BUTULU.... Part..25

62 4 0
                                    

💫 *DA BAZAR-MU WRITERS ASSOCIATION*💫

     We are here to make you happy....smile and educated to realized that we are the best Among all...... *DA BAZAR-MU MUKE TUNQAHO*💃💃💃


                     *BUTULU*

   *By*
      *Maryam Abduul*

    *Whattpad@maryamad856*
   
   
   
   
   
Wannan sadaukarwa ne gareki my luvly sweet Mom.... Allah yasaki a aljannatul firdausee....ameen.


*Part...... 25*


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


*************Cikin kwana biyu suka kammala komi aka kai kud'i  gidansu Affa, sosai sukai murna ganin sunkusa zama cikin inuwa d'aya.

Nan fa Ammar yafara qoqarin neman na lefe tunda ansa rana wata biyar masu zuwa, alhmdulillah Allah ya rufamasa asiri dan kwa yanzu yana samu ba laifi.

Kuma Mansur na d'an temaka masa da wani abu duk kuwa da cewa shi baison hakan, kuma baifiya kar'bar ba, acewarsa" hakan zaisa zuciyarsa ta mutu yakasa neman na kansa".

Shidai Mansur sai dai kawai yai murmushi ya qyalesa dan yasan komi zai cemasa bazai ta'ba yarda ba.

Zaliha ma na matuqar qoqarinta wajen ganin ta faranta masa dan sosai ta kejinsa acikin zuciyarta, tana san halayensa da yadda yake girmama kansa tun kan wani ya girmamashi.



...............Granny ce zaune tana shan fura, jiki kam yanzu sai dai ace alhmdulillah dan ta warware sosai.

Abba kam ya koma wajen aikinsa ma, kullum sukanyi waya da Daddy ko ma suyi video call.

Yanzumma wayar suke da Granny inda take cemasa" Auwal kodai za'a haqurani ka dawo kawai inajin tsoro sosai?"

Daddy yai murmushi kan yace" haba Hajiya wannan ma ai bai kamacekiba, munyi alqawari kuma insha Allahu zamu cikashi, ki kwantar da hankalinki insha Allahu zamu samuso duk inda suke ni inaji ajikina suna nan kuma zamu had'u watan wata rana"

Granny ta sauke ajjiyar zuciya kan tace" shikkenan d'an nan Allah yasa"

Daddy yace" yawwa Hajiya ko kefa, ina shalelen take ni ki bata nan"

Granny ta yamutsa fuska kamar tana gabansa tace" wani fita ta nanan, baccin asarar a saba takeyi, koda yakema yanzu zan tasota dan salla ake yi"

Daddy yai dariya kan yace" ah wannan tsakanin kune kawai nazo na shiga abar ni aciki, tam agaida min da ita, sai anjima"

Granny tai dariya irin tasu ta manya kan tace" kyaji dashi dai, yawwa ka kula da kanka dai sosai" nan sukai sallam.

Ko wannensu yana jimanta wannan al'amari yau tsawon wata hud'u kenan da zuwansu amma har yanzu ba wani cigaba da aka samu.

Yana nan kwance yaji wayarsa tai qara, koda ya duba sai yaga ashe text ne, company d'in da yatura musu da saqon san had'a kasuwancin ne suka amsa masa da " sun amince" Murmushi yai kawai ya koma ya kwanta.



..........Su malam Abdallah kuwa abin ba acewa komi duk tsawon wata ukun da suka d'eba shida sahibar tasa ba abinda ke had'a su sai fad'a , dan ita Latifa har yanzu bata daina wannan yawace-yawacen ba, yayinda shima bai fasa tambayarta ba, danma yanzu wasu ayyuka sun shamai kai, shima bai dawowa da wuri balle yagane ta gyara ko bata gyaraba.

Abinci kam sai dai idan yaje wajen Baba Ladidi shine yake samu yaci san ransa, wanda hakan yasa shaquwa mai qarfi ta shiga tsakaninsu, yakan jita kamar mahaifiyarsa dan yasan yanzu tunda bai da kowa anan.

             BUTULU.....Where stories live. Discover now