Page 4

288 14 4
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

04

"Meye abin b'oye shi ai idan kana son abu kana nuna shi ga kowa ne"

Ran janan a b'ace tace "lubna meyasa kike min irin wannan?"

Murmushi tayi sannan tace "oh sorry na zo zan takura miki ko?ina ji ina gani kina neman yi min k'wacen Aliyu ai ba k'arya nayi ba kina sonshi"

A hargitse ta shak'o wuyanta tace "ina son shi sai me?"

"Sakarmin wuya ko in tara miki jama'a"

Ganin duk mutane sun tsaya suna kallonsu ya sa ta sake ta tare da fad'in "ba haramun bane soyayya dashi?to zanyi soyayya dashi kuma zan aure shi"

Tsaki taja tayi saurin wucewa ta bar gurin saboda kar tayi kuka gashi mutane sun fara ihu da hayaniya.

Saida ta tsaya a gurin da babu mutane sosai sannan tasha kukanta ta k'oshi sannan ta goge hawayenta ta nufi department d'insu.

Ranar bata yiwa kowa magana ba har suka kammala lectures, Raihan tayi-tayi ta fad'a mata abinda ke damunta amma tak'i fad'a,itama lubna bata yi mata magana ba bare su kaure da fad'a.

Babu wanda tayi wa magana a cikinsu haka ta kama hanya ta tafi.
A bakin main gate ta tsaya ta kirashi bai dad'e ba sai gashi yazo.

Kamar yadda ya saba haka ya fito da da sauri ya bud'e mata k'ofar baya.

Kallonshi kawai tayi  ta matsa ta bud'e murfin seat d'in gaba ta shiga ta zauna.

Yafi minti 1 a tsaye bai shigo ba ita kuma tayi banza ta k'yaleshi dan tasan mamaki yake.

Sai daya gama tsayuwarsa sannan ya shigo ya zauna.

"Dan Allah kiyi hak'uri ki koma baya"

Kallon tsiwa tayi masa tace "daga yanzu nan zan rik'a zama"

Hannunsa ya d'ora kan sitiyari ya saki ajiyar zuciya yace "nan ba hurumin ki bane,baki dace da nan ba,karki manta ni direbanki............."

"Shhhhhh" tayi saurin katse shi,tare da yin wannin sassanyan murmushi "Kai ba direba na bane,saboda ina son duniya ta sani ina sonka kuma zan aureka,kaga sai aji dad'in kaini gidan radio ace na auri direba na,ina son dan Allah ka amince dani bazan tab'a cutarka ba"

Cire key d'in motar yayi tare da mik'a mata.
"Me kake nufi da hakan?"
"Ina nufin ki karb'a ki ja motar zan wuce gida dan naga abinda kike buk'ata kenan"

"Kamar ya?Aliyu karka bani kunya pls"

"Dakata Janan,kada ki maida ni k'aramin yaro kada kiga dan ina direbanki ki nemi wulak'antani,dan Allah ki fita ki koma baya,bazan iya soyayya dake ba dan bakya tsarin matan da nake so"

Bata san lokacin da hawaye ya fara zuba a idonta ba.

"Aliyu tunda nake a rayuwata ban tab'a cewa ina son wani d'a namiji ba,hasalima idan akace ana sona bana amincewa so d'aya na tab'a soyayya kuma ta wahalar dani banyi tunanin zan sake ba amma hakan har ya zama laifi kana kallon tsabar idona kana wulak'anta ni"

"Ko zaki sake bada Aliyu ba,bana sonki kuma bazanyi soyayya dake ba ki daina ma wannan maganar ina ke ina direba,kin manta irin maganganun da kike fad'a a kaina ne"

"Wallahi baka isa ba ko kana so ko baka so dole kayi soyayya dani,gwanda ma kaso"

Da sauri ta bud'e murfin motar ta fita ta koma seat d'in baya ta kwanta tana  hawaye.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now