BUTULU.... part 27

64 5 0
                                    

*BUTULU*

By
  *Maryam Abduul*

*Wattpad@maryamad856*

*My Face book Maryam Abduul*

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫


Daga marubuciyar
*BIYAYYA*

*Part......27*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

****************Ko sallama babu a bakin nasa ya shigo cikin gidan zuciyarsa afusace take dan barin shi kenan daga wajen wani malami da yake tarasu yana musu wa'azi duk sati.

To yauma kamar kullum haka ya ajjiyesu gabansa, cike da tsantsar kulawa yake fad'a kar dasu illar cin amana da mutabe sukeyiwa 'yan uwansu, shi jiyake ma kamar danshi malamin yayi, sai dai wani 'barin na zuciyarsa nacewa"a'a badakai yakeba"

To ganin abin ba qarauba yasa shi tattaro takalmansa yayo gida shine yashigo ko sallama babu.

Mama Suwaiba dake shara atsakar gidan jin fadowar mutum gida ba sallama yasata d'aga kai dan ganin waye haka?

Ido hud'u sukai da malam dake tafaman 'yan maganganunsa wanda bamai iya jiyowa.

Kallonshi tai kan tace" haba malam sai kace ba d'an musulmi ba kashigo gida god'e-god'e dakai ba sallama"

Kallonta yai cike da takaice yace" wato kewai sabida Allah duk yadda naso na hana wata kalma shiga tsakanina dake bazaki iya haquri bako, nayi shirunma amma hakan bai wadatar dake bako, to shikkenan ai sai kitayi tunda baki da aikin yi" yana gama fad'a yawuce fuuuuu zuwa d'akin Tabawa.

Ita kam Mama Suwaiba kallonshi tai tare da girgiza kai kan tace" Allah ya huce zuciyarka malam" tacigaba da abinda takeyi.

Yana shiga ta shimfid'amai tabarma aqasa tare da ajjiyemai kwanan abinci agabansa, qamshin abincin ne yadake hancinsa hakan yasa shi kasa haquri har saida yakai lomar abincin bakinsa.

"Kai amma alqur'an na yau yafi na kullum ma dad'i abincin nan, daman kin iya girki haka kike bari ina cin wancan jagwalgwalon?" ya tambayeta tare da kafeta da idanuwansa.

Tabawa tai tsaki tare da janye kwanon daga gabanshi kana tace" aikin banza malam kabani kunya wllh, to ka gama cin abincin daga wannan, daman nima kawon akai daga maqota ko ci banba na ajjiyemashi to kaiwa kanka"

Cikin sanyin murya yace" haba Tabawa ta mene haka kuma, yanzu kimin rai ki bani naci ko yane wllh da yinwa na dawo gidan"

Hararatsa tai kan tace" ai wllh na rantse ka gama cin abincin nan sai dai kaje ka kuma san yadda zakai, gobema ka qara yaba abincin wata agabana"

Haka malam Aufu yashiga yiwa Tabawa magiya akan tabashi abincin, amma sam taqi, ganin yadda tahau sama yasan bazata sakko ba haka yaja tsimmikaransa ya fice daga d'akin cikinsa namasa kukan yinwa.

Wajen Mama Suwaiba ya wuce kai tsaye yana d'aga labulen d'akin yace" ki bani abincina"

Mama Suwaiba ta kalleshi kallon mamaki kan tace" kamanta yau banice da girki ba"

Cikin hasala malam yace" ai nasani ko, ba kuma tambaya ko zancen banza nace kiminba, zakiban ko kuwa"

Itakam ganin hakan sai yabata dariya wannan shi ake kira da" qarfin hali 'barawo da sallama"  a hankali ta bud'e kwanon abincin da tazuba yanzu ta miqamasa kan tace" adai dinga kai zuciya nesa ana tunawa da Allah"

Kallonta yai da nufin fad'ar magana kome yatuna koma ohhho sai ya sauke labulen d'akin tare da ficeea daga d'akin.

Itakam Mama Suwaiba dariya kawai tai dan tasan bazai wuce taso ce ta had'o suba.





             BUTULU.....Where stories live. Discover now