Page 13

235 12 1
                                    

      DIREBAN GIDANMU
        🍁🍁🍁

by SaNaz deeyah_👄

*_wannan shafin nakune kyauta Ummi,Asma'ul husna,Aunty Ramlat,Rabi'atu Adam,Zulaihat.......godia da soyayyarku ga ni da novels d'ina gaba d'aya ina yinku sosai_*

Baku comments ba voting shiyasa nima bani posting da wuri

13

****
Cike da murna yazo ya sanarwa da Umma yadda sukayi da Janan.

Farin ciki ya rufe ta sosai har da goge k'wallah,lallai ta yarda Allah maji k'an bawa ne.

"Kaje k'auyen ka sanarwa su baffa idi da baffa mu'azu sai su shirya suje gobe a had'a harda sadakinta"

"To Umma"
"Yanzu zakaje fa kar lokaci ya k'ure naga kamar kana shirin fita wani wajen"

"Eh dama zanje gidan su Zuhra ance baffanta yana nemana,so daga can sai in wuce k'auyen su baba idin"

"A'a bana son ayi sanya ka dai fara zuwa k'auyen tunda su Malam Zakar muna tare idan ka dawo sai kaje"

"To umma"

Haka kuwa aka yi sai da yaje k'auyen ya sanar musu komai sannan ya bada dubu 11 a matsayin sadakinta dan baya da ko sisi.

Yana dawowa ya sauka a gidansu Zuhra,yaci sa'a kuwa Malam d'in yana zaure da samari biyu yana musu d'orin karatu.

Ya gaidashi ya samu gefe ya zauna,Malam ya bawa samarin umarnin su d'an bashi guri ya gana da shi Aliyun,tashi sukayi cikin girmamawa suka yiwa Malam sallama suka fita.

"Aliyu bismillah"
Tashi yayi ya dawo kusa da Malam.

"To dama magana ce nake ji jite-jite cewar wai zakayi aure cikin watan nan shine nakeson jin gaskiyar lamarin"

"Hakane Malam amma............"
"Ya isa haka" Malam ya tari numfashin sa tare da fad'in "karkace komai ai shi aure nufi ne na ubangiji fatana dai Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen Malam" ya fad'a jikinshi a sanyaye.

"Kajeka ba komai zan sake nemanka"

Babu k'warin gwiwa ya koma gida,Umma da ta ga yanayinsa ta tsorata sosai tunaninta ko wata matsalarce,sai  daya bata labari sannan hankalinta ya kwanta ta kuma tausasashi akan indai tana raye sai ya auri Zuhra.

Da dare haka ya shirya ya nufi gidan su Zuhran, koda ya aika tazo ma bata sauya a yadda ya saba ganinta ba da kuma yadda suka saba hirarsu hakan yasa hankalinshi ya kwanta sosai.

            *********

Tana kwance a kan gado tana ta juyi tunani babu wanda batayi ba,Raihan ce ta turo k'ofar ta shigo.

"Cab lallai yarinyar nan a kwance kike ma"

"Raihan"

"Dalla ki tashi meya hanaki shiga skul?wlh test zamuyi k'arfe 2 kinsan yanzu ma muka gama lecture barrister Sanusi yace mu yago paper mu rubuta test,na samu na miki amma kinsan ta statistics dole kizo kiyi dan kin fini iya calculation"

"Raihan anya kuwa zan iya nutsuwa inyi?"

"Saboda me?"
"Saboda ina cikin cakwakiya,ko kinsan wani satin bikina"

Mtsww "dalla malama bana son wasa"

"Wallahi dagaske nake"
Labarin yadda sukayi da Abba da Mameey ta fad'a mata sannan ta k'ara da cewa"a tsorace nake Raihan,gani na nake tamkar mahaukaciya,saboda Aliyu na rufe idona na kasa janyewa Abba fushi yake dani"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now