Page 14

239 10 1
                                    

🍁🍁🍁
      *DIREBAN GIDANMU*
       🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄

_Ayshat A Muh'd wannan shafinki ne ke da masoyanki❣ ki d'au rabi ki raba musu sauran😊,Allah ya bar zumuncin dake tsakaninmu Ameen🙏_



14

Sai data gama kukanta har ta gaji sannan ta duba agogonta taga k'arfe 3:45pm,da sauri ta mik'e tsaye tana goge guntun hawayenta ga yunwa ga shi ko azzahar batayi ba.

Kallon k'ofofin falon tayi daban-daban ga wani k'aton dinning area a gefe sai bene side biyu.

_to waye babanshi da har zai mallaki wannan kud'in?shin waye shi?duk yadda akai shi d'an gidan shugaban k'asa ne,to amma ai na san 'ya'yan shugaban k'asa,to d'an waye???_
Gabanta ya yanke ya fad'i lokacin da wata zuciyar ke ce mata _masu garkuwa da mutane ne_

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un wayyo Mameey Ku cece ni" wani sabon kuka ta rushe dashi lokaci guda ta nufi k'ofar da zuciyarta ta raya mata.

Tana turawa taga wani falon ne amma bai kai wancan girma ba,kallon falon kawai take tana jinjina irin dukiyar da aka kashe wajen k'awata shi,wasu k'ofofin ta sake gani kai tsaye ta nufi wadda take facing d'inta.

Tana tura k'ofar ta tsaya cak zuciyarta cike da tsoro.

Yadda taga k'ayatuwar d'akin ko bedroom d'in Mameey daya fi ko wanne kyau a gidansu bai kaishi ba,baza ta iya fasalta kyawun d'akin ba.

A hankali take tafiya tana k'ara kallon d'akin k'ofofi biyu ta sake gani a ciki wanda ta tabbatar d'aya daga ciki toilet ne.

Tana tura ta side d'in dama taga d'an k'aramin d'akina ga  qur'ani guda uku a mazauninsu,sai sallaya guda d'aya mai matuk'ar kyau a shinfid'e kan lafiyayyan carpet daga gefe kuma d'an k'aramin fridge ne.

Janyo k'ofar tayi ta rufe sannan ta nufi ta left hand side d'inta,tana turawa taga toilet ne makeke shi Kansa abin kallo ya zame mata duk da tana cikin tashin hankali.

Alwallah tayi ta nufi wancan d'akin da taga sallaya ta shiga tayi sallah sannan ta janyo Qur'an ta fara karantawa tana kuka,can ta duba agogon hannunta taga k'arfe biyar har da minti sha tara "na shiga uku,na san su Mameey suna ta nemana,me bawan Allah nan yake nufi dani?ko dai da gaske kawoni yayi ya yanka kamar yadda zuciyata ke fad'a"

Tashi tayi ta koma falon ta zauna,idonta ya k'ank'ance fuskarta tayi jajir saboda kuka.

Har ta gaji da kukan ta daina kawai ta zubawa sarautar Allah ido.

Ganin duhu ya d'an farayi ta k'ara tsorata ta tashi tana d'an zagaye ga yunwa na neman halaka ta,kamar daga sama taga haske ya bayyana a gidan,nepa ce ko generator oho!.

'Dakin ta koma tayi sallar Magrib ta duba fridge d'in babu komai a ciki sai ruwa.

"Wayyo Mameey zan mutu" ta fad'a tare da sulalewa k'asa ta lumshe idonta kawai tana jiran Allah yayi ikonsa a kanta,gani tayi d'akin harya fara juya mata rabonda taci abinci tun jiya da rana.

         *********

Mameey na zaune akan kujera tana kad'a k'afa.

Kallon Fahad tayi tace "wai har yanzu bata d'auki wayar ba?"

"Ai a kashe ma wayar take tun d'azu"

"Wannan wane irin shashanci ne ta san zamu nemeta saboda yau akayi za'a zo ayi magana,gashi mutanen har suka tafi babu ita,ina Aliyu ya tafi?"

"Ya hak'ura ya tafi shima tun d'azu"

"Janan bata da kirki"

"Mameey ki barni da ita wlh sai na b'ata mata,gidan wa zataje ta kai dare haka gashi har magriba tayi"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now