Page 5

220 13 1
                                    

🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
          🍁🍁🍁

05

A bangaren Fauziyya kuwa tunda ta fita ta sauya tafiya,sai wani irin taunar chewing gum take irin na tacaccun 'yan bariki.
Shi kanshi Ali yayi mamakin yanda take behaving a lokacin tamkar sabuwar kilaki.

Yayi sauri zai bud'e mata k'ofar baya ta dakatar dashi.
"Ban saka ka ba" ta furta tare da bud'e gaba ta zauna.

Shima zagayawa yayi ya zauna ba tare da yace komai ba.

Sun fara tafiya ne ya tambayeta ina zasu
"Park" ta bashi amsa
"Wanne"
"Duk wanda ya maka"
Maganar yaji ta wani iri dan haka kawai ya k'udiri niyyar zai ta tafiya koda zasu bar garin in har bata ce su tsaya ba.

Yanayin abubuwan da take yi ne yasa shi b'aro jirginta amma sai ya nuna baima damu ba.

Tana gani suna ta tafiya amma bata yi yink'urin tsayar dashi ba,daga tayi mik'a sai ta zame mayafinta daga jikinta kai duk wani abu da tasan zai ja ra'ayinsa haka ta rik'a yi har ya gaji yayi parking "naga mun tsaya?"
"Ina son ki fad'a min inda zan kaiki" ya furta ba tare daya kalleta ba.

Shiru tayi tsayin Rabin minti sannan tayi dariya tace "kayi kyau wallahi ka had'u"

Kallo ya bita dashi na _ban fahimci me kike nufi ba_
'Daga gira d'aya tayi ta sake fad'in "kayi min Aliyu tun ranar da aka kawoka gidanmu nake sonka"

"So kuma?" Ya fad'a a d'an razane.
"Eh so,kasan me?"
"Sai kin fad'a" kawai ya tsinci kanshi a mai bata amsa kai tsaye"
"Ina so muyi wani sirri amma ba yanzu ba ka bani number ka zan nemeka dan maganar bada rana zamuyi ta ba"

_ko dai Janan ta fad'a mata komai?_ ya tambayi zuciyarshi ba tare da ta bashi amsa ba.

"Yah kayi shiru" ta katse tunaninsa

"Yaushe zamuyi maganar?"

"Ka bani number ka sai na kiraka idan na saka time"

Babu musu ya bata numbershi,tayi masa umarni da su koma gida kawai.

          *******

Tana kwance akan gado tana juyi tunani kala-kala take a cikin zuciyarta...

_ki kalli kanki a mirrow zaki tabbatar da cewa ke d'in kyakkyawa ce ajin farko_

Maganar Salman ta fad'o mata lokacin daya fara furta mata kalmar so.

Da sauri ta tashi ta nufi jikin mirrow ta kalli fuskarta,wani murmushi ta saki na jindad'i sai take ganin kamar a lokacin ne yake fad'a mata.

_zan tafi bazan sake dawowa garinku ba dan bazan iya jurar ganinki a matsayin matar wani bani ba,k'addara ta raba mu dake,amma nasan bazan tab'a samun kamarki ba har k'arshen rayuwata_

Zubewa tayi a k'asa lokacin da ta tuno maganarsu ta k'arshe da Salman,tun a wannan lokacin bata sake jin labarinsa ba sai labarin rasuwarsa da Abbanta ya kawo mata.

"Allah yaji k'anka Salman ya yafe maka laifukanka" ta fad'a tana zubda hawaye,a dai-dai lokacin Mameey ta shigo.

"Oh dama kin shirya shine kika zauna direba na can na jiranki kin kirashi kusan awa d'aya ko kin fasa zuwa skul d'in?"

Bata bata amsa ba kawai ta cigaba da goge hawayenta.
"Janan"
"Na'am" ta amsa a sanyaye.
"Kukan me kike?"
Nan ma shiru tayi.

Kusa da ita ta k'arasa ta tallabo hab'arta
"Nace kukan me kike?"
"Bakomai"
"Oh dama anayin kukan dad'i?"
Tayi shiru
"Tambayarki nake"
"Mameey Salman na tuna"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,Janan meyesa bakya jin maganar iyayenki?wace nasihace mahaifinki baya miki ita akan Salman?idan kin tuno shi meyasa bazaki masa addu'a ba"

"Ina yi masa"
"To ba kuka yake so ba addu'arki yake buk'ata oyaa tashi ki saka gyalenki ki tafi skul"

Jikinta a sanyaye ta tashi ta zura hijab ta d'auki handbag d'inta.

Tana fita ta hango Aliyu tsaye jikin motar shi kam tun daya ga fitowarta yake murmushi.

Wani zugi taji kanta nayi ganin fuskar Aliyu take tamkar ta Salman.
A take ta zube a gurin a sume.

"Subhanallah" wasu daga cikin securities d'in gidan suka furta.

Da sauri d'aya daga cikinsu ya nufi cikin gidan dan sanarwa dasu mameey.

Aliyu ma a rud'e yazo gabanta ya tsaya a dai dai lokacin da mameey da Abba suka fito a tare.

"Me aka mata ne?"
"Fad'uwa kawai tayi bamu San dalili ba" Ali ya bashi amsa.

A kafad'a Abba ya sab'eta sukayi cikin gida.

_2hrs ago_

Fad'a sosai Abba yake yi ita kam tana jingine da fuskar gado tana kuka.

Fauzah da Fahad suna tsaye yayinda Mameey ke zaune gefen gadon.

Ganin Abba yak'i daina fad'an sai maimaita Abu d'aya yake yasa mameey cewa "fad'an nan fa bashi zai saka ta nutsu ba"

"Kamar ya kenan? Duk ba laifin ki bane,ina amfanin yarinya k'arama kamar Janan ace namiji ya shiga ranta haka,ki gaya min dalilin dayasa ta fara soyayya da Salman ba tare da iznina ba???"

"Me kake nufi da hakan?kana nufin kace Janan bata isa aure ba ko kuma bata isa soyayya bane?"

"She's just 18 me ta sani game da wannan?"

"Ko ka so ko karka so gaba d'aya yaranka sun isa aure"

"Ni kuma bazan tab'a aurar da 'ya'yana ba ba tare da sun gama karatu ba"

"Shi kuma Fahad da yake aiki fa?meyasa ka hanashi ya fito da yarinyar da yake so ka aurar dashi ba?"

"Hadiza mu bar wannan maganar na san lokacin daya dace ko wanne na aurar dashi"

"Nima ina da right d'in bawa 'ya'yana zab'i"

"Oh haka kika ce?"

"K'warai ma kuwa"

"Mu zuba mu gani"
Ya fad'a a fusace sannan ya fita ya bar d'akin,mameey tabi k'ofar da kallo ranta a b'ace.

Ranar haka kowa ya yini a gidan da b'acin rai.







_Sadeey_💫✍

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu