part....16

89 5 0
                                    

*BUTULU*

Writing by
*Maryam Abduul*

Wattpad@maryamad856.

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*💫

*DAGA MARUBUCIYAR:-*
*BIYAYYA*

*Part.....16*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

.............Hajiya ta gyara zamanta kan tace" wayeshi hakan Na'ima da kike matuqar so haka?"

Na'ima tace" dr.Auwal, shine mutumin da zuciyata take matuqar so, hajiya yazanyi?"

Hajiya ta sauke ajjiyar zuciya tabbas taji dadin kalaman diyarta ta sai dai bata ganin itama zata ci ribar hakan, tunda dai ahi dr.Auwal d'in baice yana sonta ba hasalima tana ganin kamar auren bai da me shiba tunda ai shi d'in ba yaro bane.

Kallon Na'ima tai kan tace" tabbas wannan jarrabawa ce mai wuyar cinyuwa amma inaso ki miqa komi naki ga mahaliccin ki tabbas zai mike maganin duk matsalar ki, sannan kada ki kuskura kiyi abinda zai fahimce soyayyarsa gareki dan d'a na miji ba ba d'an goyi bane, duk kirkin da kuke dashi zai iya rufe ido yamike rashin muctunci, zaki koma abar wulaqantawa gareshi inaso dan Allah ki boye soayyarki garesa dan Allah kinji"

Sauke ajjiyar zuciya tai kan tace " shikkenan hajiya na mike alqawari ba kuma zaki sami sa'bawata daga gareniba insha Allahu zan cigaba da addu'a kamar yadda kikace"

Hajiya tace" yawwa 'yata nima zan cigaba da mike addu'a insha Allahu, yanzu ki tashi kiyi sallah har likacinta na neman fita"

Na'ima ta amsa da" to". Nan hajiya ta fita tare da jinjina wannan al'amari acikin ranta.



********
Tunda ta tashi taji bata sha'awar komi sai illa taje gidan Abdallah taga halin dayake ciki, duk da tasan zuwan nata bawani abin ariziqi zai anfanar ba amma tayi alqawarin zuwa kodan gulmar datake cinta, dan taji labarin yayi aure.

Hajiya taiwa sallam akan zata wajen Fatima, jin hakan yasa bata hanata ba, taso taje da Basma amma kuma batason tafiya da ita dan tasan ba inda tace zata zataba.

Tana shiga gidan ta taddashi kaca-kaca ba alamar shara, hakan ya tabbatar mata da cewa" lallai matar gidan qazamace"

Yana zaune akan daya daga cikin kujerun falon yana game a laptop dinshi, dan ransa amatuqar 'bace yake, domin fad'a sukai sosai da Latifa akan tsabtar hidan, ita kwa tace" ba shara da aikine yakawota gidanba"

Hakan yasa yiwa Bala p.a dinsa waya akan yanaso asa mumasa mai shara da aikin gida amma na miji ba maceba, bayan sun gama wayarne ya dawo falon ya hau game.

Jin sallama da muryar mace yasashi d'ago kansa daga kan laptop d'in, ganin Na'ima tsaye a tsakiyar falon yasashi kauda kansa gefe.

Takowa tai tare ta matsowa daf dashi ta tsaya batare da ta furta koda kalma d'aya ba.

Hakan yasashi d'ago kansa ya kalleta kan yace" lafiya dai ko?"

Murmushi tai mai fidda sauti kan tace" lafiya lau, kamar yadda na ganka cikin nishad'i da annushuwa"

Wani kallo ya watsa mata kan yace" tunda kin ganni cikin hakan meyasa sai kinzo duba lafiyata ai saiki qara gaba ko"

Na'ima tai qayataccen murmushi kan tace" nazo nayima Allah yasanya alkhairi ne naji ance kayi aure ka auren 'yar hamshaqin mutum wacce ta isa mace wacce zata baka duk wani abu da kakeso sa'banin matarka ta baya, sai dai kuma ina shigowa gidan naga banbanci dan yadda nai hasashen ta sai naga yawuce haka ma ashe muhwar tsaftatacciya ce" ta qarasa tare da sakin wani had'ad'd'an murmushi.

             BUTULU.....On viuen les histories. Descobreix ara