Page 19-20

264 14 1
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁

*_by SaNaz deeyah_*👄

19

Tana ganin ya shigo ta runtse ido tana jirin me zai biyo baya.

Mari har sau biyu ya sauke mata a fuska sannan ya saka k'afa ya hankad'ata zuwa cikin d'akin sannan ya rufe k'ofar yayi mata duka tamkar ya samu jaka.

*02:30am*
Tana zaune jikin bango tana hawaye tare da soshe-soshe dan sauro ne birjik a d'akin ita kuma abinda bata saba bane,ga jikinta ciwo yake saboda dukan da tasha.

Gogan yana kwance kan katifar sai bacci yake abinsa da alama ya saba da cizon sauron ta fad'a a zuciyar.

Kallonshi kawai take tana mamakin yadda yake da mugunta haka,wai Aliyu mutumin da yake tamkar baya magana ashe gadar zare yayi mata.

Lokaci guda taji sabon zazzab'i na shirin sauka a jikinta ga masifaffan ciwon kai da take fama dashi.

Wasu hawaye na takaici ta sake gogewa tana fad'in ko me Abba yayi ma Aliyu bai kamata ya masu wannan sakayyar ba saboda farkon zuwanshi gidanmu Abba yana sonshi sosai.

Kwanciya tayi a k'asa kan tabarma inda ya umarceta da ta kwanta dan bazasu had'a makwanci ba,mayafinta ta janyo ta rufe jikinta duk da ba dad'in kwanciyar taji ba,amma a hakan bata san sanda bacci b'arawo ya sace ta ba.

*04:15am*

Kamar a mafarki yaji ana ta kyalkyala amai,yayi saurin bud'e ido ya haska tabarmarta yaga bata nan,hakan ne ya tabbatar mai da itace take amai.

Murmushi yayi ya juya kwanciyar a fili ya furta "yanzu kika fara zazzab'i dan a cikin abinda zan miki wannan somun tab'i ne sai naga kin fara aman jini sannan zan tabbatar da cewa na rama, lokacin ne zan fara murnar na cika burina"

Ganin tak'i daina aman ga dare ne gashi wata k'ila ma mak'ota na jinta.

Ya taso ransa a b'ace ya fito ya hasketa
"Oh a k'ofar d'aki kike min amai dan k'azanta?to wallahi ki tabbatar kin samu k'asa kin kwashe sannan ki saka ruwa a gurin banza k'azamar
yarinya kawai"

Bata tanka masa ba yayi ta bala'i har ya gaji ya koma ciki.

Ita ko Janan da k'yar ta samu aman ya tsaya,a daddafe ta zuba ruwa ta wanke gurin da bibbiyu take ganin komai.

Shigowa d'akin tayi ta zube masa anan tana fad'in "Aliyu bani da lafiya dan Allah ka taimakeni da ko panadol ne"

Dariya yayi a fili irin ta marasa imanin nan yace " 'yar gidan mommy da daddy ai nayi tunanin zaki ce na kaiki asibiti ko na kirawo family doctor ashe kin sakko"

"To bari kiji anan k'auyen babu inda zaki samu wani panadol ki bari gari ya waye sai kije dawa ki sassak'o ki dafa kiyi turare ko ki jik'a ki sha,wannan shine maganinmu kuma babu bawanki da zai yo miki sannan ina kara jaddada miki duk sanda kika sake d'ibar k'afa kikaje gidansu Zuhra wallahi duka ne hukuncinki dan bazaki kashe min aure ba ki hanani auren adalal mace"

Batace masa komai ba ta kwanta tana ta karkarwa idonta a rufe tana hawaye ga jikinta yayi zafi zum.

Batayi bacci ba har sai da aka kira assalatu a kunnenta,da k'yar ta iyayin alwallah tayi sallah saboda sanyin da take ji.

        ************

Ji tayi ana dukanta da k'arfi,a hankali ta bud'e ido tare da yaye mayafin.

"Ki tashi ki dama koko gashi can an siyo gasara,Ummi ta tafi siyo k'osai"

A hankali ta mik'e zaune,akwai zazzab'i a jikinta amma ba kamar da dare ba.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now