40-41

267 9 0
                                    

🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄


'''Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv'''



40

Yau misalin k'arfe hud'u da rabi Mommy na zaune a falo ita da 'ya'yan nata da Raihan duk kansu sun mayar da hankalinsu akan wani program da ake gabatarwa a Arewa24, Janan ce ta shigo tana sab'e da Abba k'arami a kafad'arta.

Dukkansu su ukun hankalinsu ya koma kanta.

'Karasowa tayi gaban Mommy ta durk'usa tace "Asabe tace kina kirana"

"Eh dama coconut juice nake son a had'a mana,kin iya?"

"Eh na iya"

"Yawwa kije kitchen na ajje komai a fridge, kawo Abba na rik'e miki shi"

Murmushi tayi tace "nagode" sannan ta mik'a mata ta tashi.

Har ta d'anyi taku kamar biyar sai Mommy tayi saurin cewa "Yawwa Janan ki d'anyi da yawa saboda ku"

Tun kafin ta kai k'arshe Janan d'in ta tsaya cak tamkar wacce aka zarewa laka.

Jalal,Adnan da Raihan kuwa sunyi mugun d'imaucewa.

Mommy ta mik'e tsaye tana fad'in "ya naga kin kasa tafiya kina mamaki sunanki na gaskiya daya fito daga bakina?"

Jalal yayi saurin mik'ewa tsaye zaiyi magana mommy ta d'aga masa hannu "dakata Yarima ka zauna karka fad'i dan naga ka tsorata "

Adnan ne yayi saurin cewa "Mommy abin ne ya bamu mamaki kin kirata da sunan da ba nata ba,ita fa sunanta Aysha indo"

"Gaskiyane Adnan, saboda kai ka haifeni bani na haifeka ba dole ka nemi yi min wayo"

Kallon Jalal tayi wanda har lokacin ya kasa zama tace "ka saki jikinka Jalal yau dai ga Janan d'in da kake ta yi min k'arya da ita,kun d'auka duk abinda kuke bana lura,ni dama tun da tazo jikina ya bani,dan naso in gane muryarta amma na manta ina na san muryar"

Ta kalli bayan Janan wanda har lokacin ta kasa motsa ko d'an yatsan ta,murmushi tayi sannan ta taka har gaban Janan d'in ta kalleta taga yadda hawaye ya wanke mata fuska sai kawai itama taji hawayen.

"Meyasa kika bari rayuwarki ta koma haka bayan da gatanki?"

Shiru babu magana sai shashshek'ar kukanta "Janan kin san bazan tab'a cutar dake ba ko?kuma tun lokacin da Jalal ya kira muka gaisa naji kin shiga raina,bazan tab'a cutarki ba Janan meyasa kika min haka?yanzu ba dan wata k'awarki Lubna ba da haka rayuwarki zata k'are Janan"

"Lubna" Jalal ya fad'a cike da mamaki.

Mommy ta kalleshi tace "eh tun da kai ka zama mace kana da rauni,ka kasa fad'awa mahaifiyarka gaskiya to ita Lubnar da ta damu da damuwar Janan ai ta kira ta kuma sanar da ni komai"

Raihan sai a lokacin ta mik'e dan ta tsorata sosai da maganar Mommy.

Hannun Janan d'in Mommy taja sannan Janan ta motsa.

Janta tayi har cikin d'akinta ta zaunar da ita gefen gado.

Sai lokacin Abba k'arami ya fara kuka yana mik'a hannu alamar ta d'aukeshi.

Kallonshi kawai take dan jikin nata babu wani k'warin da zata iya karb'arsa.

Mommy ta mik'a mata shi tace "ki bashi yasha k'ila yunwa yakeji"

Karb'arshi tayi kawai ta rungume sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani.

Jalal,Adnan,Raihan da sauri suka shigo d'akin.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Kde žijí příběhy. Začni objevovat