BUTULU...part 35&36

38 3 0
                                    

            BUTULU


By
Maryam Abduul


  Wattpad @Maryamad856

page....35-36

-------------Duk yadda Abdallah yai tunanin abin zaizo masa da sauqi hakan ya faskara, tabbas yasan baqaramin babban kuskure ya aikataba Na korar Fatima dayai, meyasa ya aikata hakan wai ma?

  Yanzu ta ina zaifara nemo Fatima, ya zaiyi? Abu daya ya sani ya San ta nanne kad'ai ZAI sameta amma shikansa yasan baida idon daze kalli Na'ima har ya soma tambayatar Fatima.

Wayarsa ya zaro duk da cewa" yace "masa ya jirashi" amma bazai iya jiranba, yasan ta hanyarsu ne kadai zai iya samawa kansa mafita, take ya hau kiran layin Sabir.




***********

........Qarfe 11:00 Na safe taiwa Ammar a qofar gidansu Mansur Saida ya kirashi a waya sannan ya fito suka qarasa ciki.

     Suna tsaye suna zantawarsu a farfajiyar gidan Zuhriyya ta fito nan ta riskesu, nan ta shiga zolayarsu tana me dariya.

    Suna haka Abbansu ya fito zuwa unguwa karaf idansa suka sauka kan Ammar dake jingine jikin motar Mansur.

 

 
    Basusan Sanda ya qaraso wajenba saidai muryarsa suka tsinkayo yana tamayar"waye wannan"?

   

  Cikin ladabi Ammar ya shiga gaisheshi.

Cike  da murmushi Mansur ya hau gabatar da Ammar GA daddynsa amatsayin sa Na abokinsa.

 

Tun kan yakai GA aya Abba ya dakatarshi da shi ta hanyar tsawa cikin zabura kamar Wanda ake kyat yace" a'uzubillahi Mansur kasankwa mekake cewa, kanka daya kuwa, Bari kaji to Sam ban lamuntaba, wannan ba irin wadanda zakai abota dasu bane, Malam ka neme aboki dai-dai dakai tun wuri, daga rana me irin tayau banso Na sakya ganin ka dashi, kai kuma ya koma kallonsa ga Ammar kan ya Dora da fad'in" ahir dinka Wllh tun wuri ka sanar min d'ana."

Ammar zaiyi magana Mama da fitowarta kenan ta hau tambayar "meyafaru" nan fa Alhaji yahau sabani ta inda yake shiga batanan yake fitaba.

  Zuhriyya ce tace" haba daddy meye aibun ya Ammar mutum ne fa kamar kowa, meyasa bazamu qaunaceshiba ,meyasa bazamu soshi....."

  Cikin tsawa yace" dakata, oho Na fahimta wato duk bakinki daya ko, kema har dake aka kawomin wannan qazamin mutumin cikin gida yazo ya zubamin tsamin talauchi ko?

  "To Bari kuji daga rana irin tayau Wllh Na sakya ganin qafarka agidan saina karyata Na zubata a bola, maza ficemin agida"

Batare da ya jira amsar Saba ya juya kan Mansur yace" kai kuma daga Yau kasan matsayinka, kasan waye ubanka"

Cikin rissinawa Mansur yace" to Abba bara Na rakashi"

    "Ka rakashi gidan ubanwa" ya tsinkayo muryar Abban nasa, "kai maza ka ficen agida" yace da Ammar.

Cikin takunta Na sauri tace" Ammar tsaya"

  "Ke maza 'bacemin daga nan shasahar banza" Abban ya fad'a badan ranta yasoba ta juya ta koma cikin gidan ranta Na mata suya.

Mama kwa ku kallonsa batai ba saidai kullum tana "Allah wadai da wannan masifa ta Alhajin tare da fatan samun shiriya Dan dawowa dai-dai da gane cewar" me kud'i da talaka duk daya suke"

Haka Ammar yasa qafa ya bar gidan idon SA cike taf da hawaye, zuciyarsa Na masa suya, Dan Kawai baida hali shi d'in talakane, shine ake masa cin wannan kashin, har da neman tsarin shedan dashi sai kace ifiritu, insha Allahu zai yi aiki tuquro yasama musu madafa kuma madogara shida Mamansa" da wannan zancan ya qarasa gida.



***********

............Latifa CE kwance jikin Bash sai faman shafa mata wuya yake, cikin kissa yace" wai my love yaushane zan sami 'yanci ne?

'Dago Ido Tai ta kalleshi kan tace" kamar yafa?"

"Haba ke kuwa baby sai kace ba bahaushiyaba, nifa na gaji da hada shinfida da wani, ya kamata ace Na sami 'yanci"

Fashewatai da dariya kan tace" Wllh Bash kana bani haushi, Na gayama akwai ABINDA nake shiryamana amma ka kasa zama wayus, plz ka ban lokachi da kaina zakaji zazzaqan labari"

Rau sayar da kai yai gefe, yana Jin wani d'aci a ransa, kan yace" shikkenan badamuwa"

Lura datai da kamar yai fushi yasa ta yin anfani da kissarta wajen jansa fadawa Harkar da suka saba.

 

*********

........Awa hud'u kenan yanzu da daddy ya bawa Abdallah kan cewa"ya nemomai 'yar sa" sai dai har yanzu be San taqamaiman inda zai sami Fatima ba.

  Zaune yake kan kujera ya Dade goshinsa, tunani Kawai yake ta ina zai fara tunkarar Na'ima?

  Sabir ne ya shigo, kallo d'aya ya masa yasan tabbas yana cikin damuwa sosai to amma koba komi ai shi ya jawa kansa koma menene gwara ya d'and'ani kud'arsa shima.

Dafashi yai kan yace" yadai abokin har yanzu baka samo mana mafita ba?

Tsaki yai kan ya kauda kansa gefe kana yace" banganeba? Ba cakai na tsaya anan zaka dawoba?"

Habawa me Sabir ze in ba dariya, shi ba tambayar ce ta BASHI dariya ba a'a yadda yai maganar shi ya sanya shi dariya.

"To in Banda abinka kaima ai ba tsayawa zakai jiranaba, kamata yai kasamo mana wata hanyar?

Batare da ya kalleshi ba yace" Na'ima"

Maida sunansa yai sosai kansa kan yace"wace ita ,a ina take, meye had'in ta da matsalarmu?"

  Sai alokacin Abdallah ya juyo kan yace" qawartace kuma 'yar uwarta tanan garin ita ta zame mata komi "

 

*Mrs.Abduul ce*

             BUTULU.....Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu