Part 1

635 24 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Mumtaz123*
*INSTAGRAM @itz_me_real_oum_mumtaz.*  

           *charpter 1*

********Zaune take kan wani k'ayataccen kujera da ke cikin rantsattsen office nata sai faman juyawa take, gajiyayyun idanunta na kallon sama alamun ta yi zurfi cikin tunaninta!

Sanye take cikin wani rantsattsen kuma d'anyen leshi mai kyawun gaske d'inkin doguwar rigar buba mai ratsin ruwan zaiba!

Fara ce tas,kyakkyawa 'yar duma- duma saboda kallo d'aya idan mutum ya yi mata kai-tsaye ba za a ce mata siririya ba,ko kuma 'yar lukuta ita dai tsaka tsaki ce!

Kyakkyawa ce ma sha Allah na gaban kwantance! Doguwar fuskarta kuwa shimfid'e take da dogon hancinta da ya sake fito mata sihirtaccen kyawun fuskartata! Bakin kuwa jajayen labba ne masu dan fad'i kad'an wanda hakan kuwa sosai ya tafi da tsarin bakin nata! Itadunta sexy eyes ne wanda ke d'auke da eye lashes dogi kamar wacce ta sa mascara na asalin fulani!

Infact dai kawai mai karatu ya fasalta yanayin kyakkyawar matashiyar mai kimanin shekaru 24 da a duniya take! ya d'aya dilo a wurin _ALH ABDUL WAALI_

Wacce mutane da dama suka fi saninta da  __ZULAYKHA ALH ABDUL WAALI_.
Cike da tsananin kasala da ya zamto dabi'arta ta mike daga kujerarta ta alfarma zuwa bakin madaidaicin fridge din da ke gefe kad'an daga inda take a cikin office din nata,drinks ne makil kala-kala cikin pridge din tare da ruwa na gora samfarin faro,inda ta fiddo da robar freshyoo guda d'aya,wanda kuma ya fi komai yawa cikin pridge d'in.

Sai da ta sake ma kanta mazauni akan kujerar tata kamin ta balle bakin ta akan robar,ba ita ta sauke shi ba sai da ta shanye sa tas,inda ta sauke kakkarfar ajiyar zuciya tana yatsina fuska kamar wacce aka ma wani abu.

Tare da taimakon A.c d'in da ke cikin office d'in ne ya sa gumi ko kad'an bai sakko mata daga goshin ta ba akan abu mai sanyin data kora ma cikinta,wanda rabon da ta sama cikin ta wani abu tin yammacin jiya sai ruwa,ga shi kuma yanzu wajen karfe goma sha biyu na rana.

Wayarta da ke kan table nata ta d'auka samfarin iphone,fuskarta ce ta wanzu da wani lallausar murmushin da ya sa gefen kumatunta side d'aya ya loba(dimples),sosai kuma ta yi wani fitinannen kyau na ban mamaki.

K'ara wayar tata ta yi a kunnen ta a lokacin da ta latso number d'in da aka yi saving da _Abbana_ tana sakin murmushin da ke k'ara ma kyakkyawar fuskarta armashi.

Sai da wayar ta yi ring kusan shida kamin aka yi recieving daga d'ayan bangaren,wanda hakan ya sa Zulaykha fashewa da kukan da ka gani za ka tabbatar da cewa tsantsar na tabara ce ba wai kuka na gaske ba.

Daga ta can bangaren kuwa a rikice muryar dattijon ya ratso mata dodon kunnen ta inda yake fadin "afuwan yar albarka! afuwan 'yar albarka ki yi shuru kar ki sa Abbanki ma kuka kinji...?" Ya kare maganar cike lallashi,wanda hakan ya sa Zulaykha share d'an gulmammen hawayen ta daya zubo tana sakin murmushi zuciyarta cike da tsantsar soyayyar mahaifin ta da kaf duniya bata da tamkar sa.

Wata irin ajiyar zuciyar zuciya Abban nata ya sauke kamar wanda yayi gudun tsere daya sa ta sakin siririyar dariya cikin daddadar muryarta tace "kai Abbana kamar wanda ka yi wani aiki irin wannan ajiyar zuciyar?"

Shi ma dariyar ya sake daga bangaren sa ya ce "Kun ji min ja'irar yarinya...? Dan mai garinku ba ke ba ce kike neman saka Abban naki a uku umm...?"Ya yi maganar tasa me cike da tsantsar soyayyar da yake ma gudan jinin tasa.

"Abbana na yi kewar ka da yawa fa!" Zulaykha ta fad'a tana wani karya wuya kamar wacce ke gaban sa!  "Nima nayi kewar babyna sosai,da fatan kina kular man da kanki ko Mamana ?" "Sosai ma Abbana,yanzun ma kawai haka nan na ji ina son na ji muryarka ne kamin na yi sallah saboda na ga lokaci ya kusa!"

"Allah ya yi ma rayuwarki albarka 'yata! Allah Ya tsare mana ke daga sharrin mutum da aljan a duk inda kike!" Abban ya fad'a fuskarsa shimfid'e da murmushi a lokacin da yake ma 'yar tasa wannan kyakkyawar addu'ar,ita kuma Zulaykha sai "Amin-amin Abbana". Take ta faman maimatawa,tana mai jin nishad'i cikin zuciyarta.

Sun d'auki tsawon lokaci suna fad'a ma junansu dad'ad'an kalamai kamin sukayi sallama wanda idan mutum ya gan su a lokacin sai ya yi tsammanin cewa sun shekara ne ba su ga juna ba,bacin kuma yau d'in nan shida kansa ya kawo ta campanyn nata kamar yadda yake yi a kodayaushe saboda soyayyar da yake gwada mata mai tsayawa a rai ne da kuma ratsa jini da tsoka da ke sake kawo kusanci mai k'arfi tsakanin d'a da iyaye.

Wayan da ta yi da mahaifinta ne ya sa ta ji zuciyarta ta cika da farin ciki sai sakin murmushi take ita d'aya akai-akai kamar wacce aka ma albishir da gidan Aljanna!

Mik'ewa ta sake yi daga zaunen da take,wanda kuma dama babu gyale a jikin ta sai d'aurin dankwali na leshin da ke kanta,warware dankwalin nata ta yi da ya sa dogon gashin ta da ke nannad'e cikin d'ankwalin nata bayyana. Ma sha Allah na furta sabada yadda gashin kan nata ma abin kallo ne! Baki sid'ik da shi da ke d'aukar ido, ga kuma tsayi har gadon bayanta. wanda kuma daga gani sosai yake samun wadatacciyar gyara na ban mamaki.

Warwaron goal din da ke hannun ta ta cire su tare da zoben da ke mak'ale a yatsar ta sannan kuma ta cire takalmin kafarta a bakin toilet din da ke cikin office d'in ta shige da addu'ar shiga band'aki a bakinta.

Tsawon minti goma ta d'auka kamin ta fito,fuskarta,hannunta da k'afafunta digar da ruwa alamun alwala ta d'auro kenan. Bedroom d'in da ke cikin office d'in nata ta shige,inda ta dauki hijjap nata ta saka tare da shimfid'a sallaya ta fuskanci alk'ibila ta tada kabbarar sallarta a nitse!

Ninke hijap din ta yi tare da nad'e sallayar ta a lokacin da ta idar da sallah, ta fito daga d'akin,duk da ba ta ganin madubi hakan bai hana d'aurin d'ankwalin nata da ta yi kyau sosai ba,sannan ta bud'e k'aramar jikarta da babu wasu shirgi a ciki ta feshe jikinta da daddad'an turaren ta tare da gyara gashin girarta da suka tarwatse sakamakon alwalar da ta yi wanda ta sake fitowa face abinta kamar a sace ta a gudu.

Wayarta ta d'auka ta duba time ta ga har karfe biyu saura,wanda kuma an zarce lokacin da ake kawo mata lunch nata da mintuna  wajen 15.

Cikin takunta na k'asaitattun mata ta fito daga cikin k'ayataccen office d'in nata da ke upstairs,zuba ma ma'aikatan da ke kai kawo a down stairs ido ta yi daga inda take kamar mai son gano wani abu mafi mahimmanci.

Mik'a mata gaisuwa ma'aikatan ke yi a lokacin da ta gama sakkowa daga matattakalar benin,ko kallo ba su ishe ta ba,ballantana su saka ran za ta ansa masu,wanda kuma hakan sam bai dame su ba saboda sanin halinta na shariya da kuma taka duk wanda ta so a duk lokacin da ta ga dama idan ka shigar harkarta.

"'Yar gatan Abbanta an fito kenan". Wani kyakkyawan matashin ingarma dake sanye da suit mai ruwan toka ya fad'a a lokacin da Zulaykha ta zo giftawa daga inda yake zaune cikin k'aramin restaurant da ke cikin ma'aikatar,"um" kawai Zulaykha ta fad'a ba tare da ta ba sa amsa ba ta yi ma kanta mazauni akan wani kujera mai kyawun gaske.

Wata ma'aikaciya ce ta k'araso wurin jikinta na rawa ta tambayi Zulaykha abin da za ta kawo mata.

Tsawon mintuna 30 ta d'auka a wajen lunch din nata kamin ta kammala,inda suka fito tare da wannan guy d'in da ya yi mata magana a farkon shigowarta mai suna _MUSTAFA_ da ya kasance p a nata.

Tare suka haura zuwa office nata bayan ta d'auko wasu files a hannun cikin office nasa da ke makwaftaka da nata,inda ya ba ta ta yi duk wasu cike ciken da ya kamata tare da sake jaddada masa kud'ad'en da zai raba ma duk wani ma'aikaci da ma'aikaciya kamar yadda aka saba sannan suka yi sallama inda ta fito tare da jikarta da kuma wayarta zuwa  bakin wata mota madaidaiciya mai kyau,ita da kanta tayi driving zuwa gidansu da ke Maitama a garin Abuja.

*vote*
*comment*
*share*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang