Page 8

286 9 1
                                    

    *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

_ohhni Safnah shiru babu ita babu labarinta,pls dan Allah ina cigiyar Safeenah writer d'in *Sunyi Sake* dan kaf numbers d'inta switched off Allah yasa dai lafiya Ameen🙏_

Kuyi haƙuri da late post da aka samu bana jindadi shiyasa

08

Tana zaune a d'aki tana ta kuka dan ta rasa mafita shikenan a karo na biyu ta rasa masoyi,ta san Abba bazai tab'a yarda ya bata shi ba tunda har haka ta faru kuma dama soyayyar a b'oye suke yinta dan ta san babu yadda za'ayi Abba ya aura mata direbanta cikin sauk'i.

Tana cikin yanayin nan taji muryar Abba yana fad'in "Arrest him" a tsawace.

Da sauri ta tashi ta fita falo,idanunta suka sauka akan Aliyu yana fad'in "Abba Ku tsaya ku fahimceni wallahi ita ta nemeni"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Janan ta fad'a tana kuka,da sauri ta k'arasa gabanshi "meyasa ta bugo waya tana neman taimako? kuma kace ita ta nemeka"

Kallonta yayi idonshi jajir yace "wallahi bani na nemeta ta ba ita tace na rakata hotel zata kaiwa wata mata kaya kuma tace bazata iya shiga ita kad........"
Abba ya wankeshi da mari "Rufamin baki" 

Janan ta juyo ta kalli Abba tace "bai aikata ba Abba"

"Janan baki da hankali ne?"

"Mameey da hankali na ku duba ku gani,akwai kissar wani malami da yake cewa duk macen da tace an mata fyad'e a duba a gani da takalmi ta shiga d'akin ko kuma babu,idan da takalminta ta shiga to tabbas ita ta kai kanta idan kuwa  babu takalmi to da k'arfi aka jata,sannan kuma tayaya Aliyu ya kai Yaya Fauzah hotel?idan ta k'arfi yayi mata babu yadda za'ayi su shiga saboda ma'aikatan ciki ai ba mahaukata bane,sannan meyasa tabi Aliyu bayan tana da motarta Aliyu baya da kud'in kama d'aki a katafaren hotel kamar Najman sannan rigar Yaya Fauzah ta gaba ta yage bata baya ba kinga kuwa duk zancenta k'arya ne koda ace Aliyu yana nemanta to tabbas ta amince ta kuma yarda sannan ita ta kama musu d'aki a wannan hotel"

"Abba k'arya take wallahi" Fauziyya ta fad'a tana kuka.

"Ki rufa min baki munafuka" fahad ya fad'a yana huci
"Abba tabbas akwai duba a maganar Janan"
"Kin cuceni Fauziyya ban yi miki wannan tarbiyyar ba" Mameey ta fad'a tana kuka

Abba da kanshi ya fara dukan Aliyu sannan ya bada umarni akaishi cell har sai ya nemeshi a kuma bashi abinci sau d'aya a rana sannan kar a yarda da belin.

"Abba"
"yi min shiru Janan".

Aliyu ya Ciro key daga aljihunsa ya mik'awa fahad "ga key d'in motarku"

Juyowa yayi ya kallesu d'aya bayan d'aya a lokacin ya k'ara k'udirar cewar sai ya shayar dasu ruwan bak'in ciki Wanda basu tab'a tsammani ba.

Suna fita dashi janan ta durk'ushe tana kuka.

"Na dawo kanki Fauziyya" a gigice ta d'ago kai ta kalleshi
"Ni kike neman zubda wa daraja da k'ima ko?"

Kai ta girgiza tana kuka "wallahi k'arya yake Abba,shine yace idan banje ba zai kasheni yaje ya wurga gawata inda baza'a tab'a gani na ba shiyasa na yarda na bishi" rufamin baki manufuka.

Fahad ya kalla yace "ka kulle min Fauziyya a d'aki kar ka yarda ko falo ta fito duk abinda take buk'ata a kai mata d'akin a k'wace system d'inta da wayarta har sai na gama bincike a Kansu"

Mameey dai kallonsu kawai take tana hawaye dan ta san duk abinda ya faru da 'ya'yanta laifin mahaifinsu ne.

        *********

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now