Butulu...part..43&44

36 5 2
                                    

        *BUTULU*  ...........

By Maryam Abdul'aziz
          (Maryam Abdoul)

Wattpad @Maryamad856


Part.....43&44



         ......................Dai-dai qofar gidan su Dr.Auwal sukai parking, Na'ima ce ta fito taiwa Baba me gadi magana ya bud'e musu.


             Bayan sun dai-daita parking din daddy yamata izini akan ta nemamusu iso acikin gidan.

            Tana shiga ta Danna layin Hajiya bugu d'aya ta d'aga "Hajiya kizo gidan Ummi muna can harsu daddyn" tana gama fad'a ta katse kiran.

             Qarasawa Tai ciki bakowa a falon, hakan yasa kai tsaye ta wuce d'akin Ummi, zaune take tana Jan jarbin ta, bayan sun gaisane ta sami waje ta zauna, nan ta shiga labarta Mata abinda ke tafe dasu har da daddy.

        Nan ta umarceta akan ta musu iso.


           Tar'ba sosai suka samu daga wajen Ummi, har lokacin Fatima da Salma na d'aki ba Wanda yasan wainar da ake toyawa.


           Cikin d'oki da hanzari Na'ima tai d'akinsu, Salma Na kwance tana karatun littafin *Waye za'bin Mubeenat* Na Mrs.Abubakar, yayinda Fatima ke sharar baccinta.


            Qarasawa tai daf da Fatima ta huta Mata iska a fuskarta, abinka da mara nauyin bacci, hakan yabata damar bud'e idanta.

           "Zo muje kika wani surprise" ta fad'a tana me Jan hannunta, zatai magana tasa Mata d'anyatsa abaki alamar Tai shiru.

           "Au ni Aunty Na'ima Babu Niko, abin 'yar......." Salma ta fad'a.


        "Kema muji" Na'ima tai saurin katseta ,dariya sukai suna me ficewa daga d'akin, dai-dai lokacin Hajiya ta shigo falon.

           Qamewa Tai a wajen bakinta Na San furta wata kalma amma takasa, ganin hakan yasa Na'ima dafata tare da fad'in " Teemanah daddy ne"

          Sai alokacin ta sami ikon fad'in " daddy na, Kaine?"

            Cike da d'okin ganin ta yace "nine ''yata ta kaina, qaraso kiga daddynki"

           Da sauri ta qaraso tar da durqusawa gabansa ta riqo hannunsa, " daddy Ashe zan sakya ganinku, ina Granny Na da Saliha?" Ta tambaya.

             Dariya yai wacce ta sakay bayyana irin farin cikin da yake ciki yace" muna nan kuma zaki sakya ganinmu diyata, har ABADA muna tare da yardar ubangiji, suna nan amma basusan cewa Na hadu dake ba"

          Yaja dogon nunfashi kan ya sauke yace" 'banta'ba tunanin cewa d'an uwa zaiqi d'an uwa ba, ban ta'ba tunanin cewa d'an uwa zaiqi 'yar uwaba, Ashe duk hasashena gaibune, meyasa ? meyasa zai aikata miki haka diyata, tabbas ya aikata kuskure mafi muni Wanda bazamu ta'ba yafemasa....."

             Cikin sauri ta tare nunfashinta game da fad'in "a'a daddy ni ba abinda yafaru, komi daka gani daga indallahi ne sarkin da Babu kamarsa, ya rigada ya tsara zanyi aure kuma zan fito, Dan Allah kumasa afuwa" ta qarasa tana me share hawayen da suka zubo Mata.


              Kowa Na wajen jikinsu yai sanyi tabbas komi jarrabawar ga bawa inyai haquri da juriya har ya cinyeta to Allah zai masa sakamako, to amma duk da haka Abdallah ya tafka babban kuskure mafi muni agareshi ,domin ya *butulcewa* ni'imartarwa da Allah yamasa.



         Nan su Hajiya suka shiga bashi labarin iya abinda suka sani ciki harda sakin Fatima da Abdallah yai.

           Wani d'aci ne ya ziyarci maqogwaron daddy, jiyake zuciyarsa na masa zafi da soya, be ta'ba tunanin abin yakai hakaba, lallai d'an Adam *butulu*.

           Cikin dabara yashiga kwantarwa da Fatima hankali game da bata baki, duk da cewar daman yayi alqawari koda akwai auren tsakaninsu to tabbasa sai ya jigatashi mafi jigatuwa.




***********

       ....................Ammar kam shiri yake sosai akan tafiyarsa, inda yasa ranar cewa " gobe insha Allahu zaiyi tafiyar tasa"

Yaso ya hadu da Mansur amma idan ya tuna maganar daddynsa sai yaji bazai iya haduwa dashi Dan yana Jin zafin maganganun aduk lokacin da ya tunasu.

Gidan Baba Haladu yaje nan yake gayamai duk yadda sukai da Affa da kuma Mama Suwaiba kan tafiyarsa ,yaji dad'i shima sosai kuma yamasa nasiha tare da fatan alkhairi, inda yabashi wasu addu'o'i yace ya lazimchisu tsarene, yakuma lazimchisu azkhar ,da alqur'ani insha Allahu zaiyi Nasara akomi.


Duk wannan budurin da akeyi Malam Audu be saniba, Wanda sai ayanzu da Mama Suwaiba take sanar dashi batun tafiyar.

Batare da yawani damuba yace" kice dai zai tafi yawon duniyar tasa, wato duk garin nan be isaba sai anyi tafiyayyiya zuwa wani garin, to Wllh duk abinda ya faru Babu saniba ficikata bazatai aiki wajen fiddashiba kinji na rantse"

" Haba Malam wannan ai zato zunubi ne, komi zakai kadinga kyautata zato, kuma Babu abinda zai faru ga d'a na insha Allahu rabbi, kuma sai kayi alfahri dashi insha Allahu ". Tana gama fad'a tai cikin d'akin ta, yaukam tabajin komi zai faru saidai ya faru amma bazata iya jurar cin mutuncin da akewa danta kullumba.


Shikam Malam sai faman kumfar baki yake, Ana haka Tabawa tasawo kai wadda shigowarta kenan daga yawon maqota, kuma Malam Audu beda ikon cemata" daina" .




*Mrs.Abdoul ce*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now