Page 10

263 11 5
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

10

Bayan sunyi sallar isha'i sun ci abinci Abba ya buk'aci ganinsu a babban falon gidan.

Janan ta k'udiri niyyar zata fad'a masa cewar ya saki Aliyu dan bashi da laifi koda zai kasheta zata tsaya da k'afafunta dan k'watar masa hak'k'insa.

Su hud'u ne a falo, Abba, Mameey, Fahad, Janan duk kansu sunyi shiru, Abba ne ya fara magana da fad'in "zan saka a saki yaron nan sannan na sallameshi bazai sake aiki a gidana ba, ita kuma Fauziyya zan mata horo mai tsanani dan sai tayi wata bata fita ko ina ba, idan ta fara samun carryover zata nutsu tasan mahaifinta cikakken d'an sanda ne kuma baya da wasa"

Janan ji tayi kamar an sakata a aljanna, cikin sauk'i za'a saki Aliyu,hamdala tayi a zuciyarta ko babu komai ta san umma bazata hanata Aliyu  ba.

Fahad kuwa yaji dad'in hukuncin Abba dan bai tab'a tunanin Fauziyya zata iya abinda tayi ba.

Mameey kuwa jikinta duk yayi la'asar, a haka tattaunawarsu ta k'are.

_Washe gari_

Kamar yadda Abba ya fad'a haka ya cika alk'awarinsa dama shi kam da wuya ya fad'i magana ya k'i aikatawa, sai dai baima yarda Aliyu yazo gidan ba daga can station yace ya tafi sannan baya son ya k'ara ganinsa a gidanshi, haka ya dawo masu da labarin ya sallami Aliyu kuma babban hukuncin da yayi masa shine rashin biyansa albashinsa na wannan watan.

Janan bata ji dad'i ba amma babu yadda ta iya da mahaifinta, ita dai dad'inta d'aya an sake shi.

A b'angaren Aliyu kuwa napep ya tara ya kaishi har k'ofar gidansu.

Yana yin sallama kuwa duk kansu suka tashi suka nufo shi, dama duk suna tsakar gida suna wanki.

"Aliyu haka ka canza?meyasa mutanen nan basu da imani?"

"Umma ai wannan ba bak'on abu bane a gurinmu kin san halinsu ai"

"Allah ya saka mana, Ummi maza d'ora masa ruwa yayi wanka"

"To umma".

Bayan yayi wanka yasha maganin ciwon jiki ya huta sannan umma ta bashi labarin zuwan Janan, haka ummi ma ta bashi labarin irin cin mutuncin da aka musu kafin su samu damar shiga gidan.

"Janan zan fara azabtarwa Umma, sai na gasa mata aya a hannunta, nafi tsanarta ita da mahaifinta domin ita ta fara nuna min tsana, kuma ta zagi mahaifina"

"Bana so ka tausayawa duk wani zuri'ar Alhaji Hashim, ina son duk runtsi ka samu damar da za'a d'aura aurenku da yarinyar nan a wata d'aya"

"Duk yadda kika ce haka za'ayi umma wannan damar ce zata bani damar auren zuhra ba tare dana sha wahala ba, Janan kuwa bayan na gama k'ask'antar da ita sannan inyi mata sakin wulak'anci"

"Tabbas bazamu raga musu ba yaya domin sunyi mana babbar illa".

          ********

_Bayan kwana 4_

Janan ce ta tura k'ofar cikin sallama ta shiga.

Hankalinsa na kan takardun da yake dubawa ko bayan amsa sallamarta da yayi kawai ya cigaba da duba abinda yake.

Kan sofa ta nufa ta zauna tare da fad'in " magana nazo muyi yaya"

"Indai akan wannan mara mutuncin ce karma ki soma"

"Yaya hannunka baya tab'a rub'ewa kace zaka yanke"

Kallonta yayi tare da fad'in "idan har hannun bai isheka da azaba ba, amma idan yana azabtar dakai ai tuni zaka yanke ka wantsar dashi"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now