Page 62-63

387 10 0
                                    

🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁

*_by SaNaz deeyah_*👄

'''Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv'''

62

Murmushi yake yana latsa waya yayinda taji zuciyarta tamkar ana tafasa ta.

"Mameey dama Mommy ce tace tana son idan zan tafi gobe in tafi da Janan" Ya fad'a lokacin daya sunkuya tamkar yana bara.

"A'a Mameey" Janan tayi maganar da sauri

"Oh k'arya nayi kenan?"

"Ni bance ba amma ka fad'a ba daidai ba"

"Ai dama kin dad'e a Kaduna ya kamata ki koma haka ga d'a kin bar mata"

"Amma munyi waya da Mommy nace sai next week zan koma"

"A'a kije gida ki shirya ku tafi goben in Allah ya kaimu tunda tana son ganin ki"

"Mameey kinga halin da Salima ke ciki fa kuma ace in tafi in barta"

"Amma ai ina nan,dan haka ki tattara ku tafi idan yaso duk abinda ake ciki zamuyi waya"

Zata sake yin magana Mameey ta katseta da fad'in "ki bi umarni na Janan"

Kamar zatayi kuka haka ta amsa wa Mameey.

Ranar kuwa Mameey ta kwana a asibiti su suka tafi gida,saida suka biya ta d'ebo kayanta a hotel tayi sign out sannan suka wuce gida.

_Washe gari_

Da shirin tafiya sukazo asibiti, sun d'an zauna kusan minti talatin sannan  sukayi sallama suka tafi.

Suna hanya ya fara k'yalk'yalewa da dariya har yana bugun sitiyari.

Hawaye cike da idonta dan ta tsani kayi mata dariya idan ranta a b'ace yake.

"Kin d'auka zakici bulus ne?har kina tunanin fara soyayya bayan ni kin hana min zaman lafiya a gida to bari kiji matuk'ar bazaki gyara tsakanin Mommy da Amal ba tabbas kema zaki rik'a had'uwa da b'acin raina"

Cikin b'acin rai ta kalleshi tace "oh akan wannan 'yar iskar yarinya kake min haka?"

Wani wawan mari ya sakar mata ya saki sitiyarin yana k'ok'arin kai hannu jikinta yaji ana salati sannan ya tuna tuk'i yake ya cigaba da yi
"Ni kike cewa matata 'yar iska to bari muje gida sai na tabbatar miki dani tantirine"

Hannunta rik'e da kumatu tace "yo na nawa ai ka tabbatar min hakan tunda babu wuya ka kai hannunka ga kuncina to wallahi indai ina raye sai Amal ta bar gidanka bazaka zauna da ita ba dan baku dace ba,Kaine giyar so ta d'auke ka har ka kasa fahimtar ita d'in wacece"

"Oh bakinki bazaiyi shiru ba ko Janan? Bazaki daina aibunta ta ba ko?"

"Bazan daina ba wallahi Jalal indai ina raye Amal dole ta rabu da kai dan bazamu yarda kana zama da k'azama kamarta ba"

"Ya wuce ke da muka zauna dake da cutarki har kike kiran wani k'azami"

Jin furucin ne yasa tayi shiru bakinta a sake tana hawaye,wai ita Jalal keda gori akan ciwon da a jikin yayansa yake.

Tana hawaye tace "wannan shine banbancinku da Adnan" ta goge hawayen idanunta "Allah yayiwa Adnan rahama shine masoyina na gaskiya dan kome nayi masa bazai tab'a wulak'antani ba"

Cikin b'acin rai yace "dama taya zamu zama d'aya bayan ba tare aka haifemu ba kuma ba sunanmu d'aya ba"

Shiru kawai tayi ta kwanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana hawaye.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 13, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now