Butulu....part...45/46

37 2 0
                                    

              *BUTULU........*


by
          Maryam Abdoul

                 *Me  Qosai*


Wattpad @Maryamad856.


Part.....45/46.


Typing..........


    ..................Murna ake sosai tsankanin Fatima ,daddy da kuma sauran mutunen dasuke ke waye dasu.

         Wayarshi ya zaro ya danna layin Saliha, kamar wacca take jiran kiran sa, Dan ko bugu dayan batabari ya gama isaba ta d'aga.

         "Daddy anga Aunty Fatiman kuwa?" shine kalmarta ta farko da tamasa.

             Da yake a handsfree yasa  ba Wanda  beji abinda taceba, "daddy plz Kayi shiru,dan Allah kada ka bari........"

 
         Cak maganarta ta tsaya sakamakon jiyo sautin Fatima da tai, kan wayar.

           "Qanwata" shine abinda Kawai tace.

         Cikin sauri da zaquwa tace" Yayata kice da gaske, ina kika shiga munata nemanki kowa ya damu, Abba ,granny duk suna d'okin ganinki"

       Murmushi Fatiman tai Jin yadda take ta zubo magana.

      "Ba inda naje Saliha nima nayi kewarku sosai ,ina granny take?" Ta tamvayeta.

       Katse wayartai ba tare da ta basu amsa ba, da gudu tai part d'in granny tana qwala mata kira.

        "Kedai kin shigangad'a menaci kuma yanzu?"

          Bata bata amsa ba tahau danna video call, tana shiga suka d'aga wayar ta saitawa granny ba zato ba tsammani granny tai arba da fuskar da suka dad'e suna d'okin ganinta, "Fatima" granny ta anbata cikin sanyin murya.

           "Granny ta" itama Fatiman ta fad'a cike da d'okin ganin kakartata,murmushi dukkansu sukai, kan granny ta d'ora da fad'in "Fatima ashe zan kuma ganinki kan na tafi, Ashe zamu kuma sakya ganin juna, meyasa kikayi nesa damu"

           Cikin kuka Fatima tace "nima ba'ason raina bane Granny ,Na dawo kuma zamu kasance har qarshen RAYUWA tare da juna, ina nan gareku bada dad'ewaba" ta qarasa tana goge qwallar data zub'o mata.


   Nan suka shiga murnar sakya ganin juna a karo Na biyu, har sai da kudin wayar suka qare sannan suka haqura da juna.


   Kowa Yau a gidan murna ya keyi, Sanda Aunty Zubaida taji labari murna d'aya Kawai tayi shine zata ga d'an ta ,kuma ba makawa sai ta raba wannan qaddararren auren dake tsakanin waccan shegiyar da d'an ta.


  Su granny kuwa kasa haquri sukai har sai da Daddy yasa aka yankar musu visa  ta tawowa garin Kano, Dan since bazasu iya haqurin zuwanta garesuba.




********
    Ammar kuwa tafiya ta kama Yau insha Allahu duk wani kayan SA da ya San zai buqata sai da ya deba a bakko din sa.

   Yana ji ya na gani yayiwa mahaifiyarta tasa sallam, duk da beso barin ta cikin halin da suke ciki ba amma qwarin gwaiwar ta shi ya qara qarfafa mai qwiwa.

  Kuma insha Allahu zai maida hankali akan abinda yasa gaba.


   Koda ya Isa tasha  kamar yadda yace "Kano" zai nufa Allah ya temakeshi yana zuwa motar Kano na cika, da qyar suka yarda suka sashi a maleji, a haka suka dauko hanyar Kano zuciyata sa cike da kewar qauyensu.




*Me   Qosai.........*

             BUTULU.....Where stories live. Discover now