Page 23

273 13 0
                                    

🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''


23

Daddy suka gani tsaye jikin k'ofa ransa a b'ace tamkar bai tab'ayin fara'a ba.

"Meya kawo ta gidannan?"

"Daddy Janan ce fa"

"Tun kafin kiyi wayo na san Janan dan haka ki tattara ta ta bar min gida yanzun nan sannan na datse alak'arki da ita kamar yadda na datse tawa data mahaifinta dan bazamu zauna da azzalumai ba"

"Daddy kayi hak'uri dan Allah,Abba yace ta bar masa gida kaima in ka koreta ina zataje?"

"Gidan uwaki" ya cilla mata dak'uwa ransa a b'ace ya cigaba da fad'in "ubanta ya koreta sai nine zan rik'e ta?tun kafin raina ya gama b'aci ki nuna mata hanya ta fita ta bar min gida"

Hawaye sharkaf a idon Janan haka ta tashi jikinta sai rawa yake ta rab'a ta jikin k'ofar ta wuce,da sauri Lubna ta saka mayafi zata bita daddy ya tsawatar mata yace ta zauna.

A falo Janan ta tarar da Umman Lubna a tsaye.
Kafad'arta ta dafa tace "Janan kiyi hak'uri kinji ki d'auki k'addara a duk yadda tazo miki Allah ya shige miki gaba"

Da k'yar ta iya cewa "ameen" ta wuce kawai.

Cikin kuka Lubna ke fad'in "Daddy tun tasowa ta nake tare da Janan baka tab'a rabamu ba sai yau rana d'aya zaka rabani da ita,daddy na san dani ce a halin da Janan ke ciki wallahi bazata tab'a min haka ba"

"Ki rufamin baki kafin in miki duka a gidan nan,ni bazaki fi k'arfina ba wallahi ni ba sakaran uba bane sakarai kawai" Jan k'ofar yayi ya fita ita kuma ta cigaba da kuka.

Napep ta tara ta shiga ya kaita har k'ofar gidan Aliyu,bata ga kowa a k'ofar gidan ba hakan ne ya bata damar fad'awa gidan Asabe.

A hankali tayi sallama dan kar su Umma su jita.
"Ah ah Amarya ce a gidan namu shigo bismilla"

Duk da tasha kuka ta k'oshi amma hakan bai hanata b'oye damuwarta ba wajen k'irk'iro murmushi,d'akin suka shiga bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa.

Cikin jindad'i tace "nagode" Jakarta ta bud'e ta fiddo dubu biyu ta mik'a mata.

Karb'a tayi tana fad'in "me za'ayi dasu?"

"Kyauta ce na baki"

Baki bud'e Asabe tace "Jaka goma fa?ina zan kaisu? a'a wallahi sunyi yawa Amarya"

"Kin cancanci fiye da haka,wallahi naso ace ma siyayya na miki amma ban samu damar haka ba,kinga tun da aka kawoni nake ajje da dubu hud'u banyi komai dasu ba sai yau ne ma na kashe  500 nayi kud'in mota ki ajje kyayi wani abu dasu karki damu"

"To nagode Allah ya Saka da alkhairi,amma idan babu damuwa zan tambayeki dan Allah"

"Karki damu indai na san amsa zan fad'a miki"

"Kowa ya ganki ya san ke 'Yar manya ce dan Allah shin auren soyayya kukayi da Aliyu?"

"Tabbas auren soyayya mukayi"

Shiru tayi kafin tace "amma idan haka ne meyasa yake dukanki koda yaushe?sannan kowa a k'auyen nan yana son Aliyu tun sanda yazo garin nan saboda kirki,hak'uri da kawaici irin nasa amma akwai wata magana da naji d'azu wadda ta d'aure min kai"

Murmushi Janan tayi tace "karki damu bara na shiga gida dan ina dawowa nan nayo" tayi haka ne dan ta kawar da maganar.

Tashi tayi da sauri ta fito,Asabe ta biyota tana sake mata godiya.
            ***
Kwance ta ganshi kan katifa yana Waya,kallon daya bita dashi ne yasa tasha jinin jikinta.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now