BUTULU... part 33

57 2 0
                                    

💫 *DA BAZAR-MU WRITER'S ASSOCIATION*💫

     We are here to make happy......smile and educated to realized that we are the best among all....... *DA BAZAR-MU MUKE TUNQAHO*💃💃💃💃💃💃

                     *BUTULU*

By
   *Maryam Abduul*

  *Wattpad@Maryamad856*
  *Facebook@Maryam Abduul*
*Instagram@Maryamad53*


*Masoyiya tagari abar alfahari bazamu ta'ba mantawa dake ba har abadan abada.....Allah yasa aljanna makomarki ya miki gafara .... *Habieberty* Allah yasa kin huta.....ameen thumma ameen.

*Part.......33*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

      *****************Tana ajjiye wayar ta sauke ajiyar nunfashi tare da juyawa inda daddy yake kallonshi tai cikin fara'a kana tace" sorry sir baya jin dad'ine bazai iya fitowa ba amma yace" inba damuwa abaka address nasa ka sameshi agida"

   Shiru yai na d'an wani lokaci kan yace" ok ba matsala bani"

   Nan ta d'au complement nasa tabashi, tare da yin sallama.

Daddy kam koda ya fita tunani yakeyi yaje yanzu ko kuwa? Rashin samun amsane yasashi shigewa motarsa ya bata wuta sai gida.


   Abdallah kam yinwace keta ad-dabarsa hakan da yaga bazai iya jurewa bane yasashi d'aukar key d'in motar sa yafice a gidan.

   Kai tsaye gidan sa babbin iyayensa.yana shigavya tadda baba zaune tana jin radio, yanayin da ya gaidata tasan lallai yana cikin damuwa, sai dai bata da ikon tambayarshi dan batin yauba ta lura shid'in mai 'boye damuwarsa ne, yana da zurfin ciki sosai.

    Abinci da ruwa ta kawo mai sai lemo, kamar kwa tasan abinda ya kawoahi gidan kenan.ko minti uku batai da ajjiyewa ba ya bud'e flet d'in ya fara ci tare da bisimillah.

  


  ...............Wajen Ammar kuwa koda ya fita samin wajeyai ya had'a kansa gwiwa " tabbas lallai an kassarashi sosai, yanzu ta ina zai soma had'a wasu kayan, gashima kasuwar tasa ta tsaya cak"

Miqewa yai tare da nufar gidansu Affa tabbas dolane ya sanar da ita halin da ake ciki, in ba haka ba shi kansa bazai sami wani sauqi daga zafin dayake jiba.




   *********Wata tsaleliyar mota ce tashigo haravar gidansu Mansur kai da ganin motar kasan ta manyace.

   Baifi minina biyu tsakani ba mamansu ta fito fuskarta cike da farin ciki , yalwataccen mirmushi tasake lokacin da tai ido biyi da fuskar mijin nata.

  Dattiji ne mai kimanin shekaru 52 sai dai ko kad'an b zakace yakai wannan shekarun ba sabida yanayin fatarsa da ta nuna samun wadataccen jin dad'i.

  Fuskar sa d'auke da murmushi shima cikin farin ciki yace" oyoyo my uwar gida" ya qarasa yana mai qarasawa inda take.

   Cikin farin ciki tace" oyoyo ya hanya??"

A sanyaye yace" haba wai ke bakya girma ne anan za'amin sannu da zuwan???"

Murmusawa tai kan tace" tuba nake muje ciki ko yalla'bai"

" Yawwa ko kefa" ya fad'a cike da fara'a.

Suna shiga yakam kalle-kalle kamar baqo a gidan " ah yanaga kamar ke kad'aice agidan ina yaran nawa, ba wanda yazo tar'ba??"

  Murmusawa tai kan tace" ni kad'aice na aikesu ba zasu dad'eba, ni dai muje ka watsa ruwa ka bawa ciki haqqinsa"

             BUTULU.....Where stories live. Discover now