Page 56-57

296 10 1
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah👄*_

'''Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv'''

_Makaranta littafin NAGA RAYUWA dan Allah kuyi min afuwa zakuji shiru babu posting, so akwai dalilin dayasa zan dan tsaya da posting dan haka ayi min afuwa._

56

        ***********

"Mommy taya zan samu visa a yau nazo Egypt" ya fad'a cikin kuka shima

'Kara manna wayar tayi a kunnenta muryarta a dashe tace "haba Jalal muma ai ba zama zamuyi ba,nan da kwana d'aya ko biyu zamu taho da gawarshi anan za'ayi masa sutura,ka dai sanar da 'yan uwa da abokan arzik'i"

"Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un yanzu shikenan na rasa shi dagaske Adnan baya numfashi"

Katse wayar tayi dan karya k'ara karya mata zuciya,a lokacin kuma Janan ta farka daga dogon summan da tayi.

"Wayyo Allah na shiga uku meyasa Adnan zai mutu a lokacin da nake buk'atar mu rayu tare,ina zansa rayuwata ya zanyi"

Runtse ido kawai Mommy tayi dan ita kanta tana jin mutuwar Adnan sosai.

Da sauri Janan ta tashi zata fita Mommy ta rik'ota "ina zaki Janan?"

"Mommy zanje gurin Adnan wallahi ban gaskata ba"

"Wanda ya mutu bazai tab'a dawowa ba,Janan kiyi masa addu'a"

'Dora hannu tayi aka ta k'walla k'ara,Mommy ta rik'eta sosai lokacin ta k'ara birkicewa tana fizgewa.

Ranar haka ta zama tamkar mahaukaciya,har susucewa ta rik'ayi kuka sosai take kamar zata amayar da zuciyarta.

Ranar kuwa Mommy tayi receiving calls da messages da yawa anata mata ta'aziyya.

'Yan gidansu kuwa da suka kira Mommy bata fad'a musu halin da Janan ke ciki ba.

Jalal kuwa duk bayan awa sai ya sake kiran Mommy dan har yanzu bai gaskata rasuwar Adnan ba.

        ***********

"Momma wallahi ji nake kamar nayiwa Janan kuka,yarinyar nan taga jarrabar rayuwa"

"Wallahi Yaya nima tausayi take bani,gashi a sanadin matsalolin rayuwar nan har idanunta fa sun juye,tabo na har abada" Zainab ta fad'a itama tana kallon Muhasin.

"Mijinta na farko shiya fara ruguza rayuwarta"

"Inji wa?" Sai lokacin Momma tayi magana.

"Momma hakane ai dan shine........"
"Ya isa haka kema har dake Humaira,ku k'addara kawai wannan itace k'addararta Allah ya kub'utar da ita da shiga wata matsalar shi kuma Allah yajik'ansa"

"Ameen" duk suka amsa.

"Yaushe zamuje Abuja?"

"Sai sun dawo Jalal yace zai kiramu"

"Allah sarki Adnan Allah ya masa rahama" Muhasin ya fad'a,duk suka amsa da Ameen.

       ***********

Yawo yake kawai a tsakiyar d'akinsa idanunsa gaba d'aya sunyi jajir.

Saif dake zaune gefen gado ya taso tare da dafa kafad'arsa.
"Jalal kayi addu'a mana"

Kallon shi yayi da idanunsa da suka gama komawa jajaye yace "ina yi amma na san bazaka tab'a fahimtar irin tarin damuwar dake damuna har na rasa wane tunanin zanyi,wallahi Saif har yanzu na kasa gaskata cewa Adnan ya mutu gani nake kamar mafarkin nake wanda har yanzu ban farka ba"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now