Part......69&70

29 1 0
                                    

  *ZAFAFA WRITERS FORUM*
         Z.W.F.........




           _______BUTULU_____

NA

    MARYAM ABDUL-AZIZ.
         (MAI_K'OSAI).

WATTPAD@MARYAMAD856.

Page.......69%70

Bisimillahir Rahmanir Raheem.





__________Yadda Alhajin sukai da Latifa hakane ta faru, inda yaje wa mahaifinta da buqatarsa, kuma yayi na'am amma yace " yabashi kwana biyu kafin yaji daga gareshi".

      %

Alhmdulillah jikin malam Audu yana ta samun sauqi, inda koda da 'batan lokaci Tabawa bata kaimasa ziyara ba, acewarta ai shi d'in gawa ne to me zataje ta duba.

     Suna zaune a tsakar gidan, suna sheqa ayarsu ita da 'ya'yan nata kamar daga sama suka kaga 'yan Sanda Na shigowa gidan.

   Ko magana basuyi ba suka cafke Taga nanfa ido ya fara raina fata.

   Cikin rud'ewa Tabawa tace " malamai lafiya zaku shigo gida ba izini kuma har ku sawa d'a na ankwa?"

    Wani daga cikin sune yace " mun zargin d'an ki da safarar miyagun kayan, Dan haka zamu wuce dashi can Dan bincike"

    "To ai kaima kaji me kace zargi kace, dan haka ba inda zaku dashi"

  Galla mata harara yayi kan yace " ku wucemin dashi"

   Yowa kansa tai zata mai rashin kunya nan yasa bakin bindigarsa ya saita ta, akan in ta kuma taku zai harbeta.

  Su Tabawa an hango lahira, tuni ta sami nitsuwa ta d'orawa kanta.

  Tanaji tana gani suka iza qeyarsa sukai gaba dashi, wannan shine kamu na uku da akayiwa Taga.

Ihu ta fasa, yanzu ya zatai daman ga halin da suke ciki na cikin da 'yar tata takwasu mata, yanzu kuma ga wannan, to da wanne zataji.


             %

Sanda suka isa har lokacin Fatima na comma , saidai Kawai kaje ka duba ta, batare da tasan waye yajeba, halin da ya ganta ya matuqar tausaya mata sosai, tabbas da da yadda zaiyi to da yasa ta farka.

  Abu daya Kawai yamata shine addu'a akan Allah ya tashi Kafad'unta.

  Haka ya koma gida jiki a sanyaye, zuciyarsa fal da tausayin bayin Allahn biyu.


         %

Yau da izinin Allah Malam Audu ya farka, zo kuga murna wajen su Mama Suwaiba.

   Bayan komi ya lafa Ammar ya gabata gareshi, nan fa Malam Audu yaita neman afuwarsa akan abinda ya jima na rashin kyautatawa da yake aikata masa.

   Inda kowa yai farin ciki da Ammar yadda ya nunawa uban bakomi, duk abinda ya faru jarrabawace kuma k'addarace ya yarda da hakan, yanzu ai gashi suna tare.

      Koda komi ya lafa gidan su Mansur suka wuce ,wanda zulaiha ce ta gayyaceshi gayyata ta musamman.

   Sanda yaje baban nasu be nan, balle su had'u dashi, duk da yana fargabar taya zai kalleshi.

   Sosai suka gaisa da mahaifiyar tasu, kan ya Hana da zulaiha d'in.

   Hira suke inda take tsokanarsa akan yayi kyau, ya sauya kamar ba shiba.

   Dariya yai kana yace "duk sau yawata ai bankai gimbiyar zulaihat ba"

  Itama dariyar tai kan tace" hmm wannan kuma sabiwar game ce ka kawo ko?"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now