26-27

272 15 5
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

*_'Kawata Amarya Khadija,a gaskiya abinda kika zo min dashi yau bazan iya musulta farin cikin danaji ba,har na cire ran zan samu  saboda yadda nasha nema na rasa,ashe abin yana ranki har sai da kika samomin,zazzafar k'auna ce wannan,na yarda ke mai k'auna ta ce,fatana Allah ya saka miki da gidan aljanna ya biya miki dukkanin buk'atunki ya k'ara dank'on k'auna tsakaninki da maigidanki,ya k'ara dank'on zumunci tsakaninmu._*
'''Nagode matuk'a'''

26

A babban falon gidan ta tsaya tana zazzare ido tana kallon mutanen dake zaune.

A hankali ta fara ganin ko ina yana juya mata,cikin kuka ta furta "Mameey kina ina?ki fito ki fad'a min gaskiya Abba na san bai mutu ba" sai kuma ta rik'e gashinta ta sulale k'asa.

Salati aka hau yi,haj Mariya tayi saurin zuwa suka kamata aka yi d'akin bilkisu da ita.

*_Few minutes ago_*

Idanunta ta bud'e gaba d'aya tana kallon mutanen dake kanta.

Wani k'ara data k'walla sai daya gigitasu dukansu.

Ta mik'e tana neman ta ruga sukayi saurin rik'e ta,wani fizgewa da tayi Alh Ibrahim shi kad'ai ya iya rik'eta gam,aka kira likita yayi mata allurar bacci.

Idonta k'yar akan likitan har bacci ya d'auketa.

Kallon Alh Ibrahim yayi yace "tana neman rasa tunaninta fa ya kamata ana kwantar mata hankali"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ya Allah ka bamu ikon ceto rayuwar yarinyar nan"

"Ameen" haj Mariya ta fad'a cikin damuwa.

Sallama sukayi da doctor ya rubuta wasu magungunan da zata samu relief sai kuma na ciwon k'afar tata,sannan yace zaizo washe gari ya cire mata bandajin goshin nata.

         *******

"Wai meke damunka Aliyu?naga duk kabi ka shiga damuwa akan waccan banzar yarinyar"

Ajiyar zuciya yayi yace "Umma wallahi ina mamakin rasuwar mahaifin Janan"

Mtsssw taja tsaki cikin b'acin rai tace "to ko shine Alh Rabe iya abinda zakayi kenan,mutumin daya kashe maka mahaifi da mata har ka ji tausayinsa,ai yanzu lokaci ne daya kamata ace muna farin ciki"

Shi dai bai ce komai ba illa kanshi kawai daya dafe "ina son dama kazo ka nunnuna mana abubuwan da bamu Sani ba,sannan kana sane da cewar wani satin za'a d'aura aurenku da Zuhra ko?"

Baice komai ba kawai tashi yayi yana fad'in "muje na nuna muku" ta lura dashi sarai akan damuwar daya sakama kanshi amma sai ta shareshi kawai.

         *******

Janan sai da tayi sati guda tana hauka-hauka sannan Allah ya bata sauk'in abin.

Yanzu ma tana zaune kamar ko yaushe tana ta kuka ,Bilkisu na gefenta tana bata hak'uri.

Haj Mariya ce tayi sallama ta shigo "Janan kukan ne har yanzu"

Zama tayi kusa da ita ta dafa kafad'arta tace "Janan Abbanki addu'a yake buk'ata ba kuka ba,ki Sani wannan kukan da kike yi kina saka masa rad'ad'i ne"

Cikin kuka tace "ina kukan takaicine,nabi son zuciya nayi abinda mahaifina baya so Ashe ajalinsa na janyo masa,ina dana sanin k'in bin maganarsa da nayi gashi har ya rasu bai bud'i baki yace Janan na yafe miki ba,sannan su Mameey sun tafi ban san ina suka shiga ba,taya bazan yi kuka ba,ku barni inyi dan Allah"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now