32-33

233 10 0
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv'''

_*Ummi kina burgeni,d way yadda  kike magana akan novel d'in nan na kanyi dariya ko ina cikin fushi😃Ummin Aliyu🤣tnx 4 d support*_

32

A dai dai kangon ta tsaya ta kalli ciki taga babu alamar datti.

Shiga tayi ta lek'a ko ina taga babu alamar 'yan shaye shaye na zuwa gurin.

'Dankwalinta ta cire ta zauna wasu hawayen na zuba a kuncinta.

_Ashe ma 70k d'in da nake tattali har ita sai da akaje banki aka karb'e,Allah ka saka min bazan tab'a yafe wannan zaluncin ba._

_Washe gari_

Bata farka ba sai da taji rana a tsakiyar kanta da yake kangon ba rufi.

Tashi tayi tana murza ido bacci har yanzu bai isheta ba ga uwar yunwa da takeji.

'Dan kwalinta ta d'ora sannan ta fito waje,unguwar tamkar babu mutane.

Zaninta ta kunce ta fiddo 2k d'in data rage mata ta fara tunanin me zata saya kafin wani lokacin.

Gari da suga ta tuno dan suna sha a gidan Aliyu duk da dole ce tasa take sha har yanzu bata saba ba.

Haka tayi ta tafiya a k'asa da k'yar ta samu wani guri ta sayi kofin roba da plate da cokali da buta da dai d'an tsince tsincen da zata buk'ata sai ta sayi gari rabin kwano da suga kwata.

Bayan ta dawo ta tsaya a wata borehole tayi pumping na ruwa a jerrycan(keg) ta tafi dashi.

Ta fara shan garin kawai taji anyi sallama a kangon
Gabanta yayi mummunar fad'uwa da k'yar ta iya amsa sallamar.

Farar dattijuwa ce,gashin girarta ma fari sol ne,fatarta duk ta yak'une saboda tsufa.

Kallonta Janan take har lokacin data samu guri ta zauna.

"Sannu baba"

"Yawwa 'yata sannu,ke kuwa meya kawoki kika zo kika zauna a kangonnan ga tsohon ciki?"

Murmushi tayi mai d'auke da hawaye tace "karki damu Iya nan ma ina jindad'in zama tunda a rufe yake"

"Ina rufuwa bayan sama a bud'e yake ga damuna tana shirin zuwa"

"Karki damu Iya"

"Yarinya ke kuwa meyasa kikayi cikin shege da k'uruciyarki?"

Jin haka ne yasa tayi saurin mik'ewa tsaye ta kalli tsohuwar tace "idan cin mutumci ya kawoki nan ki gaggauta fita,to waima ina ruwanki dani da har kike kiran cikina shege instead of ki tambayi ina mijina,bana son kowa ya sake shigo min rayuwa ki fita ki bani guri"

Tsohuwar ta tashi tana zare ido tana fad'in "ni kike fad'awa haka yarinya?"

"Na fad'a d'in idan har bakija girmanki ba tabbas zanbi ta kanshi in take"

"Shikenan kije zaki gani"

Cikin tsiwa Janan tace "Alkhairi zan gani insha Allahu"

Tsohuwar na fita ta zube ta fara kuka tana fad'in "ka cuceni Aliyu Allah kayi min sakayya".

Haka rayuwarta ta cigaba da tafiya a wannan kango take kwana,tun abinci baya gagararta har yazo yanayi.

Sai ta kwana ta yini bata ci ba,wani lokacin sai dai ta shiga daji ta ciro ganye taci saboda yunwa.

Ta zama k'azamar k'arfi da yaji dan a sati sau d'aya take wanka shima sai dare take d'ora hijabin jikinta tayi sannan idan da hali ta wanke kayanta kafin asuba sun bushe sai ta saka.

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang