Page 15

245 9 0
                                    

🍁🍁🍁
     *DIREBAN GIDANMU*
      🍁🍁🍁

_*by SaNaz deeyah*_👄

'''Safnah luv'''





15

Kallonta shima yake yana shafa fuska yace "ya naga jikinki na shaking tun kafin na fad'a miki"

Bata ce komai ba idonta yana gefe amma tsoronta k'ara dad'uwa yake.

"Idan na kaiki gida zaki gabatar dani gabansu mom da dad d'inki na gaidasu?"

A tsorace ta kalleshi,idonta duk ya firfito,ta marairaice tace "zan kaika gobe amma yanzu dare yayi za'a min fad'a"

"Okay ba damuwa kin dai yi alk'awari ko?"

Kai ta d'aga alamar eh
"Yawwa muje"

A mota suna tafiya ko wanne yayi shiru,ita tana tunanin k'aryar da zata yiwa su Mameey shi kuma yana tunanin yadda zasu k'arke da Mom.

"Kin san me?" Muryarsa ta daki dodon kunnenta,a tsorace tace "a'a" dan a matuk'ar tsorace take dashi.

"Zan fad'a miki dalilin daya saka na yiwa mahaifiyata k'arya dake dan karkiyi tunanin ko sonki nake u are not my type dan babu auren siririyar mace haka kamar ke,sirantarki tayi yawa tausayi ma kike bani dan ba zama ki iya zaman aure ba,zakiyi ragonta da yawa bazaki tab'a jurar ayyukan da matan aure ke sha ba"

"Na yiwa Mom k'aryane saboda hankalinta ya kwanta,dan tun lokacin da dad ya rasu take damunmu akan muyi aure amma aure baya gabanmu ma,kin san dalili?"

Bata bashi amsa ba,bama ta kallonshi,ya san tana jinshi murmushi yayi a zuciyarshi yace _kina da aji sosai_ a fili kuwa ya cigaba da fad'in
"Mu biyu ne a gurin iyayenmu duk kanmu maza ne, yayana Adnan sai ni yarima Jalal,na samo sunan yarima daga gurin kakana wato mahaifin Mom wanda ya kasance shine sarkin bauchi"

"Shine ya fara kirana da sunan kasancewata ina da k'asaita da isa da nuna izza tun ina k'arami,hakan ne yasa wasu mutanen suke kirana da saraki yayinda kakana Sarki Abdurrahman ke kirana da yarima"

"A lokacin zan iya cewa rabin rayuwata a bauchi nake yayinda iyayena suke zaune a Abuja,na samu tsangwama wajen 'ya'yan sarki dan gani suke duk cikin jikokinshi yafi sona,dan ko yana fada ina gefensa"

"Hakan ne yaja cece kace har abin yana son tab'a zumuncinmu dan haka Daddy yace a dawo dani Abuja kawai"

"Babana shine minista na kud'i a birnin tarayya ta Abuja C.B.N,muna da arzik'i sosai kuma mun samu gata fiya da tunaninki"

"Ni da Adnan dukanmu a U.S mukayi degree d'inmu bayan mun kammala muka dawo d'auke da kyakkyawan sakamako"

"Kwatsam bayan dawowarmu da wata uku sai daddy yace yayima Adnan mata d'iyar abokinsa mai suna bilkis"

"Kasancewarshi mutum ne mai hak'uri sai ya amince ba tare daya musawa daddy ba,ita kuma Mom tace bazai aureta ba saboda yarinyar  bata da tarbiyya"

"Fad'a ne ya kaure tsakanin Daddy da Mommy wanda har abin ya haddasa gaba tsakaninsu"

Ajiyar zuciyar da tayi ne yasa yayi saurin katse maganar ya kalleta "ya dai"
"Bakomai" ta bashi amsa,a zuciyarta tace _present abinda yake faruwa a gidanmu_.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Adnan dai ya cigaba da bawa Mom hak'uri akan insha Allah idan ya aureta zata canza hali,Mom tace sam bata yarda ba"

"Haka dai kin san namiji yafi k'arfi a fannin 'ya'ya Mommy dai bata so haka akayi auren Adnan da bilkis ya koma kano da zama saboda a can ya samu aiki a wani katafaren company na motoci dan yace shi yafi so ya gina kansa da kansa,ni kuma daddy ya sama min aiki anan C.B.N amma ko a lokacin bani da niyyar aure barni dai da wulak'anta duk macen da tace tana sona dan dama na gaya miki inada izza gashi bana jin magana,kuma dama ni da Adnan Allah bai d'ora mana biye-biyen 'yan mata ba"

DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅Where stories live. Discover now