BUTULU....PART...22

62 2 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
    *Maryam Abduul *
   
*Wattpad@maryamad856.*

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
   *BIYAYYA*

*Part......22*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

................Malam Audu ya kalli Ammar cikin zafin zuciya yace" dan ubanka ita d'in sa'arkace da har kake gayamata magana, to kayiwa uwarka datake zugaka"

Ammar ya sunkui da kai qasa kan yace" kayi haquri baba, amma ni ban mata rashin kunyaba"

Ba zato ba tsammani malam yakai masa mari akumatunsa, hakan yasa Ammar dafe kuncin nasa, malam ya dubeshi kan yace" maza wuce dan uwraka ka debo kuma ka tabbatar ka cika komi nata in bahaka sai na tattakaka"

Mama Suwaiba da tunda suke abinsu bata sa baki ba sai yanzu, cikin qonar rai tace" haba malam meyasa kake abu ba bincike, sabida Allah yaron nanfa nema zai fita kuma tun asuba ya d'ebo amma ba za'a barshi yai harkar gabansa ba"

Malam ya dubeta ayatsine kan yace" wato ke kike daure mai wajen zama ko, wllh ki fita daga ido na in bahaka yanzu ranki ya baci"

Har ta bud'e baki zatai magana Ammar ya katseta da fad'in " Mama kiyi shiru ai baba yana da haqqi akaina, dan haka zanyi duk abinda yace dani" yana qarasaw ya wuce ya d'au bokitin ruwan ya fita agidan zuciyarsa na masa soya sosai.

Mama Suwaiba kuwa binsa kawai tai da addu'a, tare da juyawa zuwa d'akin ta.

Malam kwa shigewa yai d'akin dan bin bayanta da kuma bata haquri ganin yadda ranta ya mugun baci.

Ammar kwa na fita ya tadda wani abokinsa Mansur yana jiransa awaje, ganin hawaye kan fuskarsa yasashi qarasawa kusa dashi ya dafa kafad'arsa, kan yace" lafiya Ammar meya faru kake kuka qato dakai?"

Ammar ya gige hawayen nasa kan yace" bakomi yaushe ka qaraso "

Mansur da yakula Ammar d'in baison gaya mai dan tun tuni ya lura shi din mai zurfin cikine, kuma bai fiya fad'in sirrinsaba, shiyasa ma yake matuqar sonsa, hakan yasa qyaleahi batare da ya qara tambayarsa ba, nan yace" suje ya tayashi"

Duk yadda Ammar yaso ya hana Mansur zuwa hakan bai samuba.dole ba yadda ya iya haka ya rabu dashi ya rakashin.

Mansur d'a ne ga Alhaji Bello hamshaqin mai kudin cikin qauyen ne sai dai kokad'an bai son alaqarsa da talakawa, kuma suma 'ya'yan bawani samu suke daga wajen shiba.

Matar sa d'aya mai suna Lubabatu, sai yaransu biyu Mansur shine dansa na farko kuma babba sai auta *Zuhriyya* mai sunan mamanshi hakan yasa yake cemata Mamana.

Bayan sun debo ruwan ne ya temakamai tare da saukeshi abakin makarantar da yake d'an zuwa yana zama, dan ba laifi yana samun customer acikin makarantar.

Yauma hakance ta faru yana zaune yana tunanin halin da suke ciki, qwalla ce kawai take zubomai a saman kumatunsa.

Wasu 'yan matane su biyu, hannun dayar riqe da takalminta wanda ya tsinke tafiya suke suna dan hirarsu.

'Dayarce ta dafa kafad'ar d'ayar tace" lah kin ga wani canma zaune ba sai munfita har gate ba mun huta"

Wacce aka dafa d'in ce tai murmushi kan tace" kai amma naji dad'i wllh daman na gaji"

Wacce tafara magana da farko itace tace" dalla kedai wllh kin banu kin fiya lalaci"

Ita dai dayar dariya tai kan tace" kinga malama kawai muje"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now