Part.....18

93 3 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
    *Maryam Abduul*
   

Wattpad@maryamad856.

💫*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
    *BIYAYYA*

*Part.....18*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

....................Yana fita kam yasamo yaro, nan suka shigo tare da kamamai daya daga cikin tumakan.

Koda yaje sosai aka siyesu da daraja, yana karbar kudin ya wuce kasuwa shinkafa ya aunu musu mudu biyu sai wake gwangwani biyar sannan ya dawo gidan.

Cikin fara'a ta tar'beshi tare damai sannu da zuwa, shima cikin fara'a ya amsa.nan yabata abinda yasiyo sosai taji dad'in hakan takuma yi matuqar farin ciki gashi yanzu suma zasu d'ora tukunya awuta.


Bayan kwana biyu.

Kamar yadda sukai maganar kasuwance da malam sai dai hakan baisamuba sa'banin jin shirun datai ba alamar zai yiwata sana'ar hakan tasa tun kararsa da maganar.

Yana zaune yana alwala, fitowarta daga daki kenan ganin zaune yasata matsawa kusa dashi tace" yawwa malam ashe baka fitaba daman inaso me wata magana amma inaga in kadawo zaifi ko dan naga kamar masallaci zaka"

Ya kalleta kallo d'aya kan ya kauda kansa kana yace" wace magance kuma haka, wai ke Suwaiba bakaya tsirar abu sai kinga mutum yana wani abun, tun dazu ina zaune bakice zakiyi maganaba sai yanzu da zan fita, to fita zanyi kuma bayanzu zan dawoba dan haka sai ke zauna zaman jira kinji ko"

Suwaiba tai murmushi kan tace" Allah ya huce zuciyarka to malam meye kuma natada jijiyoyin wuya, ai ba matsala maganar ba ca'akai dole sai yanzuba, fatana dai Allah yadawo dakai lafiya"

"Ke kika sani dai" yaqarasa tare da ficewa daga  gidan. Itakam girgiza kai kawai takeyi wannan al'amari nasa yana matuqar bata tsoro da mamaki.

Shikam yana fita masallaci yazarce, bayan sun idar da sallah ne ya wuce wajen wata bazawararsa da yadad'e yana son ya aureta amma talauci ya hanashi yin hakan, kwanakima da yaje saida sukai fad'a sosai, akan "indai ba aurene ya kawoahiba to qar yaqara zuwa inda take, kuma da zarar tasami wani zata aureshi" duk kuwa da irin son da takewa malam d'in.

Shi kuma jin hakan yasa hankalimsa mugun tashi, yanaji inbai aurtaba kamar zai rasa rayuwarsane, to yanzu gashi dama tasamu shine yadawo.

Koda tafiti ganinsa yasata fad'ad'a fuskarta, tasan ba shakka yasamu mafita shiyasama tamai hakan tunda tasan yana mutuwar santa.

Bayan sun gaisane yake shaida mata" yasamu kudin sadakin nata dan haka yanzu yanaso ta tsaida musu da rana"

Dariya tai kan tace" yayi nawan shiyasa nake matuqar sanka wllh, ai daman nasan bazaka bari wani ya autenba, yanzu bagashi danama hakaba ga je kasamu mana mafita, yanzu abinda za'ai kawai nan da sati daya sai ayi abun ko ya kagani?"

Ya bud'e baki tare da fad'in " ah hakan yayi shiyasa nakesonki akwai ja wllh, ai ni duk abinda kika yanke shine dai-dai yanzu zanje nafara shirye-shiryen biki da inda zaki zauna"

Cikin sauri tace" a'a nifa basai anyi wani bikiba abinka da ba yaraba, kawai dai adaura aure akaini gidanka shine kawai fatana"

"A'a bazai yiwuba in ni banyiba aike kyayi, yanzu dai ga wannan kiyi abinda zaki dasu" ya qarasa yan lissafimata kudi tare da miqamata.

Zare ido tai kan tace" malam ina kasamo wannan ku d'ad'e haka masu uban yawa?"

Murmushi yai yace" wannan ma ai kadan kika gani, zuwanai na amso wata gonata data ragemin shine nasata akasuwa, to kuma Allah yasanya mata albarka"

Matar tace" au to koda naji, Allah dai yakaimu wannan rana"

Ya amsa da" ameen" koda zai tafi sai da ya miqa mata leda mai d'auke da tsire aciki da kuma madarar shanu.





************
.............Granny ce zaune afalo dan yanzun an sallamo su daga asibitin, sai alokacin aunty zubaida ta shigo tare da durqusawa tana gaidata.

Granny kam batare data qullacetaba yasata amsawa, sai dai fuskarta ba annuri ko kad'an, kallonta tai kan tace" Zubaida inaso kisan rayuwa kisane cewa Allah baya bacci duk abinda d'an adam keyi ti yana kallonsa, meyasa kike d'ora wa kanki halayen da basu dace dakeba, dan Allah zubaida ki canza hali, banayimiki wannan maganar bane wai ko dan bakeje kinyi jinyataba a'a nayi miki dan gaba bakison ya rayuwa zata kayaba"

Turo baki tai kan tace" insha Allahu ma zatai kyau, kedai kiyi fatan Allah yaqara miki lafiya ma"

Wannan maganar datai sai ya mugun 'batawa Granny rai, amma ba yadda zatai haka ta qyaleta tare da fatan yimata samun shiriya daga wajen Allah.

Saliha kam har kuka saida tai, meyasa Allah ya jarabcesu da wannan uwa haka, sam bata da ilimin addini bata da tausayi da kuma jin qan mutane, meyasa take da baqar aqida da rashin imani?, ya Allah ka gyara mana uwar nan tamu"

Lallashin Granny tashiga yi dan tasan ba shakka Granny tashaqa amma bazata ta'ba nunawa ba koda Abba yadawo ma dadare bata sanar dashi halin da suke cikiba.

Shikam daman Abba yagaji sosai da halin aunty zubaida kawai ba yadda zaiyine, yanason daukar mataki akanta amma sai Granny ta hana, to mema zaiyi tunda shi dai ma muharramintaba, ba mijintaba balle yace zai yankemata hukuncin saki ko akasin hakan, hakan yasa yatattara duk wani maqaman yaqinsa yajefar, badan yasoba.

Itakam tata rashin mutuncinta take iya san ranta, girki kam wannan battayi tare da Granny, inkaga taci abinci to tabbas Saliha ce ta girka, ko magana akamata sai tace"bata girkaba.

Ihsan kam yanzu wani saurayine yaketa mata naci, school dinsu d'aya, sai dai ita ko kadan batta sonshi, haka yasa take masa wulaqaanci kala-kala.

Shikam ganin haka yasashi rabuwa da ita dan kwa aganinsa ba wani abu zata bashiba kuma ba itace kadai mace aduniya ba balle yace in ba ita bazaiyi aurenba, hakan yasa ya tattarata yawtsar, sa'banin da dayake mata naci kullum yana hanyar wajen datake wala gida ko amakaranta.

Sau tari Saliha kan mata nasiha akan wannan wulaqancin datakewa mane manta, amma saidai tashiga ta kunne d'aya, tafita ta d'aya kunnen.

Qarshema saida sukai fad'a sosai akan hakan, wanda har saida aunty zubaida taciwa Saliha mutunci.ganin hakan yasa Saliha zuba musu ido taga abinda hali zaiyi.



*******
" Fatima meyasa zakiyi hakane wai, meyasa bazaki karbi soyayyar amininaba wllh na rantse miki bazai ta'ba cutar dake dan Allah ki amshe tayin soyayyarsa kada ki jefashi cikin wani hali" dr.Auwal ke wannan maganar cike da tausayawa aminin nasa.

Cikin kuka Fatima tace" kayi haquri dan Allah babban yaya, banyi haka dan watsama qasa a idoba, banyi hakaba dan bata maka rai ba, dan Allah ka gafarceni, amma zuciyata tayi rauni bazata iya amsar soyayyar wani a yanzu ba dan Allah kada kace zaka tursasani yin abinda banason shi "

Jin hakan yasa zuciyar dr.Auwal tafasa danme zata dinga yimai haka, meyasa bazata sawa kanta haquri da juriya akan yasa meta meyasa zata dinga wahalar da zuciyar bawan Allah?"

Cikin qonan rai ya furta" shikkenan Fatima bazan mike doleba insha Allahu daga yau bazan sake tun kararki da wannan maganar ba amma kisani kowanne bawa yana tare da tashi jarrabawar, kuma Allah yana alfahati da bawan da yayi tawakkali ya kuma amsheta hannu bibbiyu, daga haka zance ki huta lafiya" yana gama fad'a ya bar wajen.

Fatima kam zuciyarta tayi qona Sosai, lallai ba shakka bataso bata ran dr.Aiwal ba amma meyasa zuciyarta takasa amsar abokinsa meyasa, ita tasan tana tsorone akan abinda zaije yadawo wannan dalilin yasa take tsorin qara karbar wata soyayyar"

Miqewa tai tashige dakin ta gaba d'aya qwaqwalwarta ta toshe da tunani, yanzu yazatai da wannan al'amari.

Wajen Na'ima ma abindai ba sauqi dan kullum wutar son dr.Auwal qara ruruwa take acikin zuciyarta.

Danma Hajiya nayawan bata shawarwari da kuma kwantar mata da hankali.wannan yasa takejin d'an sauqi-sauqi acikin zuciyar tata.

Editing is not allow......

Vote,
Comment,
Share and Like......

*Mrs.Abduul ce*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now