Page 16

234 9 1
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄


16

Kulle d'akin tayi da key tasha kukanta ta k'oshi,sannan ta tashi ta nufi toilet tayi alwallah,har zata tada sallah ta tuna wayarta a kashe take,tayi saurin kunnawa da niyyar tana idarwa ta kirawo Aliyu.

Tana tada sallah kuwa wayar ta fara ringing, kafin ta idar an mata missed calls ya kai goma.

Bayan tayi addu'oi ta duba wayar taga duk missed calls d'in Aliyu ne,da sauri ta kirashi,har ta kusa katsewa sannan ya d'aga.

"Assalamu alaikum,Allah ya huci zuciyarka"

Ajiyar zuciya yayi sannan ya amsa sallamar yace "nayi tunanin ko laifi nayi"

"Bakayi laifi ba ni ce nayi maka laifi ina neman afuwa"

"Karki damu ai bakyayin laifi a gurina na yafewa matata" wani dad'ine ya mamaye zuciyarta sai taji har ta manta da abinda Fahad ya mata suka sha waya sosai har  yake sanar mata ranar asabar za'a kawo lefe kuma yana son ta rubuta I.v zai shigo skul gobe ya karb'a.

"A'a Aliyu karka damu Mameey ta d'auki nauyin komai"

"A'a abin yayi yawa,d'azu da mukazo ta bani mukullin gidan da zamu zauna can tudun wada yake,sannan ta karb'i account numberta tace zata turomin kud'in da zanyi business d'in da zan rik'e ki,Janan Mameey na sonki sosai kuma Mameey tayi min gata da ban san da kalamin da zan gode mata ba"

Wasu hawayene suka sauka a idonta  najin dad'i.
"Karka damu Aliyu ai yiwa kaine"

Haka suka gama hirarsu sukayi sallama cikin kewarshi ta kashe waya.

Labarin da Jalal ya bata ne ya dawo mata a rai.

Ta zauna ta zuba uban tagumi tana tunanin dama akwai azzaluman mata haka a duniya,tausayi ne ya rufeta gaskiya akwai babbar sakayya a lahira.

          ********

*12:30pm*

Kamar a mafarki taji ana ta knocking k'ofarta.

A hankali ta bud'e ido ta kalli agogo,hamma tayi tare da salati sannan ta sakko a hankali zuwa bakin k'ofar.

"Waye"
"Ni ce"
Jin muryar ne ya saka tayi saurin bud'e k'ofar ta kalleta.

Rungume juna suke cike da murna sai kuma fauziyya ta fara kuka.

Zama sukayi suna ta maganganu akan matsalar gidan nasu, anan Janan ta fad'a mata maganar aurensu da Aliyu.

Tayi mata murna sosai dan ji take dama itace dan matsalolin gidan ta fara gajiya dasu.

A haka suka tsara komai na game da shirin bikin.

"Zan fita skul karfe 2 fa"

"Ki shirya na rakaki saboda na dade ban fita ba,daga can sai mu wuce muyi shopping ko?"

"Okay ba damuwa bara na shiga wanka"

"Nima bara na shirya ko"

"Okay"

          **********

Fauziyya taji dad'in yadda taga Janan na mayar da hankali sosai a karatun ta,yadda take yawan  amsa tambaya a lecture hall.

Bayan sun fito Raihan tace "Janan mu zagaya da Yaya Fauzah taga skul d'in"

"To" ta amsa

"Ke ni baki bani labarin yarima ba naje har gida jiya fa baki dawo ba"

Hmmmm "ke dai bari kawai"

"Ban labarin yadda kukayi dashi jiya?"

Ganin bayan shi tayi daga can nesa a zaune kan kujera.
Jikinta kawai ya bata cewar shine.

Da sauri ta k'arasa ta barsu Fauzah da Raihan anan.

Tana isa taga shine kuwa "jalal"
Da sauri ya d'ago kai da alama yana cike da damuwa a lokacin.

"Ah ah Janan kin shigo kenan"

"Eh ya kake?"

"Lafiya lau"

Sai a lokacin su Fauzah suka k'araso cike da mamaki Raihan ke kallon Janan bakinta d'auke da tambayoyi da yawa,Fauzah na kallonsa a tsorace tace "Salman dama kana raye?"

"Salman kuma" Janan ta fad'a tana kallon Fauzah

"To waye?"

"Sunanshi Jalal"

"Wallahi yana kama da Salman sosai nayi tunanin shine ma"

Kallonshi Janan tayi sosai sai a lokacin taga yayi mata kama da Salman sai dai shi Salman ruwan tarwad'a ne (chocolate color) Jalal kuwa fari ne sol.

Hawaye ne suka sauka a idonta shima cikin mamaki yake fad'in "Waye Salman?"

Da gudu ta juya ta bar gurin,Fauzah nata kiranta amma tak'i ko juyowa,Raihan haka ta bita kamar mahaukaciya da taga gudun Janan ba mai k'arewa bane sai kawai ta dawo a rikice.

"Dan Allah mu bita a mota nifa ina ganin Janan ta fita a hayyacinta"

"Wlh banzo da motana ba kawomu akayi"

"Muje a mota na" Yarima ya fad'a cikin sauri suka wuce.

Parking space na gurin suka k'arasa da shida Fauziyya suka shiga gaba Raihan na baya.

A bakin main gate da suka tambayi securities d'in da wanda ke gurin akace an ganta ta hau napep a gigice anyi tunanin ma ko wani abu ya faru da ita.

"Mu tafi gidan" Fauzah ta fad'a a kid'ime.

Baita ta kalla tace "Janan ta dawo kuwa?"

"Eh"

"Okay a bud'e gate ina masu gadin?"da kanta ta danna horn suka bud'e ya shiga da gudu.

Fauzah da Raihan suka shiga ciki suna rige rige.

A Babban falo suka tarar da ita a kwance tamkar gawa,idonta a bud'e amma hawaye na zuba ta gefe,ba ta ko motsa idon dan ta tsayar dashi cak a kan cilin kanta na bisa cinyar Mameey.

"meya sameta ne?a waje ta fad'i sai zuwa aka yi aka shigo ta ita"

Fauzah ta zauna kusa da Mameey ta dafa Janan tace "Mameey daga naga wani mai kamar Salman shikenan ta rikice kuma already ta sanshi fa dan ita taje gurinshi"

Da sauri Janan ta tashi zaune idonta sharkaf da hawaye tace "wallahi shine, Salman d'ina ne"

"Janan kin haukace ne ko kin tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo?" Mameey ta fad'a tana jijjiga ta.

"Mameey wannan fa sunanshi yarima" Raihan ta fad'a

"Waye shi?"

"A skul d'inmu yake tare muka zo dashi nan gidan ma yana waje"

"Wallahi Salman d'ina ne Allah ya dawo min dashi"

Da sauri take k'ok'arin fita,Mameey ta rik'eta.




*kuyi hak'uri masoyana wallahi kwana biyu ne na zama busy babu time d'in typing.Da masoya littafin _A dalilin so_ duk kuyi hak'uri,ku dai yi manage da wannan.*







_Sadeey S Adam_✍

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now