38-39

275 11 0
                                    

🍁🍁🍁
       *DIREBAN GIDANMU*
         🍁🍁🍁

*_by SaNaz deeyah_*👄



'''Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv'''

_Wannan shafin na sadaukar dashi ga beebah luv_✍

38

"Janan naga alama kina neman ruguza aurena to wallahi baki isa ba,zan miki warning ne, a 'yar aiki zaki zo to a ita nake son kizo bani son ko da wasa ki nuna wa Mommy kece Janan bare har ta ji tausayinki,dan babu yadda zanyi ne da wallahi baza kije gidana ba to amma da kije gidan da yace zai siya miki gwara kije gidana don kar ayi min sakiyar da ba ruwa"

Kallonta tayi tana murmushin takaici tana girgiza kai tace "bana mamaki maganganunki a kaina saboda na san ba ko wane d'an adam ya san halacci ba,bana tantama idan lubna ce bazata min haka ba" ta k'arashe maganar tana hawaye

"Karki fad'a min magana Janan dan wallahi yanzu zan wulak'anta ki,lubnar da tuni ta mance da tarihin rayuwarki k'ila ma bazata ganeki ba idan ta ganki kucaka haka"

Za tayi magana aka turo k'ofar duk suka mai da hankalinsu gurin.

Adnan ne ya shigo ya zauna yana fad'in "mun amso takardar sallama ki shirya nan da 5minutes zamu tafi"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa amma babu yadda zatayi haka ta d'auki tsumman Abba k'arami ta goyashi ta zauna gefen gadon ta rafka uban tagumi lokacin duk sun fita.

Sai bayan mintuna 20 sannan ya dawo  yace ta fito su tafi.

Hawaye zafafa suka sauka a kuncinta a fili ta furta "Abba ka yafe min na kasa cika burinka akan lokaci amma nayi alk'awari zan tara kudi in shiga k'asar nijar ko rayuwa ta zata k'are a can sai nayi abin da ya kaini"

Kallonta ya tsaya yi tana ta goge hawaye wani na sake zuba.

Yana so ya rarrasheta amma bazai iya ba baya so ta gane shine,bai san tuni ta gane ba.

A mota ta tarar da Jalal da Raihan,ran Jalal d'in a had'e yake idanunsa a lumshe,sai da ta shiga motar sannan ya juyo ya kalleta sai kuma ya d'auke kai.

Adnan ne yayi driving amma fa zuciyarshi a cunsheta take tunanin janan ya rufe ko wane b'angare na zuciyarshi,kusan sau uku yana neman karawa mota Allah ne ya kaisu lafiya amma da sai sun koma asibiti jinya koma wani ya rasa nashi ran.

Duk tsawon tafiyar nan da sukayi babu wanda yawa wani magana sai karatu kawai da Adnan yasa a motar.

A Kaduna ma da suka tsaya cin abinci Janan k'in fitowa tayi daga motar haka da Jalal yayo mata takeaway tak'i ci.

Karb'ar Abba k'arami yayi ya rik'a bashi fresh milk har yasha ya k'oshi sannan ya mik'a mata.
Hakan ba k'aramin zafi yayi wa Raihan ba,ta kuma k'udurta sai tayi abinda zai sa Janan ta gudu daga gidan da k'afarta.

Sai gaf da magriba suka isa gida.

Mommy ji tayi tamkar ta had'iye 'ya'yan nata saboda farin ciki,tana son ganin 'ya'yan nata a tare da ita.

Sai bayan sunyi sallar isha'i sannan suka had'u a babban falo.

"Adnan wacece wannan kuma?"

Ya d'an gyara murya sannan yace "Mommy 'yar aiki muka sama miki"

" 'yar aiki kuma?a wane dalili?" Mommy ta tambaya tana kallon Janan.

"Mommy tana cikin wahala ne shiyasa muka ga ya dace mu taimaka mata gashi kema kina neman taimako kuma aiki yama Asabe yawa"

"Saboda aiki yama Asabe yawa shiyasa ka d'akko min 'yar aiki mai d'anyan goyo?akan wane dalili?to bana so saboda nida Asabe muna yin komai"

Gaban Jalal ba k'aramin fad'uwa yayi ba,ya kalli Mommy zaiyi magana tayi saurin cewa "karka ce komai Jalal ku mayar da ita inda kuka d'akkota"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now