Part.......72

47 3 3
                                    

*ZAFAFA WRITERS FORUM*
        Z.W.F........



          _______BUTULU_____


NA
  MARYAM ABDUL-AZIZ.
      (MAI_K'OSAI).


WATTPAD@MARYAMAD856.
      

Page......72




Bisimillahir Rahmanir Raheem.




__________Kallon shi tai kana tace " ikon Allah, kace kai kun had'u  da sirikin na ka, amma naga da alamu baka ganeshiba??"

   Kallon ta yai shima cike da neman qarin bayani, a hankali yace " banfahimci zancen naki ba"

Murmusawa tai sannan tace " Alhaji kana tuna wanda yake zuwa nan kake korarsa, wanda kace kada d'an ka yai mu'amalarsu da matsiyaci, Wanda kacewa almajiri, to shine dai wannan d'in kuma ya dawo a karo na biyu tare da neman amincewarka akan 'yarka, sai kuma gashi Allah ya had'a ka da mutumin da ya baka kyautar abinda ya kufcemaka".

  Cikin sassarfa ya zauna dabas a k'asa, zuface kawai take karyomasa, lallai ba shakka kud'i me sauya mutum, tabbas duk wanda ya raina wani to shima za'a rainashi, kuma d'an hakin da ka raina shike tsokanema Ido.

   Nan kuma sai ya shiga da nasanin abubuwan da yajima yana aikatawa na yiwa  talakawa wulaqanci, tabbas talaka ba abin wulaqantawa ba ne, dan kuwa shi da ka raina shine zai zama ya jiqanka, kamar dai yadda ta faru akansa.

   Cikin nadama ya kalli Ammar yace " haqiqa na jima ina aikata abubuwa da nikaina ayau nayi Allah wadai dasu, sai dai inafata hakan bazai shafi 'ya ta ba, kuma ina me neman afuwarka dan Allah "

   Ya qarashi game da had'e hannayensa biyu.

   Cikin girmamawa Ammar yace " haba ,kai tamkar uba kake a wajena, ko iyalanka basu had'a mu ba to tabbas ka haifine kuma ka zama uba a wajena, dan haka duk abinda ya faru jarrabawace, kuma bakomi nidai bakamin komiba"

  Sosai kowa yaji dad'in kalamansa musamman Mansur, da jiyake kamar ya nutsi a qasa, sai dai wani fanni yana godewa Allah ta sanadin hakan mahaifinsu ya gane kuskurensa .

  Bayan 'yan hirar rakin da suka ta'ba nan Ammar ya gabatar da Mansur amatsayin wanda zai masa wakilci akan maganar Zuhailat.

  Kuma mahaifin ya amince, kowa yai murna da haka, yanzu dai idan jikin Malam Audu ya dad'a qwari za'azo ayi magana tsakanin manya.




           %

Latifa kam satin ta guda cif da komawa gidan ta fahimce lallai gidan yafi qarfin ta, dan rayuwa take a gidan tamkar jaka, gashi bata isa tace zatai wani yin k'urin nemawa kanta 'yanci ba, dan kowa matan gidan ma kad'ai sun isheta balle yaran gidan.

   Kowa tsula tafiyarsa yake San ransu, idan kwa tayi girki sai suce "su Sam be musuba" kuma haka zata sakya wani iya shegen dai kala-kala ba wanda basa mata, kuma bata isa ta tankaba.




          %

Tunda suka kaiwa Abdallah ziyara komi nata ya kwancemata, kwana biyun nan Kawai tunani take akan wannan al'amari nasa.

   Batare da sanin kowaba ta kaiwa likitan dake kula dashi ziyara, inda anan ya tabbatar mata da cewa " lallai indai har anaso ya dawo normal to sai yayi rayuwa da ita waje d'aya, wato dai sai sun zauna tare ."

     Wannan zancen ya mugun tasa mata da hankali sosai dolane tai wani abun.



     Shiri tai Na musamman, duk da batta da tabbaci akan hakan amma tasan dai dole ita zata tinkara da zancan ta fahimce ta.

   Batare da sanin kowa ba ta ziyarci gidan Hajiyar Na'ima, bayan sun gaisane ta ke isar mata da saqon zuciyarta.

  Hajiya ta nisa kana tace " hakane Fatima banqi ta takiba dan nima najima ina wannan tunanin, tabbas ya kamata ace komi ya wuce, amma mutum d'aya nake tunani akan lamarin kawunki"

   Sunkuyar da kanta tai kana tace " Hajiya banaso Kawu yasan da zancan inaso kiyi magana da mahaifina nasan shi zai fahimce maganar mu"

    " To Fatima duk yadda kikace, amma kinsan san shi ba mazauni ba ne ba ko??"

    "Ehh ba ina nufin kije ki sameshi ba, dan yanzu tafiya canma zai iya sawa au fahimci shirinmu, zan baki lambarsa sai kuyi magana ta waya, nasan zai fahimcemu"

   " To duk yadda kika ce"

Sai da tayi magrib sannan ta koma gida, dan yanzu zamanta Na gidan su Dr.Sai dai jefe-jefe takan ziyarci iyalan su Hisham, da kuma Hajiyar Na'ima.

 
         %

Masha Allah jikin Malam Audu yayi sauqi dan yanzu ba abinda baya iya yi da kansa, hakan yasa suma malaman asibitin suka bashi sallama.

Daman tun a asibiti ya aikawa da Tabawa takardar ta, shiyasa suma koda suka dawo basu tadda ta.

   Bayan fitowarsa da kwana hud'u Malam Haladu ya taryeshi da batun nemawa Ammar aure kamar yadda Ammar d'in ya buqata.

  Nan suka shirya suka je kamar yadda ya buqata , alhmdulillah komi yazo da sauqi inda kuma shi mahaifin nata ya bashi, wata biyu kawai aka saka.


          %

Lamarin Latifa fa ba sauqi dan yanzu haka jinya take, bata iya komi, amma a haka za a sanyata aiki koda da Jan ciki zatayi.

  A halin yanzu mafita Kawai take nema, wayar da zata iya Kira da itama mugun mutumin ya k'wace ta.



           %

Bash kuwa duniyarsa Kawai yake ci da tsinke, Sam ya manta da lamarin wata Latifa .

   Kwankila suka tsara shi da wata friend nasa, inda ya zuba naira miliyan uku, Wanda suma da danfarar sa ya samuso.

   Saidai a binda bai sani ba , ya bawa Kura ajjiya ne, dan kuwa yarinyar ta dad'e tana tarming d'in shi na yadda zata tagayyarashi.



    Ranar da kayan zasu iso a ranar yarinyar da cire duk wani sim nata ta kulle duk wata hanyar da zata sadashi da ita ta cale abinta.

A ranar tamkar mahaukaci ya koma, wanda sanadinbtuqin gangancin da yake yasamu hatsari a kan hanyarsa, nan aka wuce dashi emergency cikin gaggawa.

       
        %

Kamar yadda suka tsara da Hajiya, aikuwa ta kirashi cikin fahimta da nutsuwa take tura biqatarsu izuwa gareshi.

   Sai da ya sauke nunfashi, tunanin irin halin da mahaifiyarsa take ciki ga kuma d'an nata da take tunqawo dashi shima ba lafiya.

   " Na amince Hajiya duk abinda kuka yanke yayimin dai-dai, nasan bazaki ta'ba cutar da 'yata ba, batun yusif kuma kibarmin komi a hannuna"

  
   Cikin Jin dad'in kalamansa tace " nagode, Allah ya sa mudace "

  " Ameen " yace.

" Ina tunanin nan da sati biyu lamarin ya kasance ko, tunda kaga ita ba idda ce akanta ba?"

Inji Hajiya.

 
   "Ehh hakan ma yayi, Allah ya tabbatar da alkhairi"

    A tare suma amsa da "AMEEEN"



     Bayan sunyi sallama ta Kira Fatima ta sanar da ita yadda sukai da mahaifin nata.

   Sosai taji dad'i samun biyan buqatar tata, koba komi shima ya samu 'yanci.






   Vote, Share and Comment...........


*Real Mai_K'osai*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now