part.....12

125 6 0
                                    

〰〰〰
*BUTULU*
〰〰〰

Story...writing by
*Maryam Abduul*
  
Wattpad @maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS.💫*

We are here to make you happy.....smile and educated to realized that we are the best among all
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*💃💃💃

*Marubuciyar:
   *BIYAYYA*

   
*page....12*

*BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

.........Tafiyar ya Abdallah yasa mamina duk tazama wani iri ga aiki da tasa kanta sai tayi wai tafison tadinga motsa jikinta, ga rashin abokin hira danma takan je wajen Granny tana rage da zaman kad'aice.Abbana kuwa tafiye-tafiye yakeyi sosai dan yanzu bai samun zama awaje d'aya.

Ahaka har cikin mami yakai wata tara amma bazancan haihuwa domin jikake shiru, wasa-wasa har cikin mamina yakai wata goma sha d'aya da sati d'aya cikin wani dare tafara wata wahalalliyar naquda gaba d'aya tafita hayyacinta sosai.cikin abinda baifi mintinaba.

Asibiti suka nufa kaitsaye babban likitan datake gani ya amshesu dan dama yace" shi zai amshi haihuwarta" dan ko kafin nan sun jajje wajensa ganin cikin ya haura lokacinsa, shi yadinga kwantar masu da hankali.

Tsawon awa hud'u ana abu d'aya gaba d'aya mamina tafita daga hayyacinta, ganin halin dasuke cikine yasa yasa Abba na sanya hannu dan amata C.S domin cetan rayuwankan biyu.

Basufi awa uku da shigaba likitan yafito, nan ya shaidawa su Abbana" ansami nasarar fito da d'an, amma uwar babyn tana buqatar hutu saidai tana neman mutum d'aya ". Koba fad'a musuba sunsan watake da buqatar gani haka Abbana yashiga nan ya taddata cikin wani hali domin ko ina na jikinta na'urane asaqale da ita harta da nunfashi da temakon Allah da oxgyen take fitarwa ta shaqa wannan halin datake ciki yasa jikin abbana mugun yun sanyi.

Ahankali yaqarasa bakin gadin datake kai, hannunsa yazira cikin nata ahankali, takyakwa ta kamashi tare damai wata damqa, ganin hakan yasa Abbana shafa kanta batare da yace uffanba.

Kallonshi tai cikin dasasshiyar murya qacce bata fita tace" kayi haquri Mahmuda dani nasan nasa'ba koda sau d'aya ne, kayi haquri da duk wani abu dana ta'ba ma dan Allah karkayi fushi dani, ga 'yatanan ka kulamin da ita kabata kulawa dai-dai gwargwado kada kabari ta wulaqanta, nabawa Abdallah ita inaso kacikan wannan burin inhar yanasonta ka aura mai ita, kar kabari tayi kuka dan rashina ko dan wani abun"

Damqe hannunta yai da qarfi yace" meye haka Maimunatu haba, meyakawo wannan maganar kar nasakyaji kinji ko koma menen ni na yafemiki, kuma 'yarmu na tare damu zamu bata kulawa nidake"

Kallonshi tayi cike da tausayawa duk da batason ya mutuwa takeba amma tanaji kamar itan zatai, tanaji kamar wannan ne ganinta dashi na qarshe, cikin dashewar murya tace" a'a Abban yara ko kad'an rayuwarmu kad'ance inaji......" bata kaiga ayaba wani tari ya sarqeta, gani n hakan yasashi fita da sauri dan kirawo likitan,

Atare suka dawo yadda likitan yaga jikin nata duk ya rikice yasashi fitar da Abbana waje dan aduba mamina, nanfa akashiga qoqarin tallafamata, saidai duk da wannan qoqarin nasu hakan baisamuba dominkwa mamina takye tai kalmar shahada rai yai halinsa.

Ganin hakan yasasu jamata mayafi suka lullubeta, Abbana dake tsaye bakin qofa takya yaji qirjinshi ya buga ai bai wata-wataba ya fad'a d'akin yayi dai-dai da kai mayafin fuskar mamina, a 360yaqarasa bakin gadon hannun likitan ya riqe yana girgiza kai.

Sai daddy da Granny dake tsaye suna ganin Abbana ya fad'a d'akin jikinsu yai sanyi nan suma suka mara masa baya.

Nanfa likitan yashiga basu haquri domin kwa tarigamu gidan gaskiya, "Allahu akbar, lallai duk mai rai mamacine" gani kawai sukai Abbana ya fad'i qasa sume bakinsa na ambatan sunan mamina, ganin hakan likitan yasa aka d'aukeahi aka bashi d'aki guda dan bashi kulawa.

             BUTULU.....जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें