44-45

324 11 0
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄


'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''



44

Kai tsaye d'akin Adnan ta nufa.

Tana tura k'ofar ta tarar dashi zaune akan sofa ya d'ora hab'arsa akan gwiwarsa.
Idanunsa akan plazma dake manne jikin bango amma a zahiri ba kallon yake ba.

Shigowarta yasa shi juyo kai ya kalleta.

Wasu zafafan hawaye ne suka sauka a fuskarta ta kalleshi tace "Adnan alk'awarin Iya dan Allah ka zamo mai halacci da adalci"

"Wannan ne iya adalcin da zan miki Janan,wannan shine zai nuna wa duniya cewa ina son ki kuma bana fatan cutar dake daga ke har Jalal,wallahi da kinsan irin son da Jalal yake miki da baki nuna masa k'iyayya ba"

Cikin kuka tace "kenan kai baka sona Adnan?"

"Ina son ki mana amma Jalal shi yafi cancanta da ke"

"Oh kenan idan da babu ciwo bazaka Aure ni ba saboda Jalal?duk irin son dana nuna maka?"

"Da babu ciwo a jikina babu abinda zai hanani aurenki Janan"

"Shikenan zan wa tufk'ar hanci yanzu"

Kafin yayi magana ta kai razor nan ta yankin hannunsa.

Yaji azabar zafi,amma a fusace ya rik'o hannunta dan karta aikata abinda take shirin aikatawa,aikuwa ta bank'are hannun cikin zafin nama ta yanke razor a cikinta.

Wanin azababben k'ara ta k'walla hakan bai hanashi d'aga hannu ya wanketa da mari ba.

Hawaye gaba d'aya ya wanke mata fuska hannunta rik'e da kuncinta wani jiri-jiri take ji.

Shima hannun nasa ya rik'e yana hawaye ya kasa tab'uka komai.
"Kin cuci rayuwarki Janan" ya fad'a a can k'asan mak'oshinsa.

A haka Jalal da Mommy suka shigo.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Mommy ta fad'a tare rik'o Janan d'in da take k'ok'arin sumewa,jini gaba d'aya ya wanke mata gaban rigarta.

Jalal ya tsaya cak ya kasa motsawa wasu hawaye ne kawai ke fita daga idanunsa.

Mommy ta juyo a rikice tace Jalal muje asibiti.

Jikinsa a sanyaye ya juya zai fita tayi saurin cewa "Jalal bazan iya d'aukanta ba"

A sanyaye ya juyo ya d'auketa a sume kamar gawa ya fita.

Mommy ta kalli Adnan tace "tashi mu tafi ga yadda jini ke zuba a hannunka"

'Dago ido yayi ya kalleta yana hawaye yace "Mommy zan wanke da spirit ku kaita kawai"

"Haba Adnan idan kai baka san ciwon kanka ba ni na sani"

"Mommy kunyar had'a ido da Jalal nake"

"Adnan ka bar maganar nan ka tashi muje kawai,wai baka san ciwon kanka bane"

Jikinta a sanyaye ya  bita.

Har zata shiga baya Jalal yayi saurin cewa "Mommy dan Allah kiyi driving wallahi bani da wani k'arfin da zan iya yi"

Tausayinsa sosai taji ta karb'i key d'in maigadi ya bud'e gate d'in aikuwa a guje taja motar.

_*Asibiti*_

Suna zaune a office d'in likitan yana sake musu bayani.

Jalal kanshi a k'asa yake ya dafe goshinsa da hannu.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now