Part.....19

91 2 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
       *Maryam Abduul *

Wattpad@maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
     *BIYAYYA*

*Part.......19*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

....................Abincin daren datai musu da shinkafar daya kawo musu d'azo shi takawo masa , sai da ya kammala cin abincin sannan ta gyara zamanta tare da fad'in " malam d'azu nace zamuyi magana, amma baka dawoba"

Ya kalleta yayin da yake sud'e hannunsa kan yace" inajinki to yanzu ya akai"

Ta d'anyi murmushi kan tace" daman akan maganar kasuwancine, naga har yanzu bakace ga abinda zakai ba, kuma kai bakace ga kudinba"

Sai da yagyara zamansa sosiy ya kalleta kallon haka-haka kan yace" to sai akai yaya, yanzu dan kin d'au tumakinki kin bani shine yazama abin magana, wannan kuma ba ruwanane ba , kedai bakin bada kyauta ba, matsalar ku ku mata kenan bazaku ta'ba bada abuba sai kunyi gori kun nuna halin ku ko,?"

Ta dan rausayar dakai kan tace" haba malam yanzu duk me yakawo haka kuma, maganace fa akan kasuwanci meyasa kuma zaka juya maganar, banyi niyayyar baka ba zan baka"

"Au to wayasani kuma, kya santa dai"

"Kayi haquri malam, amma dai yakamata ka yi abinda akace da kudin nan kar azo ana lahaula kuma"

"In naqi fa sai yaya?" ya tambayeta a fusace. Ita dai bata iya cemasa qalaba tai shigewarta d'aki, tana mai jinjina halin irin nasa.

Malam Audu kenan haifeffen d'an qauyen dake cikin garin qiru, yataso cikin rashin gata dan mahaifinsa tun yana qarami Allah yamasa cikawa, mahaifiyarsa ce kawai ta ragemai, domin duk dangin mahifinsa basansa sukeba acewarsu mai zai qaresu dashi, tunda baida komi hasalima uban nasa ai bai bar masa komi ba.

Malam Audu yayi fad'i tashi wajen ganin ya nema musu abinda zaau dinga sanyawa abaki shida mahaifiyar tasa.

Sai dai hakan bata samuwa dan wani sa'inma da yinwa suke kwana.a haka rayuwa ta dinga garawa yayinda mahaifiyar tasa ke aikin wankau ana biyanta.

Wannan shine rufin asirin dasuke samu suci dashi.har wata rana yaga Suwaiba tun daga lokacin kuma yafara bibiyarta yana nuna mata so, dayake itama d'in taji tanason shi saita aminci masa har takai magana taje ga magabata.

Sanda mahaifiyarshi wacce suke kira Inna taji wannan batu tashiga tashin hankali soaai dan dai tasan bashi da abinda zaiyi auren.

Amma ganin abokinsa malam haladu yabata baki tare da nunamata cewar" shi zaimai komi" yasata samun nutsuwa har ta sanya albarka a auren.

Da yake suma dangin matar bawani wadatace garesu ba sai dai ba kamar su malam Audu ba dan su da wuya surasa abin dazasu sa abaki, suna da rufin asiri ba laifi.

Haka dai aka gargad'a akai wannan biki, yayinda aka kai amarya gidanta, wanda asalinsa ma kyautace daga wajen abokin nasa, danshi yana sana'arsa ta saida nama da kuma kayan miya, ba laifi kuma yana samu sosai Allah yasa mai albarka shiyasa mai rasa abubuwa.

Bayan bikin malam Audu da shekara d'aya Allah ya azurtasu da yaro, inda ran suna aka sanya masa suna *AMMAR* yaro yasami rago dan sosai malam Audu yadage wajen fitar kunya

Bayan shekara biyu da aurensa Malam Haladu inda shima yanzu yana da d'a namiji mai suna Saleh.

Wanda nan suka suma shaquwa da Ammar sai dai shi Ammar yana qoqari wajen neman nakasa dan yanzu shekarunsa sun kai 22 yanzu haka yana sana'arsa ta shushyna.

             BUTULU.....Where stories live. Discover now