Page 25

262 14 0
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
        🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

*_Wagga shafi naki ne kyauta Mom Haidar😍,ki daure ki karanta banso ki tafi strike shiyasa nasa dole Aliyu ya rangad'awa Janan saki uku🤪_*

25

*inna lillahi wa inna ilaihi raji'un* shine abinda ko wannensu ke fad'a.

Wata harara Umma ta zabga musu tare da fad'in "munafukan banza kawai salatin me kuke?"

Nura ne ya kalleta yace "meya faru da ita haka Umma?"

"Kai baka ga abinda tayi ba,da namiji ta dawo gidan nan fa"

Sum-Sum ya fice ya bar gidan dan yaga ran Umma ya b'aci sosai.

Asabe da Yabi suka durk'usa gabanta har lokacin kuka take a fili yanda take jin azabar ciwon na sake shigarta.

Ummi ba shiri ta shiga d'aki, tunda take bata tab'a tausayin Janan kamar yau ba.

" 'Dagata mu tafi da ita gidanmu sai dai kome Haidar zaiyi yayi"

"A'a mu kaita chemist" Asabe tayi maganar.

"Ina mukaga wani chemist a k'auyen nan muje kawai gidan Malam Ayuba ya bata magani"

Haka kuwa sukayi suka d'agata tana kuka ta kasa ajje ko k'afar,har a lokacin jini zuba yake a k'afarta haka suka isa har gidan malamin.

Sai daya shafa mata man alayyadi a k'afar sannan yayi mata addu'oi kuma ya bata maganin da zata rik'a shafawa a gurin.

Suna fitowa daga gidan malamin cikin kuka tace "dan Allah ku kaini gidanmu"

"Ai bamu san gidanku ba Janan" Asabe tayi maganar.

Cikin kuka tace "zan nuna muku dan Allah ku muje bakin titi mu samu abin hawa"
*
Tun a k'ofar gate d'in su Yabi suka rik'a mamakin yadda Janan ta auri Aliyu bayan ta fito daga wannan tafkeken gida.

A babban falo babu kowa dan haka tace suje k'aramin falon.

Suna shiga suka tarar da Mameey da Fauziyya ne kad'ai a zaune a falon.

Da gudu fauziyya ta k'araso ta rungumeta suka fara sabon kuka.

Mameey tashi tayi ta k'araso gabanta ta rik'eta tana kallon k'afarta da har ta kumbura tayi jajir.

Gaisawa sukayi da su Asabe sannan tace su zauna.

Janan na zaune kusa da Mameey tana kuka tana fad'a mata irin azabar da ake gana mata a gidan Aliyu.

Duk kansu kuka suke hatta Asabe sai da ta koka,'yan aiki suka kawo masu ruwa da lemo.

A lokacin Fauziyya take kuka tana fad'a mata irin shari'ar da ake gudanarwa sannan Abba yace kar a fad'awa kowa har ita.

Kuka sosai Janan take gani take k'ila laifi tayiwa Allah yake jarabtarta da hakan amma wannan tsanar da Abba yayi mata tayi yawa.

Kallon Mameey tayi taga itama hawaye take,da sauri ta saka hannu tana goge mata "Mameey kiyi hak'uri karki k'ara tsinka min zuciya dan Allah" ta fad'a tana hawaye.

"Meya kawo Janan gidana?" Suka ji muryar Abba.

Da sauri Janan ta mik'e tsaye sai kuma ta zauna saboda zafin k'afarta tama manta da ciwon.

"Bance bana son ganinki tare damu ba,na yanke alak'armu dake na sallamaki a matsayin 'yata dan haka ki bar gidan nan yanzu-yanzu"

"Yallab'ai baka da lafiya fa amma har ka jiyo muryar Janan ka fito"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now