50-51

282 9 1
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
              🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄



'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''



50

Juyowa tayi sai lokacin ta kula da k'afar Mommy ninke da bandage amma dan bala'i haka ta fito da Zuhra duk da azabar da take ji.

Shigowar su Mameey ba k'aramin d'agawa Aliyu hankali yayi ba yadda ya gansu tare da 'yan sanda da alk'ali daya yanke shari'a.

Bayanin komai aka yiwa Aliyu sannan suka juya dukansu zuwa farfajiyar gidan.

Daga can tsakiya gefe ya nuna daidai rumfar da aka yi ta hutawa yace "Allah ya taimake ka nan ne inda aka sare wannan bishiya"

"Ka tabbata?"

"na tabbata yallab'ai"

Juyowa yayi ya kalli Fauziyya "karki manta idan har ba'a ga komai ba kinada shekara d'aya a prison shima sai shari'a ta hukuntashi"

"Ni kuma ina da kud'in da zan d'aukaka k'ara idan har aka sake zaluntar mu"

Duk suka juyo suka kalli Janan wanda a lokacinma hawaye take.

Ja'afar magana kawai yake son yi mata amma tsananin mamakin da take bashi ya hanashi cewa komai.

Kujera aka d'akko wa alk'alin ya zauna,yayinda duk su kuma suke tsaye.

"Janan dama zan sake ganinki a rayuwata"
Zuhra ta fad'a tare da rungumeta tana kuka.

Ja'afar ya samu k'arfin gwiwar kamo hannun Abba k'arami tare da rungumeshi.

Aliyu kallonta kawai yake ita da yaron dan ya tabbatar d'ansa ne a jinin jikinsa yake jin son yaron.

Suna tsaye aka kirawo masu hak'on rijiya dan su tona gurin.

Kusan minti talatin da fara abin Umma ta juyo ta kalli Zuhra dake tsaye a gefe "munafuka an sakeki shine kika tsaya ganin gulma" ta juya ta kalli Aliyu "ka kureta ta fice anan"

"Umma rabu da ita a gama wannan aikin tukunna"

Harara ta dallawa Janan lokacin da suka had'a ido.

Da sauri Janan ta tashi ta koma gefen Adnan ta ja kujera ta zauna.

Mommy na tare da Mameey a tsaye,Fauziyya ma suna zaune a gefe ita da mijinta da 'yarsu.

"Ba dai wannan shine babyn da kika haifo ba?" Ja'afar ya fad'a.

Murmushi tayi tace "shine,Ashe dama zamu sake had'uwa da kai d'an sanda mai basaja?"

Murmushi shima yayi yace "kece mai basaja ai,tunda kika tafi kika k'i dawowa kullum da munji sallama sai munyi tunanin kece"

"Allah sarki dan Allah kuyi min uzuri insha Allahu zanje in gaida Mammy"

"Allah yasa da gaske kike"

"Ameen"

_kenan dagaske itace Janan d'in da wannan yarinyar ta fad'a?to meye had'in Janan da wannan gida da kuma tonewar da za'ayi yanzu?tabbas zanso jin labarin chakwakiyar nan._

"Janan a ina kika san wannan kuma?"

"Shine wanda na kwana a gidansu lokacin da na taho daga Yola"

"Janan d'ita mai mutane"

Murmushi kawai tayi

Har kusan awa d'aya da wani abu  sannan aka ga akwatin,duk ya mak'ale da k'asa da k'yar suka fiddo shi.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now