Page 2

368 17 1
                                    

*DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_by_
*_SaNaz deeyah_*👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

02

Suna shiga falo ta zube ta fara dirzar kuka.

Da sauri mameey ta taso ta rik'eta tana tambayar abinda ya faru.

Fauziyya ce tayi mata bayanin komai.

Janyo Janan tayi tana rarrashi tare da fad'in "ki daina musawa babanki Janan, kin san shi baya da wasa kuma kaifi d'aya ne"

Ta d'ago idonta da suka gama rinewa tace "akan direba Abba zai mareni,ya zubar min mutumci a gabanshi"

"Ya isa haka kiyi hak'uri"

Ranar haka ta yini a bedroom d'inta tana kuka,ko abinci sai da aka tilasta mata sannan ta fito taci.

Bayan sallar isha'i Abba ya sa aka kirawota,nasiha yayi mata sosai akan babu kyau wulak'anta d'an Adam sannan kuma ya rarrasheta har zuciyarta tayi sanyi,fahad kuwa gaba d'aya lamarinta haushi yake bashi.

            ******

Haka ta hak'ura Ali ya cigaba da kaita makaranta amma kullum cikin zaginshi take tana nuna masa tsana k'arara.

A satin kuma aka sayowa Fauzah motarta sabuwa k'yal k'irar 'prado'.

Yau ma kamar kullum tana zaune a bayan mota tana latsa waya shi kuma yana driving a nutse.

'Dago kai tayi ta kalleshi tare da jan dogon tsaki "dalla malam kayi da jiki sai jan mota kake a k'asaice kamar ta tsohonka,Malam kar kasa na makara fa"

Da sauri yaja burki ya tsaya yana kallonta.
"Kallo na kake? To ko motar babanka ce kaifa direbana ne wall............"
Wuyanta ya shak'o Wanda ya hana ta k'arasa maganar.

"Karki k'ara ambatar mahaifina ki zaga" sakin wuyan yayi ta zaro idonta a tsorace cike da mamaki tace "ni ka shak'e?to wallahi a bakin aikinka"

"Zan miki abinda yafi shak'ewa idan har kika cigaba da zagin babana"

"Ni kam yau sai ka bar aiki a gidanmu tunda har kasan shak'a to tabbas zaka iya kisa"

"Na yarda zan bar aikin koda kuwa baki saka an koreni ba ni zan bar gidanku da kaina" ya fad'a yana goge hawaye.

Abin ya mutuk'ar bata mamaki ganin yana zubda hawaye _gaskiya yana son babanshi da yawa_ ta fad'a a zuciyarta.

Har suka je skul ba wanda ya sake yima wani magana tana son ta bashi hak'uri amma tana ganin kamar zai rainata ne.

Tana fitowa daga motar su Raihan suka k'araso,Lubna tayi saurin k'arasa jikin motar tace "sannu Aliyu ina yini"
"Lafiya lau ya karatu?" Ya amsa cikin sakin fuska.

"Karatu Alhamdulillah ya mantawa dani"

Da sauri Janan ta juya suka had'a ido tayi saurin janye k'wayar idonta daga kanshi.

"Ban manta dake ba saboda kina da matuk'ar mahimmanci a gurina"

"Nagode da wannan matsayi da ka bani"
"Nine da godiya"
"A'a ni dai Dana samu kyakykyawa handsome yayi appreciating d'ina"

"Lubna idan kin gama surutun ki samemu a hall"
Janan ta fad'a ranta a b'ace dan tana jin haushin yadda lubna ke kuranta Ali har tana fad'ar yana da kyau a gabanshi salon ya raina masu aji.

"Karku damu zan taho"
Lubna tayi maganar.

Ali kam sakin jiki yayi yana hira da lubna dan ya San Janan tana jin haushin hakan.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora