Part......65&66

29 2 0
                                    

   *ZAFAFA WRITERS FORUM*
            Z.W.F..........



         ________BUTULU_______

         NA
MARYAM ABDUL-AZIZ.
   (MAI_K'OSAI)





Page.....65%66

Bisimillahir Rahmanir Raheem.





____________Kamar yadda Hajiyar Na'ima tace "zasu tattauna" hakan ne ya faru.

    Sai dai shikam Daddy ko ajikin sa duk ance masa d'an nasa na cikin wani hali, amma shi kam yace" koma menene shi ya jawa kansa, hak'k'in yarinyar mutanene ya soma cinsa"

  Ba yadda su Ammi basuyi ba su shawo kansa dan ya shiga cikin batun amma yace" Sam shi a'a".

   Haka suka k'yaleshi, amma su sunyi alqawarin tallatawa Abdallah duk cikin ya nayin da yake ciki.

   Sun shirya akan zasu ziyarci asibitin da yake kwancen Dan dubashi, duk da dai Sabeer ya shaida musu cewa" ba'a barin kowa ya shiga d'akin ,dan ba'aso hayaniya ta masa yawa".




        %

Kasuwanci kam ta fannin Ammar ba'a cewa komi sai dai godiyar ubangiji , gidan da sukai niyyar canzawa mahaifiyar tasu shi suka je Yau suka duba, abinda be musu ba zasu sauya.

Masha Allah gidan yayi duk da ba wani babba ne sosai ba amma dai a wadace gidan ya ishi mutum zaman rayuwa.

  Koda suka kaita ta gano gidan har kuka Saida tai, bata ta'ba haihuwa ba, yau 'ya'yansa wasu sanadin riqe sun da tai sun maye mata gurbin 'ya'yansa da bata samu ba, sun mata abin bata ta'ba zato ba, tana matuqar alfahri da su matuk'a.



   

          %

Satin Hisham yanzu biyu da tafiya ,kullum suna nanuk'e da juna, kodai ta waya ko kuma ta WhatsApp ana video call.

  Kullum burin Fatima ace yau Hisham d'in ta ya dawo, dan tabbas da da yadda zatai to da ta dawo dashi gareta.

   Satin ta d'aya a gidan su Hisham d'in ta koma, Na'ima ce me mata sintirin kai ziyara, duk da cewar su Saliha na gidan.

   Yau tunda tashi take Jin jikin ta ba dad'i, waya suke da Hisham amma Sam takasa samun nutsuwar ta, ita dai Kawai tana Jin ba dad'i ,tana Jin kamar wani abu na shirin kusantarta mara dad'i.

   Koda ya fahimce hakan nan ya shiga qoqarin ganin cewa" hankalin ta ya kwanta" duk da cewar batare suke ba amma Saida ya qoqarta wajen ganin ta sake ranta kan suyi sallama.


        %

Su Hajiya da Ammi sunje duba Abdallah ,inda suka tadda jiki kam ba dad'i ,in Banda surutai ba abinda yakeyi, wannan dalilin yasa har sai an masa allurar bacci sannan ake samun shirin bakinsa.

   Sosai suka tausaya mai, tabbas abu d'aya ne zaisa Abdallah cikin nutsuwa saidai kuma abun nan ya masa nisa, sukam basu San ya zasuyi, amma dai suna mai fatan samun lfiya mai d'orewa.

   Saida suka kuma zan tawa da likitan, inda dai ya kuma basu wasu 'yan shawarwari, da kuma inda samuwar kawo mai abinda yake so din.

   Sun jinjina lamarin dan sun San tabbas wannan bame yiwuwa bane, da haka suka baro asibitin.

   Sabeer kam iya shiga damuwa ya shiga dan shidai kam a yanzu burinsa be wuce ace abokin nasa ya tashi wasai ba , to amma "tayaya?" Itace tambayar da kullum yakewa kansa, kullum burinsa samowa Abdallah mafita amma duk inda ya 'bulla to a toshe take.





             BUTULU.....Where stories live. Discover now