42-43

306 9 0
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄


'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''


_*Wannan shafin sadaukarwace ga duk wani masoyin littafin nan*_😘😍
_#TARENE#🤝❤_

42

Adnan rud'ewa yayi ya kasa cewa komai  dan yana ganin yanayin fuskar Jalal ya san tabbas yaji komai.

Dariya Jalal yayi wadda iyakarta leb'e sannan yace "kuyi hak'uri na muku katsaladan na shigo kuna magana na katse ku"

Yayi saurin wuce wa side d'insa duk suka bishi da ido.

Janan ta goge hawayen idanunta ta kalli Adnan tace "Jalal yana da damar da zai zab'i macen da duk yake so amma kai baka da dama, hakan ne yasa zan jajirce dan ganin na samo maka farin cikin rayuwa,ina son na ganka da d'anka na kanka Salman"

"Me?ke! Janan ko dai kin fara samun matsalar kwakwalwa?"

"Koma me zaka ce kace amma ka sani ba zan auri Jalal ba kai nake so Allah ya sani ban tab'a son wani kamarka ba"

"Karki saka raina ya b'aci a kanki bana son samun matsala dake Janan na san Mommy tana ta shirye-shiryen aurenku da Jalal,ki duba irin d'awainiyar da yayi miki amma kawai rana d'aya kice baki son shi"

"Bana son Jalal kai nake so idan har naga ana shirin aura min wani ba kai ba to tabbas zan bar muku gida"

"Ba sai kin bari ba Janan"
Kawai suka jiyo muryarsa.

'Daga ido tayi tana kallonsa Adnan kuma ya juya gareshi.

"Jalal ka fahimceni dan Allah karka saka zargi a zuciyarka" Adnan yayi maganar.

Murmushin karfin hali ya sake yi sannan yace "babu zargi a ciki sai gaskiya,idan har kaine Salman d'in da ake fad'i kuma itace wadda kaje kayi soyayya da ita a Kaduna to tabbas tana matuk'ar k'aunarka dan Raihan ta bani labari,bros kai take so bani ba dan haka zata auri zab'in zuciyarta ba zab'in wata zuciyar ba"

"Bata da wani zab'i da ya wuce kai Jalal" Adnan ya fad'a yana kallonsa.

Tun kafin Jalal d'in yayi magana tayi saurin cewa "ni ban tab'a cewa ina son Jalal ba kai nake so kawai kana guduna ne saboda bani da gata"

"To kaji ta fad'a da bakinta,bata sona kai take so nine nake son ta,nayi kuskuren sonta da nayi,dan Allah bros ka nuna mata ita d'in mai gata ce,ka aureta kawai"

"Abinda ba zai yuwu ba"

Kukanta ne ya fara fitowa fili dan haka tayi saurin to she baki da hannu ta wuce d'akinta da gudu.

Shima Jalal hawayen idon nashi ya goge yace "Adnan kaine zab'in zuciyarta"

"Ka daina fad'ar haka Yarima dan Allah, wai taya zan auri lafiyayyar mace bayan ina da ciwo"

"Tace zata sakawa kanta idan har baka saka mata ba ina tausayin Janan bana so ta cutu ka daure bros"

"Na san fad'a take kawai ka daina wannan furucin Jalal"

Hmmm "na san halin Janan wallahi zata iya aikatawa,karka damu na san yadda zan sanarwa Mommy"

"Karka kuskura ka fad'awa Mommy zancen nan,bazai yuwu in auri Janan ba"

"Saboda me bayan da kunnena naji kace kaima kana sonta,kana k'inta a yanzu saboda kawai ina sonta,to ni na bar maka bros"

"Yarima......."
"Dan Allah ka bar maganar nan Adnan"

Da sauri Jalal d'in ya wuce ya bar Adnan a tsaye shi kad'ai.

Kan kujera ya zube dan ji yayi k'afafunsa ba zasu d'aukeshi ba ga azabebben ciwon kan daya fara ji.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now