Page 11

239 12 1
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁

*_by SaNaz deeyah_*👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

11

Batayi bacci da wuri ba hakan ne yasa ta makara sosai,dan sai kusan k'arfe 6:30am ta farka,ko sallar asuba batayi ba,da sauri ta fad'a bathroom ta d'ora alwallah ta fito ta gabatar da farilla.

Komawa ciki tayi tayi wanka ta fito ta fara shirin fita.

'Karfe tara ta fito k'aramin falo dan gabatar da break fast,sanye take cikin wani Swiss material  yellow da touch d'in red a jiki,ta yana d'an k'aramin veil(million stones), fuskarta d'auke makeup yauma ta saka fashion glass d'inta brown color,tayi kyau ainun.

Bata tarar da kowa a dinning area ba dan haka ita kad'ai ta zauna tayi breakfast sannan ta tashi ta nufi d'akin Mameey.

Da sallama ta shiga ta gaidata sannan tayi mata sallama,harta juya zata tafi Mameey tace "waye zai kaiki?"

"Baita! na fad'a masa tun jiya"
"Okay ki kula"
"Insha Allahu"

       *******

Suna zaune a plantation suna hira bayan sun fito daga lecture,Raihan ta kalleta tace "naga kina yawan duba time lafiya"

"Eh lafiya lau ina dubawa ne saboda Aliyu yace k'arfe sha biyu zaizo"

"Amma Janan me zai miki?"

Dariya tayi tana sake duba agogon hannunta tace "yanzu har an tambayi dalilin zuwan saurayi gurin budurwarsa"

"A'a amma ai inajin kinsan zamu shiga lecture na cost Accounting ko?kuma 12 d'inne sannan kinsan halin Mr Eze"

"Ki min attendance bazan samu damar shiga ba"

"Lallai yarinyar nan kin shirya rungumar  carryover kenan"

Kallonta tayi ta yatsina fuska tace "kawai dan banyi attending lecture guda 1 ba sai in samu carryover?"

"To naga kina neman yin wasa da karatunki Janan"

"Kinga Raihan ki rik'e wannan jawabin idan na dawo kin d'ora daga inda kika tsaya Aliyu ya kirani" da sauri ta tashi ta bar gurin.

"Ohni Raihan ya Allah ka magancewa Janan wannan mahaukaciyar soyayyar".

Janan kuwa tana barin gurin ta d'aga kiran " hello kana ina?"
"Inda kika ce mu had'u"
"Okay gani nan"

Cike da zumud'i ta nufi side d'in can wajen Faculty of engineering dan nan ne babu mutane sosai.

Tunda ta hangoshi take murmushi shi kuma gaba d'aya idanuwansa a kanta yana ta shiryo irin muguntar da zai shirya mata.

"Barka da zuwa"

"Yawwa sarauniya" ya fad'a yana murmushi.

Zama tayi kan kujerar dake facing d'insa ta kalleshi tace "kamar kana cikin damuwa"

"Eh damuwa mara misaltuwa kuwa"

"Subhanallah meya faru?"

"Gani nake kamar zan rasa ki Janan,kuma rasa ki tamkar rasa rayuwata ne" ya k'arasa maganar kamar zaiyi hawaye.

"Ka daina fad'ar haka Aliyu"

"Dole ne na fad'a saboda muna cikin had'ari sosai,muna da banbanci dake sosai gashi umma ta sakoni a gaba"

"Bamu da wani banbanci saboda dukkanmu mutane ne kuma munzo daga Adamu da hauwa'u"

"Janan kenan! Meyasa kike b'oye abubuwan da suka zama gaskiya,na tabbatar ba Wanda yake son tarayya ta dake har k'awayenki taya ya zamu samu damar zama abu d'aya"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now