Part......53&54

42 6 1
                                    

      *ZAFAFA WRITERS FORUM*
             Z.W.F


            ******BUTULU

         NA
*Maryam Abdoul*
     (Mai_'Kosai)


      Wattpad@maryamad856.

Part....53/54.

Typing.........




Bisimillahir Rahmanir Raheem.



_______Dariya sukai gaba dayan su, "Aunty kije dai yana jiran ki" Saliha ta fad'a.

  Daf da zata fita Salma tace " asha love lafiya Auntyn mu"

  Bata kula suba tai ficewar ta.

Bata tadda Na'ima a falon ba haka nan bata ga motar ta a parking space ba, murmushi tai tana jin jina irin qaunar da take mata.

" insha Allahu saina cika miki burin ki" . ta fad'a a sanyaye.

   Yana zaune yana danna wayarsa, sallamar ta ce yasanya shi ajjiye wayar gefe, kamar qaramin yaro haka ya kwabe fuska yace.

    " Sabida family sun dawo aka manta dani ko?"

   Cike da murmushi ta qarasa kusa dashi, 'yar dariya tai kan tace.

     "Wace ni, ni na isa namanta da habiby na"

  
  
   Dariya yaibkan yace "ke asu d'an wake  a hotel"

Cunu baki tai kamar qaramar yarinya tace " nagode da matsayin da aka bani"

  Murmushi yai kan ya shiga aikin bada haquri na kuskuren da ya tafka.

 

   Cikin salo na nuna tsantsar tsafatatacciyar soyayya suke hirarsu, wacca rabin hirar ma akan yadda lamarin shirye-shiryen auren nasu zai kaya ne.






          %

..............Dai-dai 'kofar wani madaidaicin gida suka tsaida mai napep d'in, kudin suka miqa masa kudin ya qara gaba.

   Sallama sukai, tana zaune tana dauraye kwanikan da tai anfani da su, dan bata son taga ta ajjiye kwanika sun kwana bata wanke ba.

    Cikin murmusawa tace " sannunku da zuwa"

  "Yawwa Innar mu "  suka fad'a tare da darawa.

  
Ammar kam Saida ya durkusa har qasa sannan ya shiga gaida ta.

   Ba yabo ba fallasa ta amsa masa fuskar ta dauke da murmushin da ya zame mata jiki.

Kallon su ta shiga yi cike da son qarin bayani daga garesu.

   Nan Tijjani wanda shine ya janyo ra'ayin Ammar zuwa gidan nasu ya hau bata labarin yadda suka hadu da tahowarsa tare da su.

  Sosai tai murna, ko ba komi ta sakya samun wani d'an .

   Nan ta shiga kwantar mai da hankali tare da dada nusassheshi akan rayuwa da ya nayinta.

     Inna Rabi kenan , mijin ta ya Jima da rasuwa shekaru goma sha daya baya,  bata da d'a ko daya bata ta'ba haihuwa ba, amma tana da son yara , wannan yasa kowanne d'a tagani takejin sa kamar nata.

    Ta tsinci Tijjani ne a zanin goyansa, Wanda ko jinin dake jikinsa ba agoge ba. shi kuwa Halliru almajiranta yazo yi garin, tun yana debo mata ruwa tana biyan sa, har  take ya dawo gidan nata da zama.

  Tana matuqar ji dasu, duk wata kulawa tana qoqarin basu ,duk da ba wani qarfi gare taba, amma tana yin 'yar sana'arta ta hannu tana samin abinda suke samun na sanyawa abaki.

Har su Tijjani suka mallaki hankalina kansu, har yazamana yanzu bata komi , sai dai su fita su nemo su kawo mata.

  Halliru kuwa ,ko kadan besan komawa garin su, duk randa tace " ya shirya yaje" to tamkar ta jefa masa nashi a qahon zuciyar sane.

  'Daki guda daman ta ware musu a gidan, kasancewa gidan dakuna ukune , sai kitchen da bandaki.

   Bayan sun gama 'yar hirarrakin sune ,tace " suje su kwanta haka"

  Koda suka shiga d'akin, nan hira suka barke da ita, yayinda Ammar ya zuba musu Ido yana mamakin sirutun su haka, kodan shi bameson hayaniya bane oho.

    %

   Washe gari da safe , Inna Rabi ta hada musu abin Kari, sukazo SUKA d'auka.

  Sai goma suka fita neman na kansu, koda sukaje Ammar cayai Bari ya gwada shoe-shining shi ya gani.

    Aikwa cikin ikon Allah ya fara samun masu kawo masa dinkin takalmi, ganin hakan yasa shi miqewa tare da d'an tattakawa.

  

      %

     Abdallah kuwa koda su Daddy suka fita, kasa daurewa yai, dan me za'a dakeshi a hanashi kuka ,tabbas sai ya kai qarar koma waye yakeson shika tsakanin su da Fatiman sa, dole zaije ga alkali Dan dakile auren da Fatima keson yi.

  Mukullin motar sa ya d'auka ya fice daga gidan.

  Kai tsaye koto ya wuce, "tabbas shigarta da qara zaiyi, tunda Anson rabashi da ruhinsa."

   Da wannan tunanin yayi aran gama da alk'alin dake shari'a a wannan lokacin.

  Take ya neme shigar da qarar, kuma ya samu.

    Daddy ne zaune yana waya da Abba ,duk da cewa " ya 'boyemasa wani abun ,ciki har da sakin da Abdallah ya mata".

  Aka aiko masa da takardar sammaci, mamaki ne sosai ya kamashi ,wai Yau  d'an SA ne ke shigar da qara akan sa? Kuma akan abinda shike da laifi.

  Tabbas zai halacci zaman koto, kuma Kowa zaije, amma zasu bashi matuqar mamaki iya mamaki.

   Nan ya shiga cikin gidan yake shida musu abinda ke wakana.

  Kowa saida ya girgiza, Saliha kam masifa ta dingayi, akan muddin Fatima ta yarda ta koma gidan sa, to sun raba jaha.


     %

Abdallah kam koda ya koma gida ,jinsa yake wasai, dan gani yake "Fatiman sa ta dawo "

   Ko takan Lad'ifa bebi balle yasan wacca nahiyar take, shidai Allah-Allah yake gari ya waye da yake gobe alkali yasa musu ranar sauraran shari'a tunda baida qara da yawa a goben.

Tofa bari mud'an jirayi goben mugani ,shin zaiyi nasara ko kuwa?

    Sai mun had'u a koto.......

Vote and Share........

*Mai_k'osai ce..........*

             BUTULU.....Donde viven las historias. Descúbrelo ahora