Page 12

261 9 1
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

Dis page goes 2 Hawwy Garba(Ambaby),tnx 4 d luv n support,am glad 2 hav u as bst sista,a sista 4rm another mother❤words can never express how mch i luv u...i jst mean it.....tnx u 4 everything😍😍

12

_Bayan wasu mintuna_

Tana kwance akan gadonta tana baccin wahala,rabin jikinta a kan cinyar Mameey yake haka hannunta ma Mameey ta rik'eshi gam.

Abba na zaune a gefensu yana kallonta ransa duk a b'ace shi dai Allah ya jarabceshi da 'ya mai taurin kai.

Gyaran murya yayi ya kalli Mameey yace "wace irin yarinya ce Allah ya bani wadda take da taurin kai,Janan ta san bazan aurar da ita ba yanzu to akan me zata bi ta damu kanta?sannan Sanin kanta ne bata dace da irin mazan nan ba"

Cike da mamaki Mameey take kallonsa,ya cigaba da fad'in "ko zanyiwa Janan aure ai bazan tab'a aura mata wanda baya da albashin da zai rik'e kanshi bare iyalinsa ba"

"Kamarya?me kake nufi?Janan baiwace wadda Allah yayi maka dan ka gane illar abinda kake,ka kasa gane mutum bashi yake yiwa kansa arzik'i ba,dan haka a wannan karon zan jajirce a matsayina na Uwa dan ganin na aurawa Janan zab'inta tunda bashi da wani gurb'ataccen hali"

"Wallahi baki isa ba,ni nake da ikon zab'a musu mijin daya dace dasu,kuma bazan tab'a aurawa Janan wannan yaron Aliyu ba kamar yadda ban aura mata Salman ba"

"Idan har da ranmu kuwa kaine mad'aurin auren Janan da Aliyu bata da uba daya wuce kai sannan a wannan karon dole ka barta ta Auri Aliyu dan bazaka saka rayuwar 'ya'yana ta salwanta ba gashi kana so ka sabauta min Fauziyya duk ba kaine silar komai ba" ta k'arasa maganar cikin fad'a.

"Okay ai ga fili ga mai doki kisa in aura mata Aliyu mutumin da yayi yunk'urin lalata 'yar uwarta"

"In har da ranka zaka ga aurensu kuma kaine waliyinta,sannan ka daina alak'anta yaron nan da abinda bai aikata ba dan Fauziyya ta fad'i gaskiyar komai"

Haka Abba da Mameey sukayi Baran baran, Fahad daya dawo haka yayi ta bin kowa yana bashi hak'uri amma abin yaci tura.

Haka ya hak'ura ya zubawa sarautar Allah ido,gidansu daya kasance kullum cikin nishad'i yau gashi shiru tamkar anyi rasuwa.

          ***********

Yana ta aikin yiwa d'akinsa fenti da sauran 'yan gyare-gyare,Nura da Nazifi Wanda suka kasance aminansa suna aikin zagaye b'angaren nashi da jar k'asa.

Ummi ce ta k'araso gurin tace "Yaya kazo inji umma"

Hannu ya saka ya yarfe zuffar goshinsa sannan yace "kice ina zuwa"

Tafiya tayi,shima ya d'ebi ruwa ya wanke hannunsa sannan ya k'arasa gurin umma.

"Umma gani" yana fad'a yana k'ok'arin zama

"Sannu da aiki Aliyu"
"Yawwa umma"

Shiru ta d'anyi kafin tace "Aliyu kun gama magana da yarinyar?"

"Eh umma amma jiya na kirata dan jin yadda sukayi da mahaifinta naji wayarta a kashe na san k'ila ta samu matsala ne daga shi dan dama na san hakan zata faru"

"Kana ganin babu matsala?"
"Da yardar Allah umma"
"Toh Allah ya ida nufi"
"Ameen Umma,ina son a had'a komai kafin azo biki,inason na had'a mata lefe ma"

"Lefe kuma?"
Umma ta fad'a tana masa kallon Mara hankali.

"Ina son in had'a akwati guda in kai mata,a matsayin lefe ina son mahaifinta ya fara ganin b'acin rai tun kafin bikin,zan saka k'ananun atamfa guda hud'u,man shafawa 1 makilin da brush,sai reborn biyu hijabi da mayafi d'aya sai takalmin roba da sark'a da d'ankunne d'aya d'aya shikenan fa"

"To ba damuwa Allah taimaka" ta fad'a ba dan ranta yaso ba.

         *******

Tana zaune akan gadonta idonta na kallon silin yayinda hawaye ke bin kuncinta.

Mameey ce ta turo k'ofar ta shigo cikin sallama.
A hankali ta amsa mata sallamar idonta ya koma kan Mameey.

'Karasowa kusa da ita tayi ta dafa ta "Janan bazaki bar kukan nan ba,tun jiya kike abu d'aya"

Kamo hannun Mameey tayi ta rik'e,gwiwowinta a k'asa tana kuka take fad'in "Mameey ki taimakeni ban san ya zanyi ba wallahi Mameey tausayin talaka da yanda mutane ke wulak'anta su yasa na fara son Aliyu,ban tab'a tunanin zan so shi haka da yawa ba dan Allah ki tayani da addu'a Mameey ina ganin tamkar na haukace ne"

Rungumeta tayi tana rarrashinta tare da alk'awarin yau za'a bata damar tace wa Aliyu ya turo magabatanshi.

'Dago kai tayi ta kalleta tace "Mameey taya ya?Abba bazai tab'a yarda ba"

"Abba shima ai yana da manya ko?na sanarwa su Alhaji babba kuma yanzu haka ya kira shi yace yaje yana son ganinsa a wannan karon bazan bari rayuwarki ta shiga had'ari ba"

Hannu tasa tana goge mata hawayen tana fad'in "tashi muje falo"

Ita dai jikinta a sanyaye yake haka Mameey ta kama hannunta suka fita.

Suna zaune Mameey ta kunna tv suna kallo saboda ya d'ebe mata kewa ta saki jikinta.

_2hrs later_

Janan na kitchen tana had'a musu fruit salad taji k'arar motocin su Abba da alama ya dawo.

'Kirjinta sai buguwa yake dauriyace ta saka kawai ta cigaba da abinda take.

Kamar daga sama taji muryar Abba yana fad'in "ina Janan d'in".

Da sauri ta ajje wuk'ar hannunta ta koma falon a tsorace.

"Kin zab'i d'a namiji akan ni mahaifinki ko?kin zab'i aure akan karatunki ko?to ga Aliyu nan zan aura miki shi"

"A'a dakata Alh karka mata baki mana,idan har baka sanya alkhairi ba to kaja bakinka kayi shiru"

"Kin kaini k'ara gurin Alhaji babba kin sa ammin dole akan abinda banyi niyya ba to wallahi duk sai kun fuskanci hukunci daga gurina"

Da sauri ya haye sama shida guards nashi guda biyu.

Hawaye ne ya fara sauka daga fuskar Janan,ta kalli Mameey tace "Mameey kawai na hak'ura"

"A'a Janan ki k'yaleshi zai sakko"

Suna nan zaune a falon ya fito,da sauri Janan ta sauke kanta k'asa dan wani mugun tsoro ne ya ziyarceta.

Zama yayi kan kujerar dake gefenta,tayi saurin sulalewa k'asa ta zauna.

"Ki ce masa ya turo iyayenshi gobe,ke kuma ki shirya wani satin zan d'aura aurenki dashi kuma zaki bar min gida a ranar da aka d'aura aurenki,sannan na janye hannuna daga komai naki mijinki ne keda iko dake idan yaga dama ki cigaba da karatu idan baiga dama ba kanki,idan yaga dama ku zauna a daji ma ba gidan k'asa ba wannan ba damuwa ta bace abu d'aya zan sake nanata miki duk abinda ya biyo baya karki nemeni matuk'ar bazaki canza ra'ayi ba"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi hawaye gaba d'aya ya wanke fuskarta.
Kafin tayi magana taji Mameey tayi saurin fad'in "sai kuma aka yi sa'a mamanta 'yar kasuwa ce kuma tana da arzik'i dai-dai gwargwado dan haka zan basu gidana dana gama ginawa su zauna,dama nayi shine ina son in bawa Fahad shi kyauta amma na barwa mijin Janan halak malak,ni dai fatana ka d'aura aurensu amma bance ka bada komai ba zan zamto Uwa da uba a gareta zan share mata hawayenta kuma duk abinda ya taso zan mata shi"

"Da kin kyauta" ya fad'a tare da tashi ya koma sama.

Janan ta matso ta rungume Mameey ta cigaba da kuka.

"Karki damu ki share hawayenki ki kira Aliyun ki fad'a masa ya turo iyayenshi gobe sannan ni zan bashi jari ya fara Sana'a mai kyau wacce zata rik'eku kuma zan bashi takardun gidan yayi signing na bashi ku zauna ku rayu a ciki,ko babu komai Aliyu ya ceci rayuwar fauziyya dan da yanzu ta shiga gurb'atacciyar rayuwa"

"Mameey Allah ya biyaki da gidan aljanna" ta fad'a tana goge hawaye.




_Sadeey S Adam_✍

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now