BUTULU... part 34

82 7 3
                                    

💫  *DA BAZAR-MU WRITER'S ASSOCIATION*  💫

      We are here to make you happy .....smile and educated to realized that we are the best among all...... *DA BAZAR-MU MUKE TUNQAHO*💃💃💃💃

          
                        *BUTULU*

*By Maryam Abduul*
    *Wattpad@Maryamad856*
    

             *Marubuciyar  BIYAYYA*
   
   
*Part.....34*


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


************Sai da yai sallar azahar sannan ya nufo hanyar gida, bakin tito yasamu yai parkinga tunabi yake kawai pal cikin zuciyarsa baisan yanzu kuma wace wai nar zaije ya gani ba balle ya tuyata.

  Saida ya shafe rabin awa sannan ya ja mitar tasa ya bar wajen.yana isa ya tadda mota a parking space "waye wannan to, ko kuma Sabir ne may be ma" da wannan tunanin ya qarasa cikin falon gidan agajiye.

  Saida ya dan zauna na minti biyi sannan mai gadin gidan ya shigo yake sanar mai da cewa yayi baqo yana falon baqi ya d'an jima ma yana jiransa.

  Shi harga Allah yama manta da wani batun yace" abada address na gidansa, wai waye wannan yake son su had'u haka da zai uzzuramai??"

  Har ya bud'e baki zaice" ace masa ba yauba, sai kuma ya danyi jim na yabada izinin ace gashinan"

  Yana fita mai gadin shima ya mara masa baya, qofar falon ya tura zaune yake yana latsa sysytem nashi, fargaba da tsoro ya baibayeshi take ya fara ganin kammanin dadsynsa da yasa, ji yai zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri.

  Bai yi gigin qarasawa ba, ganin inuwar mutum tsaye akansa yasashi d'agowa dan kallon wanda ya shigo.

  Ido cikin ido sukai ido hud'u da juna, mamaki ne yasa daddy saurin janye laptop din nasa daga gabansa, saidai kuma komi ya tuna oho naga yayi saurin mazewa kamar baisan waye ba ke tsaye.

  "Qaraso mana yalla'bai" daddy ya fad'a cike da murmusawa.

    Ba yadda ya iya haka ya tattako kamar mai koyan tata ya qarasa, cikin qarfin hali ya bud'e baki zai magana daddy yai saurin dakatar dashi ta hanyar fadi'in" daman inaso nasan waye nake mu'amala dashi wajen kasuwancina wannan ne kai dalilin da yasa natako har gidan ka, sai dai kuma gashi zuwane yabyayemin wata matsala da na dad'e ina fama da ita"

   Ya nisa ya d'ora da fad'in " magana ta farko akan kasiwanci ne ina tunanin mu ajjiyeshi gefe, magana ta biyu kuma maganace akan 'yata daka d'auke tsawon shekaru muna nemanta, yanzu inaso kamin iao da ita zan tafi da ita dan sama mata 'ingantacciyar rayuwa"

   Wata muguwar zuface ta tasomata jiyake inama wannan rana bata zoba inama baice" abada address d'in nasaba" yanzu ya zaiyi sam baisan ina zaiga Fatima ba balle ya badata  ga daddy yazaiyi"

   Ganin hakan yasa daddy kallon shi cikin kakkausar murya yace" bazan shiga gidanka sabida ni nasan darajar gidan aure, amma inaso ka fidso min da 'yata yanzun nan ba tare da 'bata lokaci ba"

  Cikin in-ina yace" daddy kayi haquri ka bani lokaci zamuyi magana amma yanzu ka zauna ka dan ci wani abun mana amatsayinka na ma'aikaci da kazo akan harqalla"

  Daddy ya girgiza kai dan ya lura abinda yakeyi kamar mara gaskiya, cikin sanyin murya yace" niba daddyn ka bane, sannan kuma bana yawo da yinwa duk inda zanje sai na baiwa cikina haqqinsa, na jima ina zargin wani abu akan company d'in inaji kamar nasan mai shi sai dai ina kokwanto, hakan yasa na shiga harqallar sai kuma akayi dace hasashena yazama gaskiya"

  "Kasani cewa " abinda ya kawoni nan neman 'yata bawai kasuwanci ba" dan haka inaso ka fiddo min da 'yata yanzu nan ko ranka ya nugun 'baci".





   **********Zaune suke gabansu tulin kayan marmarine , Zuhailat ce tace" yawwa daddy tubda Allah yasa kadawo kaimana tsakani da yaya kullum sai yaci zalina ba abinda nakemai fa kuma" taqarasa cikin shagwa'ba.

  Kallon mansur yai kan yace" ah a'a son banason girman banza fa da cin zalifa, kul wllh mai sunan mim d'in akewa rufdugu?"

 
  Mamace tai saurin ta rarsa da fad'in " kaima dai kasan 'yartaka da shegen rashin ji ga kuma qarya yanzu kai har ka yarda da abinda tace?"

  Kan Alhaji yai magana Zuhailat ta fake idansu ta makawa Manaur harara, ganin hakan yasa shi kuma kawo mata maka cikin zafin nama alhaji ya tare shi cikin fad'a yace" au agaban nawa ma yi zakayi to bisimillah gaka gata"

  "Daddy gwalo fa tamin harda harara yanzufa" ya fad'a fuska a had'e.

   Alhaji kam ko takan Mansur baibiba ya juya ya shiga baiwa Zuhailat haquri tare da ban baki.

  Shikam Mansur na ganin hakaya miqe tare da barin falon, wayar sa yafidda daga aljihu ya danna number din Ammar bugu d'aya ya daga kamar yana jiransa.

Bayan sun danyi hirani yake shaidamai daddyn su fa yadawo, yakamata yazo su gaisa "

  Jin hakan yasa Ammar tayashi murna sosai domin sun jima suna san ya dawo dan ya dad'e da tafiyar, nan sukai akan gobe insha Allah zai shigo.




    *********
   
    Ba yadda Abdallah ya iya dan duk yadda yaso ya ganar da Daddy hakan bata faruba domin kwa ba qaramin fad'a yadinga mai ba ta inda ya shiga to batanan yake fita ba, cikin fushi ya kalleahi tare da fad'in " banta'ba tunanin cewa kai d'in cikakken mayaudari bane kuma cikakken BUTULU ba sai yau ashe daman irin tarbiyar da nabaka kenan, irin abinda zaka sakamain dashi na dau amanar 'yata na baka shine zaka wofantar min da ita, to wllh inaso kasani duk inda ka kaimin 'yata nabaka nan da zuwa anjima ka fiddo min da ita in ba hakaba kotoci zata rabamu na rantse " yana qarasa fad'a ya fice tare da diremai complement nasa akan ya tuntu'beshi tanan.
   
   
   
    Sosai Abdallah ya shiga cikin d'imuwa zuciyarsa ta karaya yarasa ma ta wanne fanni zai soma, shikansa bazaice ga inda Fatima takeba, yanzu ya zaiyi meye mafita.
   
   
    Cikin sairi ya fidda wayarsa daga aljihu yashiga neman layin Sabir shika d'aine mutumin da zai iya temaka mai ayanzu.
   
   
    Bugu biyu tai ya d'aga, cikin karyayyiyar murya yace" inasan ganinka plz" daga haka ya kashe wayar.
   
   
    Tabbas yasan ayadda yaji muryarsa yana cikin matsala da damuwa hakan yasa ya tattara duk wasu ta kardu ya ajjiyeau gefe ba tare da yayi sallama da kowaba a office d'in ya fice.
   
   
   
    Yana zuwa ya taddashi nan inda daddy yabarshi cikin hanzari ya qarasa indabyake tare da tambayarsa lafiya??"
   
   
    "Daddy " ya fad'a a hankali.
   
   
"Me ya faru da daddyn, wani abunne ya sameahi" Sabir ya tambayeshi.

      "A'a Sabir inacikin wani hali daddy yasamo inda nake yanzu baidad'e da fita daga hidan nanba, kuma yace duk inda zanyi na samomasa 'yarsa nan da anjima in bahaka ba kotoci zata rabamu, yazanyi Sabir a ina zan ganta??"

    Ajjiyar zuciya sabir ya sauke kan yace" tirqashi kaga irinta ko abinda na dad'e ina gayama kenan kai kunan uwar shego dani"

   "Nidai yanzu ba wannan ba plz ina zan samo Fatima nima ina da buaqatarta tabbas nayi wauta sosai ya Allah"

   Cikin jin haushi Sabir yace" wautama yanzu ka farayinta, kabani nanda minti biyar zanje na dawo"

   Bai jira amsar sa ya fice daga d'akin, ganin hakan yasa Abdallah zamewa ya zauna kan kujera tare da dafe kansa.


Comment and Share.....plz


*Mrs.Abduul ce......*

 

             BUTULU.....Where stories live. Discover now