28-29

283 15 1
                                    

🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁

*_by SaNaz deeyah_*👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''


28

"Karki mana haka,dan Allah ki tashi"
Momma ta fara jijjagata tana hawaye.

Nurses ne suka shigo aka d'auketa aka mayar da ita gadon sai a lokacin ta dawo hayyacinta,ta bud'e idanunta wani mugun zugi take ji a k'afarta yayinda wasu hawaye ke k'ara fita a idanunta.

"Kina son k'afarki ya rub'e?" likitan ya fad'a lokacin da yazo dai-dai kanta ya tsaya.

Ba taka kalleshi sai dai hawayen dake idanunta basu daina zuba ba.

"Indai kina so k'afarki ya warke sai kin daina taka ta,ko bakisan kin samu karaya a k'afarki ga kuma ciwo,ki daina takata ki hak'ura har ki samu lafiya"

Idanunta ta lumshe saboda yadda ta fara ganin d'akin yana juya mata.

Momma ta zauna gefen gadon ta rik'e hannun Janan tana kallon fuskarta cike da tausayi.

Mtswww Muhasin yaja tsoki sannan yaja kujera ya zauna yana kallon Janan tamkar ya daketa,yana ta addu'ar karsu had'u amma sai da ta k'ara shigowa rayuwarsu.

_Na gode ma Allah daya kasance cikine da ita da yanzu an lik'an Jaraba auren 'yar k'auye ko wahala_ yayi maganar a zuciyarsa sai kuma ya mayar da kallonsa ga Momma wadda ta k'urama Janan ido tun lokacin data zauna.

"Momma yaushe zamu tafi yolan?"

'Dago idanu tayi ta kalleshi tace "sai munga abinda Allah yayi kaga ai bama tafi mu barta a wannan halin ba"

"Momma to ta fad'i k'auyen da take sai in kira iyayen nata idan yaso sai mu basu kud'in da zai isa su cigaba da jinyarta mu mu tafi"

"Saboda rashin Adalci?"

"A'a amma naga ko muna nan ko bamu nan zata samu lafiya,kinga na bar aiki kwana biyu kenan banje office ba"

"Muhasin!zaka iya tafiya ni ka barni anan,ai nasan hanyar Yola tun kafin na haifeku to zan taho idan ta warware" Momma ta fad'a rai a b'ace.

"Ku tafi kawai" sukaji ta fad'a.
"Nagode da kawoni asibiti da kukayi ku tafi kawai ni na san tawa ta k'are" duk maganar nan da take idanunta a rufe suke.

Shiru su kayi basu ce mata komai ba,Muhasin ko kallonta baya son yi saboda takaici.

_3 days later_

An d'an jingina mata pillow a jikin gadon tana zaune ta jingina bayanta dashi,duk ka idanunta a k'asa tana goge hawayen da basu daina fitowa ba.
Muhasin yana jikin bango ya hard'e hannunsa a k'irji yana kallonta yana mamakin yadda ko gajiya batayi da kuka,shi ya tsani yaga ana rarrashin mutum yana kuma k'ara cigaba da kuka.

"Dan Allah ki bar kukan nan ki tsaya ki fad'a min meke faruwa naga tun da na tambayi iyayenki kike kuka,abinda yasa na tambayeki saboda yau muke son tafiya kuma ai bazamu barki ke d'aya ba shiyasa na tambaya saboda na san suna can hankalinsu a tashe tsawon kwana uku bakya nan,idan kuma cikin jikinki kike tsoron su sani ni zan musu bayani saboda babu wanda yake kaucewa rubutacciyar k'addararshi"

"Momma akwai sakaci fa,ni fa naga k'ok'arinki da kuka zauna asibiti jinya a tsohon kwana uku babu wata dangantaka"

"Muhasin idan ka sake magana sai na tsab'a maka"

'Daga kai Janan tayi ta sake kallonsa sannan tayi saurin kawar da kanta saboda gaba d'aya tsoronshi take,har yanzu idan ta tuno marin da yayi mata tana jin zafinsa.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now