Part.....21

78 5 10
                                    

*BUTULU*

Writing by
    *Maryam Abduul*
   
*Wattpad@maryamad856.*

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
   *BIYAYYA*

Dedicated to you
   *My luvly Dad* Allah yaja da kwananka.

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

*Part......21*

..................Da safe kam koda malam ya mata magana akan abin kari bata cemasa qalaba haka ta dakko kunun data dama ta bashi Allah sarki baiwar Allah har da qosan data siyo suka karya dashi ta rage mai.

Bayan ya kammala karyawarne ta tunkareshi da maganar kudin da kuma kasiwancin da zaiyi, nanfa yashiga" zazzagamata fad'a tare da mata kalamai marasa dad'i",,

Ba kunya ba tsoron Allah yake gayamata cewa" zaiyi aure" duk da ta rigada taji maganar, amma hakan sai da yasa taji dum, sai dai ba yadda zatai  jin hakan yasata" fara bashi haquri" daga haka tai shigewarta daki batare da ta sake cewa komiba.

Shikam in banda faman fad'a da mita ba abinda yakeyi har yafita daga gidan.

Yana fita ya wuce wajen bazawarsa, yayin dabita kuma tashiga aikin sarrafa kan gidan.Ammar kam ficewarsa yai wajen nemawa kansa abinda zasu samu.




............
Kamar yadda suka tsara haka aka sa sati daya na zagayowa aka d'aura aurensa da Tabawa, a daren ranar ta tare agidanta.

Washe gari kam malam ya fito da fara'arsa zai fita, yayinda Mama Suwaiba ke share gidan.

Gaidashi ta shigayi tare da fad'in " malam ga abin karin naku can ka fita baka karyaba?"

Wata harara yadakamata kan yace" ni an gayamiki nayi kala da cimar abinda kika ce, to kisani da dayanzu ba d'aya bane ki kuma fita daga sabgata"

Kallomshi zuciyarta na mata qona kan tace" da kayi aure kenan malam har kasan cemar mu ba d'aya ba, amma inaso kasani duk wani abu da zakai ka dinga tunawa da Allah yana ganin ka a ko'ina, kuma zai maka hisabi kaida wanda ka zalunta, ita wacce ka d'akko ka kawo gidan baka cemata da kudin wata kai auren ba"

Cikin masifa da borin kunya yake fad'in " yayi kyau Suwaiba wati wuyanki har yakai riqar da zaki dinga gayan magana ko, har nawa kudin yake dan kin bani kudi shine zaki na gayan magana, matsalar mata kenan shiyasa ba'ason karbar abin suba sabida duk tsiya sai sunma gori"

Mama Suwaiba taja nunfashi kan tace" koma dai nawa yake ai dai gashi kayi aure dashi wllh malam ka ji tsoron Allah"

Kafin yabata amsa Tabawa ta katsesu da fad'in " masoyi lafiya mekake baka tafiba"

Nan yashiga wage baki tare da fad'in " ina kwa naga ta fita wannan tasani agaba" ya fad'a yana nuna Mama Suwaiba.

Tabawa ta harareta kan tace" ke lafiya da safe zaki tsaren miji ki bashi hanya ya wuce wllh ko rai ya baci"

Mama Suwaiba data shaqa sosai cikin zafin zuciya tace" nawa mijin yake da za'a bashi hanya, kar kimanta sai da nace na rage dai, na rigada nasan komi kan kisani, kuma wllh sai dai duka rayuka su baci ehhn"

Tabawa na jin haka ta d'aga hannu da niyar kai mata mari, cikin zafin nama Mama Suwaiba ta riqe hannu game da fad'in " a hir dinki wllh baki isaba baki da wannan matsayin"

Kafin ta sauke hannuta daga na jikin Tabawa sai jitai kawai an d'auke ta da zazzafan mari afuska, kallonshi kawai ta shigayi kan tace" ni ka mara akan kayi amarya ko malam, ba komi kaje kaida rabbil izzati bazan ce zan ramaba dan ni nasan yaya ibada take"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now