BUTULU... part 31

49 2 0
                                    


💫 *DA BAZAR-MU WRITER'S ASSOCIATION* 💫

We are here to make you happy....smile, educated and to realized that we are the best among all........ *Da bazar-mu muke tunqaho*💃💃💃💃

    

          *BUTULU*

By
  *Maryam Abduul*

  *Maryamad856*
*@face book maryam Abduul*

            *Marubuciyar:*
         *BIYAYYA*


*Part.....31*


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.


     ***************A fusace ta bud'e qofar tata, kallon tara saura kwata ta masa kan tace" lafiya meyafaru kake bugan qofa kamar zautacce"

    Cikin kid'ima Ammar yace" dan Allah ki taimakamin mamace nazo na tadda a kwance rai a hannun Allah"

     Harararsa tai kan tace" au rashin kunyar taka har takai kazo ka tadani ina bacci da sassafe, to ta mutu man ina ruwana"

     " A'a ba hakabane dan Allah ke temaka, idan baba yana nan ki masa magana mama tana buqatar temako" Ammar ya fad'a.

     " Yo to ina ruwana da temakon nata" ta fad'a a hasale.

     "Dan girman Allah ki taimakan nazo na taddata tana nunfashi sama-sama kuma tana tacewa 'barayi-'barayi"

     "Oh kai dai kace nice 'barauniyar, haka kake nufi ko" ta fad'a.

     " A'a dan Allah ki temaka ki sanar da baba idan yadawo daga masallaci tana buqatar temako tana cikin wani hali" Ammar ya ambata cikin fuskar tausayi.

    Kan tace wani abu malam Audu ya rabka sallamar sa cikin sauri Ammar ya tafi garesa tare da fad'in " baba mama, 'barayi muje ka gani bata ko......."

     Kan ya qarasa Tabawa ta tareshi da sauri cikin fashewar kuka, ganin hakan yasa malam Audu cewa" wato kana nufin uwar takace 'barauniya ko?, lallai na yadda baka da kirki ko kad'an, gyaturce ta aikoka dan batajin zata iya ziwa da kanta, wato yau taga ta haife mai qwarin qashi wanda ya qware a fagen shushyna ko??"

   A hanzarce Ammar yace" a'a wllh baba bata da lafiya ko motsi batayi ma dan Allah muje kaganta"

Duka yakaimai da car'bi tare da fad'in " dan uwar taka ba inda zani, ba abinda zanmata wllh ko qwandalata bazan bada ba"

  " Kina ina ke kuma munafuka fiti nace , zaki wani turo yari ai da sai kizo ayi dake ko, qaramar mara kunya" ya qarasa cikin hasala.

   Ganin hakan yasa Ammar wucewa d'akin nata dan yaga babu alamun cewa" zasu temaka mata" shima malam Audu na ganin hakan ya jiyo zuwa wajen Tabawa nan yashiga aikin rarrashinta da bata baki akan tai haquri zai d'au mataki.

    Cikin sauri Ammar ya shiga neman wayar Mansur, Allah ya temakeshi bugu d'aya ya dauka nan ya shiga sanar dashi halin da ake ciki.

  Baifi minyi gomaba sai gasu da Zulaihat a mota, nan suka dau mama sai asibiti.





    *************Yanzu Fatima rayuwa take cikin kwanciyar hankali da annushuwa domin kwa tana samun kyakkyawar kulawa daga wajen iyayen nata biyu.
   
   
    Uwa uba ga kuma gogan dan sosai yake bata kulawa, acewars" inda da hali ko qoda baisan ya ra'beta"
   
   
    Wannan yasa kulkum take cikin kwanciyar hankali tayi qiba tayi 'bul'bul da ita kamar ba Fatiman da kasani ba.
   
   
   
    Kullum suna manne da juna a waya ita da sahubul qalbin nata, zancansa d'aya shine ranar auren su tazo yaganta cikin d'akin sa tare da juna"
   
   
    Itakam abin na matuqar bata mamaki sosai yadda ya qagu ayi bikin, wani zubin idan tace mai" ya fiye gand'oki" sai dai kawai yai dariya ko yace" ai duk ke kika ru'dani, kika burkitani shiyasa" itakam sai dai kawai tai dariya abinta.
   
   
   
   
   
   
    **********Wajensu granny ma abin alhamdulillah sosai take samun kulawa daga wajen Abba da Saliha, dan suna matuqar ji da ita.
   
   
   
    Sai dai har yanzu kullum burinsu da fatansu shine" Allah ya bayyana wad'annan yaran"
  


  
   ************Bugune sosai ya tsananta akan kunnensa hakan yasahi dole idanuwansa, a hankali ya saukesu kan ta sanye take da riga da wando sai abaya data d'ora akan kayan, ba wani hijab ko mayafin arziqi illa mayafin abayar da tai rolling dashi.

   Fuskarnan tata tasha uban make up kamar wacce zata gasa, kallonshi tai kan ta kauda kanta gefe tace" to ni na wuce idan ka miqe ka iya had'a breakfast d'in yasin na makara sai jirana akeyi" ta qarasa tana me jiyawa.

   Ba tare da ya miqe zauneba yace" ina zaki haka??"

  Ba tare data jiyo ta kalleahi ba tace" wai kai meyasa fisabilillahi sai ai ta maimaita abu d'aya ne, nakeji mun gama magana dakai tun jiya bikin qawata akeyi kuma ya zama dole naje"

A daqele yace" amma nace" bazaki bako??"

A yatsine ta jiyo ta kalleshi tace" kai ma kasan hakan ba zaiyiwuba wllh, ni kaga tafiya ta"

  A zafafe ya miqe tare da fincikota tayo dakin kan yace" wai ke meyasa kamar dabba kike ne, nace bazaki ba ko ba kya fahimtane??"

  Fincike hannunta tai kan tace" wllh wllh Abdallah ko me zakace bazai hanani fitar nan ba idan kaga dama ka aikon da takardata gidanmu" tana gama fad'a ta juyawarta tai waje.

Dafe goshinsa yai, yana jinjina wannan al'amari yana matuqar dana sanin aurenta, meyasa ma yai hakan ?? gashi tanaso ta zamemasa qarfen qafa, sam baison dukan mace amma da yau ba'abinda zai hanashi yai mata la-las.


  Cikin sauri ya fad'a bayi tare da sakarwa kansa ruwa, sai da yashafe mintina goma sannan ya fito zuciyarsa na masa suya yanaji inama bashi bane ba.

 
Sauka qasa yai zuwa kitchen dan had'a wa kansa abin karin kumallon, wani takaicine ya turniqeshi wai shine a kitchen da safe, hakan yabashi damar tunawa da Fatima, lokacin da take nan kan ya tashi ta gamai musu komi hatta da ruwan wankansa ta had'amai a bayi.

Tsaki yaja tare da kashe gas d'in yai ficewarsa daga kitchen d'in.

  Takwas da rabi ya gani duk da baison fitar amma ya gwammace ya fice daga gidan ko ya rage zafi, hakan yasashi saurin shiryawa ya dau jakarsa yai waje.


Comment and Share........plzzzz

Taku har kullum.......

  *Mra.Abduul ce*.......

             BUTULU.....Where stories live. Discover now