Part.....59&60

37 3 0
                                    

    *ZAFAFA WRITERS FORUM*
                 Z.W.F.......

    
           ______BUTULU______

       NA
MARYAM ABDUL-AZIZ
    (MAI_K'OSAI)

  WATTPAD@MARYAMAD856.


   Page.....59$60

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.




________Ranar juma'a sukayi gagrumar walima, da kamu abin gwanin ban sha'awa,duk yadda Hisham yasu su fita Fatima tak'i Bari, a cewar ta "ayi komi a hankali yafi aje a barnatar da dukiya a banza"

     *Ina Kira gareku masu biki, da dai ku fita ku nuna duniya cewa kun zubar da dukiya, gwara ku Kira mutane kuciyar dasu ku shayar dasu, ko bikin naku yayi albarka ladan wannan ciyarwar da shayarwar*

    Ranar Asbar tai yi ninta dasu hajiya, inda ranar lahdi aka daura auren Fatima Muhmud Waro da Hisham , yayin da sutin kunnuwa na suka kuma jiyomin d'aurin auren Na'ima Bashir Turajo da Dr.Auwal Farouq Khamis.

    To fa meke faruwa ne????

   

       %

Tunda Abdallah ya koma gida ya kasa ta'buka komi, kwanan sa biyu yau a gida ko nan da k'asan gidan baya sakkowa yana sama abinsa a kwance, iya kaci yaci biscuit yasha lemo.

    Koda sakatariya ta kirashi cayai "tayi komi ta rufe ma'aikatar, karta kuma kiransa"

   Duk da ba yau ya saba mata haka ba, amma koma menene ai ba a dinga cewa" a rufe ma'aikata ba."

   Bata sakya bi takan zancan nasa ba, P.A ta Kira da manager ta gaya musu halin da ake ciki, had'a kai sukai suka cigaba da rik'e ma'aikatar su ukun.


       %
Su Ammar kam ranar da sanya musu wato Monday ranar suka kai masa ziyara ,inda ya yi musu wasu tambayoyi, anan yaga cewar ma ai Ammar yana da shedair karatu na N.C.E, su kuwa kam iya Secondary suka tsaya, Wanda shima da temakon Inna sukai.

   Nan ya bawa Ammar sashin Hulda da safaya na motocin sa, ya bashi manager, yayin da yabawa su Tijjani bangaren kula da baqin sa na Restaurant din da yake dashi, sune zasu Na kula da duk wani shige da fice, da kuma duk baqin da zaiyi daga ta wajen.

   Murna kam kamar me, koda suka gayawa Inna itama farin ciki tai sosai, da sosai, nan tai ta musu fad'a da Nasiha akan su rike amana da alqawari.

  Ranar litinin me zuwa zasu fara zuwa office, kuma kowanne Saida ya mai sha Tara ta ariziki.




      %

Salma ce ta shigo hancin ta d'auke da guda, da gudu ta dane Na'ima tana dariya tace "Ashe kece kika dauke mana yayan ku,?, kai wllh naji dad'i sosai, daman ina tunanin wacce Aunty zan samu da zata kula dani, Ashe kece"

   Cikin mamaki da neman qarin bayani take kallon ta.

    " kamar ya fa??"

Ta tambayeta da sauri.

Salma cikin karaji tace " ehh man, kina nufin kice bakisan cewar ki matar yaya na bace kenan??"

   "Bangane ba, wanne yayan naki, kinga bana son wasa ko zancan da ba tushe".

   Salma ta gyara zamanta kan tace, " wai Aunty bakisan wainar da ake tauyawa bane, wallahi da gaske nake kin zama matar yayana , ina nufin an daira aurenki da Dr.Auwal yanzu ke din matar shi"

  Zuruuu tayi a zaune kamar wacca aka dasa, takasa cewa komi ma, dai-dai shigowar Hajiya tana fad'in " Fatima , Na'ima maza ku shanyan wannan ko kuma zo inji Daddynku".

             BUTULU.....Où les histoires vivent. Découvrez maintenant