawai,tana nan kwance kanta na sarawa tana d'an jin hayaniya sama-sama Umma na ta zaginta.

Tafi awa a kwance a gurin sai da taji an fara kiran sallar magrib sannan ta tashi jikinta na rawa alamar zazzab'i na son rufeta.

Tsakar gida ta fita da niyyar tayi alwallah,buta ta hango ajiye jikin randunan ruwa,ta nufi gurin ta d'auki guda d'aya tana shirin ta bud'e randar ta d'ebi ruwa caraf taji an rik'e hannunta.

'Dagowa tayi dan ganin ko waye.
"Bazaki d'iba ba tunda bake kike mana jigilar d'aibo ruwa ko siyan ruwa ba"

Mamaki take yadda Ummi take gaya mata magana kai tsaye,ta tuno lokacin da taje gidansu tana kuka an rufe mata d'an uwa a cell.

"Mamaki kike ko?to bari kiji wannan somun tab'i ne idan har kina raye sai kinga yadda ubanki zai rik'a bara a kasuwa yan.............." Mari Janan ta wanketa dashi cikin jin zafin cin mutumci da take neman yi mata.

A zafafe Ummi ta d'aga hannu zata rama Janan tayi saurin rik'e hannu ta wullar gefe tare da shak'o wuyanta ta matse ta jikin bango.

Wani ihun azaba da kururuwa Ummi tayi wanda ya saka Umma fitowa daga d'aki a guje.

"Ke kashe ta zakiyi?"

"Rai ba a hannuna yake ba amma ina mata gargad'ine"

Ummi sai k'ok'arin k'wace kanta take amma ta kasa,Umma sai dukan Janan take tana fuzgarta amma tak'i sakin Ummi har ta kai mak'ociyarsu ta lek'o ta katanga da yake bata da tsayi,ganin tak'i sakinta ne yasa mak'ociyar ta zari hijabi ta fito,Aliyu da Nura ta tarar kan taya suna shan rake ta fad'a masu abinda ke faruwa da sauri suka shigo gidan.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now